LAILAH-DIZHWAR

1.4K 75 0
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
         🌷🌷🌷🌷🌷🌷
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
          🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*🌼👸🏻LAILAH-DIZHWAR🤴🏻🌼*
  *🌷🌷🌷🌷NA🌷🌷🌷🌷*
  *ZAINAB NASEER SARKI*
       *_ (ZEENASEER😘) _*
       🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

'''Editing by : Ameerah Zarewa'''

*© REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄*
                ☆We the best ☆

ViaWattpad@Zeenaseer01
https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&__tn__=H-R

Email:realhausafulaniwritersforum@gmail.com
Facebook:www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITTERSFORUM.com


*143*



Lailah kwance kan kujera suna faman Hira, Anty Yusra ce tace da ita,
_"Lailah dare fa yanayi bazaki tashi ki tafi bah"_

Dariya tayi tare da janyo wayar tah, lokaci ta duba dan 9pm ta kusa.

Ahankali ta mike tare da jan hannun Anty Yusra zuwa dakin Mama.
zama sukayi kan gado sabo da babu kowa cikin dakin.

ita kuwa Anty Yusra kallanta kawai take yi.

_"Anty dama tun dazu nakeso mu samu waje muyi wata magana kafin in tafi"_
  Lailah ta fada tana kamo hannun Antyn tata.

Itama binta tayi da kallo tare da kallan hannun nata yanda Lailah ta rike tan.

_"Inajinki"_
Yusra ta fada bayan ta maida kallanta ga fuskar Lailah.

_"Anty wani abune yake faruwa a cikin gidan mu, wanda yayi matukar bani mamaki ya kuma daure munkai, na rasa wanda zan gayawa inji dadi,gashi magana tana ta cina shine dalilin dayasa nazo gida"_

Tunda ta fara maganar take kallanta dan so take taji me zata fada.

_"Anty ashe jaririn Husna ba nata bane"_

Da sauri Anty Yusra ta kuma kallan lailah da alamun tambaya a fuskartah..

_"Wallahi kuwa Anty  abun nima kaina ya bani mamaki da tsoro"_
Nan ta kwashe dukkan abunda taji da kunnanta ta fada mata.

Cike da jin jina al'amarin Yusra ta furta,
_"Dan karin ubancan,amma tunda nake ban taba jin hatsabibiya irin wannan kishiryar taki bah, lallai mutane akan kudi babu abunda bazasu iya bah, Allah sarki mahaifiyarshi ko wani hali take ciki"_

_"uhm kema Anty kya fada toh bana san in zo in fada kuma bani da wata cikakkiyar hujja, dan har ga Allah in har yaran nan yana wajan ta hankalina bazai taba kwanciya ba sabo da tausayinsa da Mamansa, shiyasa banyi abu kai tsaye ba nazo na gaya miki dan kibani shawara"_

Ajjiyar Numfashi Anty Yusra tayi kafin ta kara gyara zama sannan ta fara magana kamar haka,
_"Gaskiyane, amma abunda nake so dake yanzu shine, kije ki tambaya dawa aka je Asibitin lokacin haihuwar tatah, tabbas tunda ke matar sarkice hakan bazai miki wahala bah, ki fara tabbatarwa ta wajan asibitin tukun sai ki dau mataki tunda kinga nan ne tushen gaskiyar abun "_

Cike da fahimta Lailah ta furta,
_"Gaskiyane Anty kuma wannan itace shawara me kyau, dama Anty Allah, Allah nake wani abu ya kifta wanda zanyi amfani da damata da kuma sarautata nima akan Husna, sabo da abubuwan da take mana nida mijina da yan uwansa  in su ta gama dasu asiri ya cisu ni bata isa bah, wallahi in har na gano tabbas abun nan gaskiya ne, sai tayi nadamar auran Dizhwar"_

Dariya Anty Yusra tayi tare da daga hannunta daya sama tare da jinjina tana fadin,
_"Allah yaja daran uwar gidan sarki"_

Dariya itama tayi.

LAILAH-DIZHWAR page 105 to the endWhere stories live. Discover now