LAILAH-DIZHWAR

2.2K 108 0
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
         🌷🌷🌷🌷🌷🌷
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
          🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*🌼👸🏻LAILAH-DIZHWAR🤴🏻🌼*
  *🌷🌷🌷🌷NA🌷🌷🌷🌷*
  *ZAINAB NASEER SARKI*
       *_ (ZEENASEER😘) _*
       🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

'''Editing by : Ameerah Zarewa'''

*© REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄*
                ☆We the best ☆

ViaWattpad@Zeenaseer01
https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&__tn__=H-R

Email:realhausafulaniwritersforum@gmail.com
Facebook:www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITTERSFORUM.com

*107*

Lailah dake kwance ita kadai dan ta gaji da zaman shirun gashi ta kasa bacci, Kadaicin gida da yan gidansu duk ya dameta, jin an bude kofar an shigo da sallama yasa ta Kallan kofar da sauri.
Cike da mamaki taga Dizhwar,batayi niyar tashi ba ganin Husna a bayanshi yasa tayi saurin mikewa zaune.

Kallanta take yayin da Husna da Dizhwar din suma Lailah suke kallo dan ba karamin kyau tayi ba.

Wani kishi ne da bakin ciki ya cika Zuciyarta, kenan dan zaizo wajan tama saiya taho da matarsa, hakan yasa taji kuka na kokarin taho mata, amma tayi saurin maida kwallarta ta koma ta zauna kanta a kasa.

_"Munafuka sai wani sunkuyar dakai kike, Malama ki bude ido ki kalleni kuma ki bude kunne dakyau ki jini, Mijina yafi karfinki in har baki fita harkarsa ba keda kwanciyar hankalin acikin gidan nan har abada, yanzu kin fita kin dawo in kika kuma fita keda gidan har abada"_

Tana kaiwa nan ta fice tana huci da bakin cikin ganin kyan da tayi.

Shikuwa shiru yayi kamar wani sauna yana kallan Lailah da zuwa yanzu hawaye kebin kumatunta, Lailah abunda taji ya tabbata kenan bazai iya magana ba tana gaya mata maganganu marasa dadi, shine ma ya janyota kenan dan acimata mutunci.

Zuwa yanzu kukan me karfi ya kwace tana me dana sanin dawowa inda ba'a santa kuma ba'a kaunarta.

Jin kukanta yasa yayi saurin ajje wayarsa a gefe ya karasa wajanta, hannu yasa ya janyota kan kirjinsa yana me lumshe ido dan bayasan jin kukanta.

Da sauri cikin zafin nama ta kwace jikinta ta koma can kasa gefe guda ta takure tana kukan, tare dasa lafayar ta kuma kudundune jikinta zuciyarta tana tafasa iya tafasa.

Da sauri ya karaso wajan nata tare da durkusawa inda take.

_"Lailah kukan menene kuma kike, dan Allah kiyi hakuri bana san jin kukanki, ki gayamin manayi miki har bakisan zama ajikina"_

Wani bakin cikine ya kuma taso mata wannan karan kukan tsayawa yayi illah shiru da tayi masa kawai.

_"Lailaaah!"_
Ya kuma fada yana matsowa gareta.

Da sauri ta mike tsaye zata bar wajan.

Sauri yayi ya kamo hannunta tare da mikewa tsaye, kirjinsa ya jingina da bayanta hannunsa yana rike dana juna ya furta,
_"Dan Allah kiyimin magana mana, meyasa bakyasan farin cikina? "_
  Ya fada yana juyo da ita, fuskarta data jike da hawaye yake kallah cikin shaukin so da tsantsar kauna,

Ahankali yasa harshanshi yana lashe dukkan hawayan dake fuskarta, tare da sakar mata hannunta ya rungumota jikinsa ya na sauke sassanyar ajjiyar zuciya jin tayi shiru.

Sun jima a tsaye Kafin ya furta,
_"Lailaaah"_
Shiru tayi bata bashi amsa bah.

_"Menene yake samin ke kuka ko bakya san gidan nan, ko bakya farin ciki da kika dawo gareni uhm? "_

LAILAH-DIZHWAR page 105 to the endDonde viven las historias. Descúbrelo ahora