LAILAH-DIZHWAR

1.6K 94 4
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
         🌷🌷🌷🌷🌷🌷
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
          🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*🌼👸🏻LAILAH-DIZHWAR🤴🏻🌼*
  *🌷🌷🌷🌷NA🌷🌷🌷🌷*
  *ZAINAB NASEER SARKI*
       *_ (ZEENASEER😘) _*
       🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

'''Editing by : Ameerah Zarewa'''

*© REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄*
                ☆We the best ☆

ViaWattpad@Zeenaseer01
https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&__tn__=H-R

Email:realhausafulaniwritersforum@gmail.com
Facebook:www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITTERSFORUM.com


*122*

Cikin kulawa da tausayinta ya matseta cikin jikinsa yana fadin,
_"Zai gyara Amar, shima zai zama cikakken mutum insha Allah, amma ki daina kuka kiyi masa addu'a, tunda kin yafe masa nima na yafe masa kuma yanda kikace haka za'ai sarauniyatah.

Ya fada yana kallan fuskarta,

sai yanzu ta saki murmushinta me sanyi tare da komawa jikinsa tana fadin,
_"Nagode Rouhi, Nagode"_

Da sauri ta mike zaune tare dajan blanket din jikinta.

Biyota yayi yana kissing bayanta, da sauri ta mike tana dariya,
_"Tafiya zanyi gaskiya, kaima ka tashi bayan sallar magriba zamuje can din tare da Zahra tana jirana tafiya xanyi"_

Ta fada tana daukar zanin tah.

Kishingidawa yayi yana kallantah, tare da fadin,
_"Ya Amar tafiya zakiyi ki barni"_

Bata masa magana ba saida ta gama saka kayanta tukun, juyowa tayi tana kallansa tare da fadin,
_"Inq tare da kai har abada"_

Jin haka yasa yayi dariya tare da bude hannunsa alamun ta taho garesa.

Ganin haka yasa tayi saurin bude kofar ta fita daga dakin.

_______
Husna kuwa jin abu yaki karewa har ana shirin yin sallah yasa ta kara hasala, ta kasa zaune ta kasa tsaye ita kadai cikin daki.

Ahankali ta kuma mikewa ta bude kofar karo na biyar kenan, sake lekowa tayi tana me dubawa ko xata jishi, amma falon babu kowa gyarashima yan aiki suke.

Da sauri ta fito tana kallan wata me aiki hannunta rike da wayarta ta gyara tsayiwarta.

Magana tayi mata, da sauri ta juyo tare da kara suwa wajan cikin girmamawa.

_"uhmm yawwa bakiga Memartabah Dizhwar bah Dallah?"_
Ta tambaya tana kallan tah.

Cikin rissinawa ta furta,
_"Ranki ya dade da alama baya cikin gidan nan dan ban ganshi bah"_

Jin haka yasa Husna murmsuhi batare data kuma magana ba ta koma dakin cike dajin dadi dama ita bata san taji ance yana nan dan tasan duk inda yake yana tare da wannan mayyar.

______
Ita kuwa Zahra koda ta idar da sallah  ganin Lailah bata dawo ba, zama tayi cikin dakin tana jira ayi magariba.

Jin Lailah ta turo kofar yasata kallanta fuska dauke da murmushi.

Da sauri ta karaso tare da rungume Zahra tana fadin,
_"Zahra nayi masa magana kuma ya amince, bara in fito sai muyi sallah muje tare ko? "_
  Ta fada tana kallan fuskarta.

Murmushin farin ciki tayi tare da gyada mata kai.

Kayanta ta cire ta shiga wanka.

Bata jimaba ta fito tana goge kanta dan sauri take yi.

LAILAH-DIZHWAR page 105 to the endWhere stories live. Discover now