LAILAH-DIZHWAR

1.6K 99 22
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
         🌷🌷🌷🌷🌷🌷
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
          🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*🌼👸🏻LAILAH-DIZHWAR🤴🏻🌼*
  *🌷🌷🌷🌷NA🌷🌷🌷🌷*
  *ZAINAB NASEER SARKI*
       *_ (ZEENASEER😘) _*
       🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

'''Editing by : Ameerah Zarewa'''

*© REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄*
                ☆We the best ☆

ViaWattpad@Zeenaseer01
https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&__tn__=H-R

Email:realhausafulaniwritersforum@gmail.com
Facebook:www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITTERSFORUM.com


*146*

Kai tsaye Lailah da jama'ar ta part din Mami suka nufa.

Da shigarsu kuwa ta nuna musu wajan zama yayin da jakadiya da kanta ta shiga ta kira Mami kasancewar a Babban falo suke gaba dayansu.

Bata jima bah ta iso tare da jakadiya da kuma kuyanginta guda biyu.

A tunaninta bakin Lailah ne sudin ko yan uwanta hakan yasa ta zauna cikin sakin fuska,gaisheta sukayi yayin da Lailah ta gaba tar musu da kodin ita wace.

_"Lailah kin kaisu sunga jaririn? "_
Mami ta fada tana murmushi.

Tasowa tayi daga inda take tare da zuwa ta zauna kusa da Mamin.

Cikin fahimta ta shiga mata bayani yanda zata gane, tunda ta fara maganar matar medan kawai take kallo harta gama.

_"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'una,Innalillahi wa'inna ilaihir raji'una,Allah yayi wadaran wannan yarinyar ashe abunda taje ta aikata kenan, tana san ta bata mana sunan masarautar mu da kuma dangin mu,anya kuwa tana da hankali kode Asma'u haukacewa tayi"_
Mami ta fada tana kuka dan abun ba karamin girgiza tayi bah.

_"Ta cucemu, ta cucemu Lailah,  yanzu yaya Dizhwar xaiji wannan maganar taya za'a tunkareshi da wannan maganar"_
Mami taci gaba da magana hanklinta a tashe.

_"Mami ki kwantar da hankalinki, insha Allah zanyi masa bayani ta yanda xai fahimta batare da wani abu ya faru ba, inasan in wanke wannan masarauta da ga zargin da jama'a zasuyi, ina neman izninku dan Allah"_
Lailah ta fada tana me hada hannunta waje daya.

Goge hawayanta Mami tayi kafin ta dafa kafadar Lailah cike da kwarin gwiwa Mamin tace,
_"Lailah nabaki hadin kai dari bisa dari ga dukkan abunda kika ya dage kice wannan masarauta tamu, kece kika kawo mana dukkan wani farin ciki, kece meyi mana Abunda muke so, babu abunda zai gagareki, mungode kwarai Allah ya bada sa'a"_

Nan dogari da kuyangi aka hau kirari wa Lailah,suna buda sabo da sunsan ta cancanci fiye da hakan.

_______
Husna da Anty Amarya haka aka jasu aka nufi kurkuku dasu batare da tayi musu bah dan atunaninta In Dizhwar yazo Dole bazai bari aci mata mutum ci bah.

Cikin wani daki aka saka ta ita kadai yayin da itama Anty Salma aka sata cikin nata dakin kusa dana Anty Amarya da sauran masu laifi.

Kuka Anty Amarya take tana basu hakuri akan tayi nadama kar suyi mata komai.

Wata katuwar matace ta shiga tahau ta da duka saida ta tabbata bata yin magana sannan ta fito ta kulle dakin tana huci ta shiga dakin Husna dake tsaye kikam tana faman raba ido.

_"Ciro dukkan kayan kele kele dake jikinki, umarni na Uwar gida(Lailaaah)"_

Wani kallo Husna tayi mata tare da fadin,
_"Kedin banza, kin isa ki sakani inyi abunda banyi niya ba daga ke har uwar gidan naki data saka ki aikin, wallahi wallahi zakiyi nadama mutukar mijina yasan ina nan wajan daga ke har wanda ta aiko kin"_

LAILAH-DIZHWAR page 105 to the endWhere stories live. Discover now