LAILAH-DIZHWAR

1.5K 86 1
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
         🌷🌷🌷🌷🌷🌷
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
          🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*🌼👸🏻LAILAH-DIZHWAR🤴🏻🌼*
  *🌷🌷🌷🌷NA🌷🌷🌷🌷*
  *ZAINAB NASEER SARKI*
       *_ (ZEENASEER😘) _*
       🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

'''Editing by : Ameerah Zarewa'''

*© REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄*
                ☆We the best ☆

ViaWattpad@Zeenaseer01
https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&__tn__=H-R

Email:realhausafulaniwritersforum@gmail.com
Facebook:www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITTERSFORUM.com

*123*

Bayan kowa yayi shiru, ana jiran jin wanda zai fara magana, Alhajin Faisal ne ya furta,
_"Alhamdulillah dole yau mugode ma Allah daya nuna mana wannan lokaci, kuma ina fatan wannan zai kasance na farko kuma na karshe da hakan zai kuma kasancewa da family din mu, Duba da irin babban abunda ya faru, wanda ko acikin mafarki babu wanda yayi tunanin faruwar hakan acikin gidan nan, amma da yake kaddara ta riga fata, sai Allah ya nufemu da jarabawa akan danmu,toh mungode masa kuma yau gashi ya kawo mana solution, wanda komai ya warware sanadiyar wannan yarinya me cike da abun al'ajabi"_
  ya fada yana nuna Lailah.

Sannan yaci gaba da fadin,
_"A tunanina dukkan wanda wannan abu ya faru dashi, Bazai taba tunanin yafema Wanda yayi masa bah, zata bada goyan bayane akan a kwatar mata hakkinta da irin cikin mutuncin da aka mata, amma da yake tana da hankali, nutsuwa da kuma tawakkali, sannan tana da kyakkawar zuciya itace wanda ta fara yafe masa, kuma ta yi kokarin daidaita tsakaninsa da iyayansa,Munji dadi kuma gaba dayan ku mun jinjina muku, muna masu matukar godiya a gareku, dafatan Allah zai albarkaci auranku ya kuma baku zuri'a ta gari wanda zakuyi alfahari da ita nan gaba"_

_"Ameen"_
Kowa ya furta dake cikin falon.

Sannan Alhajin ya juyo kan Zahra da Faisal dake jikinsa tayi shiru tana sauraran Alhajin.

_"Sannan kai Faisal kayima Allah godiya daya azurtaka da mace ta gari, wanda take sonka tsakani da Allah, kuma take fatan ganinka cikin farin ciki, dan tabbas da wata ce ba Zahra ba bazata taba jin sha'awar xama dakai ba, badan komai ba saidan halayanka da suka kasance masu rauni Faisal"_

Ahankali ya janye jikinsa daga jikin Zahra tare da mikewa ya matsa har gaban Alhajin nasa,
_"Abba dan Allah dan annabi badan niba ka yafemin dukkan abunda na aikata, naji dadi kuma na gode da kuka fahimceni har kuke yimin addu'a, insha Allah zan kasance mutum Na gari wanda zakuyi alfahari dani"_
  Sannan ya juya ya kalli Uncle tare da fadin,
_"Uncle Nagode daka bani Zahra a matsayin matata, nayi farin ciki Allah kuma ya saka maka da alkairi kaima ka yafemin dan Allah"_

Cikin farin ciki ya gyada masa kai, yayin daya juya ya kalli Mamansa, tare da hade hannayansa yana me bata hakuri, itama nuni tayi masa da ta yafe masa, sauran yan gidan ya bama hakuri, suma suka yafe masa.

Juyawa yayi ya bama Lailah hakuri, wanda ta fara kuka tsabar farin ciki, itama yafe masa tayi kafin ya koma gaban Dizhwar.

Duk da yasan ya suke dashi amma beji komai ba cikin ransa, cikin muryar rauni da kuma bada hakuri ya furta,
_"Dan Uwana ka kasance mutum me kyakkyawar zuciya, tabbas koda nine akayiwa abunda nayi maka, zan kasance me daukar dukkan matakin daya dace, kuma bana tunanin zan iya yima wanda yayimin afuwa, amma duk da haka ka yafemin kuma ka daidata tsakanina da iyayena, Nagode maka Allah ya baka zaman lafiya da matanka da kuma iyayanka, Allah ya kareka daga Sharrin dukkanin makiyanka, Nagode "_
Ya fada yana hawaye.

LAILAH-DIZHWAR page 105 to the endWhere stories live. Discover now