LAILAH-DIZHWAR

1.3K 80 2
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
         🌷🌷🌷🌷🌷🌷
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
          🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*🌼👸🏻LAILAH-DIZHWAR🤴🏻🌼*
  *🌷🌷🌷🌷NA🌷🌷🌷🌷*
  *ZAINAB NASEER SARKI*
       *_ (ZEENASEER😘) _*
       🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

'''Editing by : Ameerah Zarewa'''

*© REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄*
                ☆We the best ☆

ViaWattpad@Zeenaseer01
https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&__tn__=H-R

Email:realhausafulaniwritersforum@gmail.com
Facebook:www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITTERSFORUM.com


*138*

_______
Koda aka shiga da ita bangaranta, zama tayi kan gadan tana ta faman mutsu mutsu, kasancewar dukkan Nurse din da suke duty lokacin sun san da zuwan tah duk suka taru kanta kamar gaske.

Mutum ukune suke labor, da ita da kuma mata biyu. Ta farko aka fara shiga da ita, kasancewar anyi mata scanning anga yan biyu zata haifa hakan yasa Suka saka *Edd* dinta daya dana Husna.

Sukuwa sauran mutanan suna nan waje suna jiran Fitowar tasu.

Nurse daya ce ta leko tare da kiran Anty Salma, jiki yana rawa kamar gaske ta shiga cikin dakin.

Kasancewar tun jiya take fama da labor har zuwa yanzu babu wani labari yasa aka shiga kiran mijinta dan ya saka hannu ayi mata Cs.

Sosai Husna ta rude ganin yanda matar take fama da kanta.

Suna nan mijin nata yazo yasa hannu aka shiga da ita.

Bayan mintina da basu huce goma da shiga da ita bah Ta kusa da gadan Husna ta haihu,amma duk da sun san dan nata lafiyarsa qlau shima suka shiga theater room dashi, acewarsu yazo da matsalar numfashi sabo da Ruwan mahaifa da yasha.

Suna nan aka shigo da yan biyun da akayima Mamansu CS. Amma babu wanda yasan biyu ne dan waje daya suka saka su.

Yara uku yanzu suna hannu, biyu maxa sai mace daya, namjin yan biyun ne ya mutu dan basu fito dashi da rai ba, dan haka sai aka Kawo wa iyayan wanda ta haihun batare da C.S ba a cewarsu yaran ya mutu batare da sanin me Jegon bah.

Ita kuma wanda aka ce yan biyu zata haifa sunce ruwane ashe acikin nata mace ta haifa gata nan tubarkallah masha sallah.

Jaririn matar farko data fara haihuwa wanda aka musu karyar numfashi, shi aka dauka aka kaima Husna a matsayin danta.

Nan aka sanar da duk anyi nasara sun haihu murna wajan Mami da sauran yan gidan fadi ma bata lokaci ne.

Suna nan cike da san a kawo jariri a xaune, aka fito dashi shirye cikin kaya na alfarma.

Jakadiya ta amsheshi ta mikama Mami tana washe baki, Mami cikin farin ciki ta amsa harda kwallar farin ciki tana me yima Allah godiya.

Yayin da sukuma masu ainayin jaririn suna ta kukan rashi, sabo da Shekarun matar takwas da aure bata haihu ba sai yanzu Allah yayi.

Ita kuma me yan biyu, aka bata macan ta sunata murna suma.

Waya tasa aka kira mata Dizhwar,amma kasancewar suna cikin meeting da manyan mutane ba'a daga bah.

Sabo da an tabbatar da lafiyar me jego da baby aka sallamesu zuwa gida.

Tun kafin suzo gida jama'a labari ya riskesu, nan da nan aka cika dan tarbar yarima.

LAILAH-DIZHWAR page 105 to the endTahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon