LAILAH-DIZHWAR

1.7K 110 3
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
         🌷🌷🌷🌷🌷🌷
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
          🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*🌼👸🏻LAILAH-DIZHWAR🤴🏻🌼*
  *🌷🌷🌷🌷NA🌷🌷🌷🌷*
  *ZAINAB NASEER SARKI*
       *_ (ZEENASEER😘) _*
       🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

'''Editing by : Ameerah Zarewa'''

*© REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄*
                ☆We the best ☆

ViaWattpad@Zeenaseer01
https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&__tn__=H-R

Email:realhausafulaniwritersforum@gmail.com
Facebook:www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITTERSFORUM.com

*126*

Kallan kowa dake dakin tayi, kafin ta juyo tana kallansa, alamun bada ita yake bah.
Hakan yaba Humairah Dariya.

_"Dake yake"_
Zakiyyah ta fada tana dariya itama.

Daga gira yayi tare da zuba mata ido, yayin da itama shidin take kallo.

Sai. Kuma ta juya kallanta ga Asiya, suna hada ido, Asiyar ta taso tare da kwanciya kan kirjin Dizhwar din.
_"Yaya dan Allah ka barta sai gobe mana"_

Ita kuwa juyawa tayi tana shirin jin abunda zai fada, ahankali ya janye Asiyar daga jikinsa tare da fadin,
_"Ina jiranku, ki tashi ki shirya mana"_

Ya kuma fada yana kallan Lailah tare da fita waje.

_"Ki bishi ki rokeshi, wallahi inba haka ba dake za'a tafi"_
Humairah ta fada tana kallanta.

Nokewa tayi dan kunyar su mami take ji.

Asiyace ta daga ta tare da bude mata kofar ta turata,
_"Dan Allah kije mana, ni inasan ki Kara kwana"_

Ba musu tabi bayansa dan ya kusan shiga lungun dazai sadashi da dakin da aka kai Husna.

Da sauri ta karasa tare da kamo hannunsa.

Janyota yayi ta dawo gabansa, sakinta yayi tare da saka hannunsa daya cikin aljihu yana mata wani Kallo me sanyi.

Itama kallansa take tana murmushi.

Tsawan lokaci ahaka kafin ta matso tare da rike habarsa da hannunta tayi pecking kumatunsa, tare da shafa hannun nata kan kirjinsa,
_"Ka tashi lafiya? "_
Ta fada tana kallansa da sexy eyes dinta.

Cigaba yayi da kallanta batare da yace mata komai bah,

Hannunsa daya yasa ya kamo kugunta tare da janyota jikinsa ya fara kissing dinta a fuska,dariya ta kama tare da kwace jikinta tana dariya.

Wani irin kallo yake mata, da idansa kamar wanda ke shirin zubar da kwallah.

_"Dan Allah ka bari sai gobe mu taho tare dasu Humairah kaji"_

Ahankali ya tako inda take still hannun nasa daya yana cikin aljihunsa.

_"Kar muyi haka dake in kina san na kuma Barinki kizo"_

Da sauri ta fada kirjinsa tana tura Kanta saman huyanshi tana fadin,
_"Amma fa tun a gida kace tare dasu zamu dawo, dan Allah nifa na riga da nasa ran sai gobe, pls ka dau su Mami ku tafi ga Anty Husna ma kaji"_

Hannu daya yasa ya kuma matseta ajikinsa batare da yace komai bah.

Jin shiru yasa ta dago ta kalli fuskarsa.

Shima Kallanta yayi,Murmushi ta sakar masa tare da fadin,
_"Ka yarda"_

Kai ya gyada mata.

Ihu ta danyi tare da tsalle ta kuma makalkale shi tana dariyar jin dadi tare da kissing dukkan fuskarsa tana murna.

LAILAH-DIZHWAR page 105 to the endWhere stories live. Discover now