LAILAH-DIZHWAR

1.6K 91 1
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
         🌷🌷🌷🌷🌷🌷
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
          🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*🌼👸🏻LAILAH-DIZHWAR🤴🏻🌼*
  *🌷🌷🌷🌷NA🌷🌷🌷🌷*
  *ZAINAB NASEER SARKI*
       *_ (ZEENASEER😘) _*
       🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

'''Editing by : Ameerah Zarewa'''

*© REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄*
                ☆We the best ☆

ViaWattpad@Zeenaseer01
https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&__tn__=H-R

Email:realhausafulaniwritersforum@gmail.com
Facebook:www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITTERSFORUM.com

*142*

Saida Lailah tayi kukanta ta gama yanda Dizhwar bazai gane ba tukun ta kullo kofar ta nufi part din nata.
____
Dakin Husna kuwa koda Lailah taje ta ajiye yaro, hankalin Husna tashi yayi.

Cikin kidima ta furta,
_"Anty Anya wannan munafukar bata Ji abunda muke fada ba kuwa"_
Husna ta fada tana kallan Anty Salma.

_"Haba dai bata sani bah, ya za'ai taji bayan zuwanta kenan"_
Hakanan dai husna tayi shiru dan bata Yarda bah.

Janyo yaran tayi tana kallansa, baccinsa yake hankali kwance, kwantar dashi tayi batare data saka shi ajikin ta ba, itama ta juya ta kwanta zuciyarta cike da tunane tunane kala kala.

______
Yanda Lailah taga rana haka taga dare batayi wani baccin kirkiba, tana me jinjina irin rashin imani na Husna, har ta iya raba jariri kamar haka da iyayansa amma ko ajikinta.

Iya Damuwa Lailah ta shiga, tasan tabbas Husna tasan tasan da wannan maganar babu abunda bazata mata bah, kar itama ta raba ta da dan nata da ko duniya bezo bah.

Hannu tasa tana shafa cikin nata ahankali, tunanin jaririn Husna yana mata yawo cikin ranta.

Dizhwar dake kwance kusa da ita sai yanzu ya farka ahankali ya bude idansa yana kallan tah.

Murmushi tayi masa wanda shima ya maida mata, ahankali ya mike tare da jingina bayansa da pillow  ita kuma ta zame daga zaunan da take ta kwantar da kanta kan kirjinsa tare da fadin,
_"Good morning Paper spray"_

Dariya yayi tare da fadin,
_"Morning my cupcake"_

Shiru tayi tana wasa da kirjinsa kafin tace dashi,
_"Rouhi yaya kakejin soyayyar Babyn Anty Husna acikin ranka"_

Shiru yayi tare da lumshe idansa,batare daya bata amsa bah.

Hakan yasa ta kuma fadin,
_"Kana jin son da kake musu daya da unborn din mu"_
Ta kuma fada batare data dago bah.

Idansa yana a rufe ya furta,
_"Ya Amar bawai dan agabanki ba, ko agaban waye zan iya fada miki, son da nake yima cikin ki yafi dukkan wani so da nake yima komai da kowa dake cikin duniyar nan, bansan meyasa bah, Allah ya banbanta soyayyar da nake yima jaririn nan da kuma na cikin ki bana fatan hakan ya kasance har abada, sabo da Bana san in banbanta yarana a ko wani hali, inasan in basu soyayya da kuma tarbiya na musamman yanda zasu kasance abun alfahari.

Dadi taji har cikin ranta kafin ta kuma fadin,
_"Wani suna ka saka ma jaririn namu?"_
Ta fada tare da dagowa tana kallan fuskarsa.

_"Ya Amar wani suna ya dace in saka masa, Jafar na saka masa, amma sabo da Husna bata da hankali take gayamin magana har muka samu sabani ajiyan"_

Murmushi Lailah tayi tare da kwanciya ajikinsa tana fadin,
_"Ka barta ta zabi sunan da take so, nide kayimin alkawarin in na haifi namiji za'a saka masa sunan yaa Jafar , in kuma mace aka haifa inasan asa sunan Hajiyar jafar dan Allah"_

LAILAH-DIZHWAR page 105 to the endWhere stories live. Discover now