LAILAH-DIZHWAR

1.8K 106 25
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
         🌷🌷🌷🌷🌷🌷
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
          🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*🌼👸🏻LAILAH-DIZHWAR🤴🏻🌼*
  *🌷🌷🌷🌷NA🌷🌷🌷🌷*
  *ZAINAB NASEER SARKI*
       *_ (ZEENASEER😘) _*
       🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

'''Editing by : Ameerah Zarewa'''

*© REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄*
                ☆We the best ☆

ViaWattpad@Zeenaseer01
https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&__tn__=H-R

Email:realhausafulaniwritersforum@gmail.com
Facebook:www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITTERSFORUM.com


*115*

*NA SADAUKAR DA WANNAN SHAFI WA DUKKAN YAN GROUP NA _DANDALIN UMMIJAFAR_,NAGODE DA IRIN SOYAYYARKU GARENI DA NOVEL DINA,ALLAH YABAR KAUNA❤*

_______
Haka su *LAILAH-DIZHWAR* suka yini ranar suna nunawa junan su so da zallar kauna, koda zai tafi sallar magriba da er ta barshi ya tafi shima haka nan ya tafi badan ya so bah.

Koda ya tafi, saida ta kuma yin wanka dan yin sallar itama dan Fitinar Dizhwar din bata barinta hutuwa.

Bayan tayi sallar abinci taci sannan ta koma daki inda ta dauki wayarta dan kiran gida, sun jima suna hira dan yau tasamu kowa yana nan, sannan aka turo mata da number Hibba dan jiya Aliyu mantawa yayi, bayan sun gama wayar ne ta kira Humaira ta sanar mata Ya barta maganar tafiyar tasu.

Bayan nan Hibba ta kira har kunya take ji dan har ga Allah tasan bata da mutunci.

Koda Hibba ta daga da sallamar ta kunya magana Lailah taji kamar zata kashe sai kuma ta amsa mata sallamar tatah.

_"Amarya manyan gari, sai yau aka tuna damu"_

_"Hmm ba haka bane ykk ya sch.?"_

_"Alhamdulillah komai lafiya qlau, ya kike ya Amarci munyi waya da yan gidanku sun sanar min da har kin tare, wallahi saida suka gayamin  hankalina ya kwanta, Allah ya kiyaye Gaba Lailah"_

_"Ameen ameen Nagode Hibba, sannan matsalar data faru tsakanina dake kafin mu rabu dan Allah kiyi hakuri wallahi ba'a san raina bane, cike da Nadamar hakan na dawo gida"_

_"hmm babu komai wallahi, ni ko kadan ban rikeki bah, Allah de ya kiyaye"_

_"Ameen"_
Lailah ta kuma fada.

_"Ina Angon naki, ko saike kadai cikin dakin, kar na cika ku da surutu"_
Hibba ta fada tana murmushi.

_"Wallahi bama ya nan, saini kadai, yaushe zaki zo gidana?"_
Lailah ta tambaya.

_"Uhm, sai nima an kawoni Zamfara kinsan bikina next month ne kuma Zamfara za'a kawoni"_

_"Dan Allah dagaske kike? "_
Cikin farin ciki Lailah ta tambaya.

_"Wallahi kuwa, sabo da haka dole kizo wallahi dan nariga da na saka ran zuwan naki"_

_"ai insha Allah zaki ganni kuwa, kede ki kwantar da hankalinki, Allah ya sanya alkairi wallahi"_

Sun jima suna hira kafin daga bisani suyi sallama.

_____
Dizhwar kuwa koda ya tafi masallaci saida yayi ishsha'i sannan ya nufi part dinsa dan yayi wanka yaje yayi ma Lailah sallama.

Ga mamakinsa sai yaga Husna acikin bedroom dinsa zaune tana danna waya.

koda yayi sallama bata ba amsa ba, dan haka shima be damu ba, wanka yayi ya fito ya fita yaci abincinsa, dawowa yayi ya shiga toilet din, be jima ba ya fito tare da ajje wayarsa ya nufi kofa zai fita, da sauri ta kalleshi tare da fadin,
_"Ina kuma zaka? "_

LAILAH-DIZHWAR page 105 to the endDonde viven las historias. Descúbrelo ahora