LAILAH-DIZHWAR

1.4K 79 0
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
         🌷🌷🌷🌷🌷🌷
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
          🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*🌼👸🏻LAILAH-DIZHWAR🤴🏻🌼*
  *🌷🌷🌷🌷NA🌷🌷🌷🌷*
  *ZAINAB NASEER SARKI*
       *_ (ZEENASEER😘) _*
       🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

'''Editing by : Ameerah Zarewa'''

*© REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄*
                ☆We the best ☆

ViaWattpad@Zeenaseer01
https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&__tn__=H-R

Email:realhausafulaniwritersforum@gmail.com
Facebook:www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITTERSFORUM.com

*149*

________
Koda Dizhwar yabar wajan Fareeda part din Mami ya nufa dan sanar mata da abunda yake faruwa, suna zaune suna hira ita da jakadiya.

Ganin me martaba yazo ta shiga kokarin tashi, amma sai Mami ta tsayar da ita danta yanka masa fruit.

_"Sannu da kokari Dizhwar, Allah yayi maka albarka ya baka yara masu Albarka"_
Mami ta fada tana kallansa.

_"Ameen summa Ameen"_
Jakadiya ta fada tana yanka masa fruit din.

Shiru yayi nadan lokuta kafin ya sanar da Mamin abunda yake faruwa.

Kallan jakadiya tayi, yayin da itama hakan kallan nata takeyi.

_"Toh Allah ubangiji yasa mu dace, shikenan mu daga wannan sai wannan shide dan Adam baxai san abunda ya dace dashi ba tsakani da Allah, nide bana ganin abunda yayi kama da xafin ciwo anan wajan, tunda yarinya ta bude baki ta fadi wannan abu tabbas gaskiya ne, sabo da haka kayi gaggawar sanan da mahaifinka dan in ba hakan bane menene dalilin dazai saka tayi yinkurin kashe yar cikinta? "_
  Mami ta fada tana kallan Jakadiya da tunda Mami ta fara magana take gyada kai.

_"Gaskiya ne ranki ya dade tabbas ko gaban Allah xan bada shaidar abunda nima na gani da idona, duk da ban kamasu cikin halin da ake zargin dasu ba, amma alamu sun nuna hakan"_
Nan Jakadiya ta sanar musu da abunda ta gani din.

_"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'una ni Sakina duniya ina zamu dake, ubangiji Allah ya kare mu daga sharrin shaidan ya tsare mana yaran mu da kuma zuri'ar musulmi  baki daya"_
_"Ameen duk suka fada"_

_"Yanzu lalacewar har takai haka tsakani da Allah mutum ya rasa inda zaiyi wannan abu sai cikin dakin auransa"_

Shiru duk sukayi dan kowa abun ya bashi mamaki.

_"Tabbas babu wanda zai yi mamakin wannan abu da yake faruwa, tunda har fareeda ta kasance ba yar memartaba ba ranki ya dade Lallai kuwa me hali baya fasa halinsa"_
Jakadiya ta fada.

_"Gaskiya ne maganar ki, sabo da haka wannan abu, babu maganar ayi shiru da ita domin ta sabawa ko wata irin shari'a balle ta musulinci kuma acikin gidan sarauta kuma a matar sarki,dan haka sai an sake saban zama dan Magana bata kare bah"_
Mami ta kuma fada

Nan suka ci gaba da tattaunawa harna tsawan lokaci kafin yayi musu sallama ya tashi ya fice.

_____
Lailah kwance cikin falonta ita kadai tana hutawa kira ya shigo cikin wayarta.

Zaune ta mike tare da daga kiran tana murmushi ganin me kiran nata, ba kowa bane sai Zahra.

_"Amarya ansha kamshi, kwana biyu sai yau aka tuna damu "_
Lailah ta fada tana dariya.

_"Kai Anty, wallahi ba haka bane, naji abunda ya farune da Yaya Dizhwar shine na kira inyi muku jaje"_
Zahra ta fada.

_"Wallahi kuwa Zahra"_

LAILAH-DIZHWAR page 105 to the endWhere stories live. Discover now