LAILAH-DIZHWAR

1.4K 86 1
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
         🌷🌷🌷🌷🌷🌷
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
          🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*🌼👸🏻LAILAH-DIZHWAR🤴🏻🌼*
  *🌷🌷🌷🌷NA🌷🌷🌷🌷*
  *ZAINAB NASEER SARKI*
       *_ (ZEENASEER😘) _*
       🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

'''Editing by : Ameerah Zarewa'''

*© REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄*
                ☆We the best ☆

ViaWattpad@Zeenaseer01
https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&__tn__=H-R

Email:realhausafulaniwritersforum@gmail.com
Facebook:www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITTERSFORUM.com


*135*

Lailah bata tashi ba sai wajan La'asr, hakan yasa ta tashi jikin ta babu kwari ko kadan duk ko ina ciwo yake mata.
  kafin lokacin an cire mata drip din kasancewar da sauri dr. din ta saka shi.

Asiya dake gefanta tana bawa Ayman Nono ce ta kalleta tare da saurin tashi ta kwantar da yaran ta taimaka mata ta tashi zaune.

_"Sannu Anty Lailah ya jikin naki"_
Asiya ta fada cikin tausaya mata.

Kai kawai ta iya gyada mata.

Daidai lokacin Humairah ta shigo tare da fadin,
_"Alhamdulillah  kin tashi kenan"_
  Bin Humairah tayi da kallo tare da lumshe ido ta koma jikin pillow ta kwanta.

_"Sannu Lailah, bara in hada miki ruwa me zafi ki gasa jikinki zakifi jin dadi"_
Ta fada tana shiga toilet din.

Bayan ta fitone ta furta,
_"Yawwah tashi ki shiga ki gasa jikinki"_

Ahankali ta mike tana cijewa.

Tashi tayi tahau cire kayanta, jikinta yayi zafi sosai.

Towel ta miko mata ta daura, wata yar karamar roba ta mika mata me murfi tare da fadin,
_"Inkin shiga kiyi fitsari anan ki bani pls"_

Da sauri ta kalleta tare da fadin,
_"Fitsari kuma? "_

_"Eh"_
Ta bata amsa a takaice.

Babu musu ta shiga bata jima ba ta fito tare da mika mata.

Amsa tayi fuskarta dauke da murmushi ta fita daga dakin.

Kallan Asiya tayi dake zaune da alamun tambaya.

_"Gwaji za'ai aga meke damunki"_
Asiya ta fada tana murmushi.

Itama maida mata tayi tare da komawa ta shige tana me sake sake a ranta.

Taji dadin ruwan sossai dan saida ta tabbata kaso 80 cikin 100%na kasalar da takeji ya ragu.

Fitowa tayi ta murza lotion sama sama ta saka doguwar riga ta koma ta kwanta.

Mami ta shigo dauke da abinci da kuma lemuka masu sanyi da ruwa ta nufota tana fadin,
_"Allah mungode maka, sannu Lailah yaya jikin naki"_

_"Da sauki Mami"_
Ta fada kanta a kasa.

_"Toh Allah ya qara sauki, yanzu haka zama da kukeyi da yinwa ne yake san saka miki ulcer ku yima kanku adalci kuna cin abinci akan lokaci dan Allah, yanzu ki zuba abinci kici ki koshi kinji"_
Ta fada tana kallanta.

_"Mami sallah zanyi, kuma bana san abincin nan tea kawai nikeso shima babu madara"_
.Kallan Asiya tayi da itama ta kalleta,sannan ta maida kallanta ga Lailah,kafin tace,
_"Ikon Allah yanzu ruwan bunu ne zai rikema mutum ciki ni sakina, kede fadi abunda kikeso sai a kawo. Miki amma tea yayi kadan"_

LAILAH-DIZHWAR page 105 to the endWhere stories live. Discover now