LAILAH-DIZHWAR

1.6K 105 0
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
         🌷🌷🌷🌷🌷🌷
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
          🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*🌼👸🏻LAILAH-DIZHWAR🤴🏻🌼*
  *🌷🌷🌷🌷NA🌷🌷🌷🌷*
  *ZAINAB NASEER SARKI*
       *_ (ZEENASEER😘) _*
       🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

'''Editing by : Ameerah Zarewa'''

*© REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄*
                ☆We the best ☆

ViaWattpad@Zeenaseer01
https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&__tn__=H-R

Email:realhausafulaniwritersforum@gmail.com
Facebook:www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITTERSFORUM.com

*110*

Murmushi yayi tare da takowa wajanta ga mamakinta ya durkusa tare da yima gefan kugunta kiss, sannan ya dago yayima bayanta har zuwa huyanta.

Cikin kunan ta ya furta,
_"Amarya Zanje in dawo, ki shirya na yau sai yafi na jiya"_

Saida ya tafi ya kullo kofar sannan ta juyo ta dauki kayanta ta saka tana gunguni.

______
Tun jiya da daddare aka dawo da Fareeda gida, dan haka banda kuka babu abunda take yima Anty Amarya.

_"Ya isa haka Fareeda da kukan naki zanji ko kuma da abunda yake damuna, kina ganin komai ya lalace min yanzu, gaba daya na zama kamar bani ba, Gidan nan tamkar yanzu ba gidan mulki bah, mijina yanzu ya rage Sona, gashi Wannan shegiyar Matar Dizhwar Husna tamkar itace sarauniya, yanzu cikima gareta tana nan dashi, gashi an kuma kawo wata Amaryar jiya Lailah ta dawo, ya kike so inyi tsakani da Allah"_

Kallanta tayi da jajayan idanta tare da fadin,
_"Mommy ni ina san mijina, ki gayama Abba dan Allah ya gayama Dizhwar suyi hakuri a sakeshi"_

_"Ke Dallah can rufa min baki, kwata kwata baki da zuciya, yanzu ya kara auran batare daya sanar miki ba sabo da baki da daraja a idansa har ki dinga sha'awar komawa wajansa, aini kin dawo gida kenan, aiba shi kadai ne namiji bah"_

_"Ni bana san in rabu dashi, wallahi yana sona kuma nima ina sanshi, dan Allah kima ya Dizhwar magana dan Allah Mommy"_

Shiru tayi cike da takaicin yar tatah dan ji take kamar ta rufeta da duka.

Tashi tayi ta fita daga cikin dakin dan yanzu duk abun duniya ya ishe tah.

_______
Yau aka sallamo Alhajin Faisal daga asibiti, dan haka gidan biki babu kowa sai yan gidan.

Saida ya tara kowa acikin falon dan duk sunyi jikinsu a sanyaye suna me jiran abunda Alhajin zai fada, Maman Faisal gabanta yafi faduwa akan na kowa dake falon sai Zahra Amaryarsa.

_"Gaba dayanku basai nayi muku tariyar baya ba akan abun kunyar da Faisal ya kuma yi mana acikin family dinann, kuma hakan tamkar tozarcine acikin mu, sabo da haka abunda nake so daku shine,daga yau kowa da yake nan ya saka acikin ransa babu wani me suna Faisal acikin family dinmu, tunda ya zabama kansa rayuwar da zai dinga yi toh muma mun zabi cireshi daga cikin family, sabo da haka yau zamuje wajansa dan amsowa Fatima takardar ta"_

Jin haka yasa gabanta yayi mugun faduwa, haka Mamanshi.

Ahankali ta fashe da wani irin kuka me tsuma zuciya.

Cikin kuka ta mike tare da karasa gabansa duk kunyarta amma yau ta zauna gaban Alhajin tana kuka sosai.

Kowa mamaki take bashi da tausayi.

_"Dan Allah Abba kayi hakuri, dan Allah a kuma bashi dama daya in har be gyara halinsa ba sai ka dauki hukuncin daya dace, Abba wallahi ina san Yaya faisal tun ba yanzu ba, kuma bana san na rasashi a karo na uku kenan, bana san na zama bazawara Abba dan Allah"_

Ta karasa maganar tana kuka, haka Mamanshi itama kukan take dan tana mutukar kaunar Faisal din.

kowa jiran abunda zai fada yake, ganin ya tashi yabar falon yasa Zahra kara fashewa da kuka har tana kwarewa.

Maman faisal dince Hajiya Amina ta taso tare da rungumetah tana lallashinta ,cikin wata iriyar murya ta kalleta tana fadin,
_"Mama amina wallahi ina san Yaya faisal dan Allah kicewa su Abba kar susa ya sakeni"

Hawayanta ta shiga share mata tana girgiza mata kai alamun ta daina kukan haka.

Haka kowa yabar wajan cike da tausayinta, Mama amina ce ta jata zuwa dakin nata, tana me mata alkawarin zata yi iya bakin kokarinta dan cika mata burin nata.

______
Husna kuwa datayi me isarta itama, Anty Salma ta kira tawaya ta sanar mata abunda yake faruwa har marin da yayi mata.

ko kadan bataji dadin abunda ya faru da ita din ba, dan haka ta sanar mata da tana nan zuwa kuma zata dau matakin hakan.

Sai lokacin taji ranta yayi mata sanyi, wanka tayi taci uban kwalliya kamar yanda ta saba, ta ci abincinta ta koshi dan dama bata wasa da cikinta, tana zaune acikin falonta ,sai faman fadanci take yi, taci kunu dama ita bata yima kuyanginta wasa ko kadan tsakaninta dasu sai kyara da hantara.

_____
Lailah kuwa bayan fitar Dizhwar falonta ta dawo ta zauna tana kunna wayarta da tun jiya Anty Yusra ta kashe mata.
Number Anty Yusrar ta kira dan tana kewar gida sosai.

Tana dauka da murnarta ta furta ,
_"Amarya sai yanzu aka tuna damu, ana can ana shan soyayyah "_

Cike da kunya ta furta,
_"Kai Anty, yakike yasu Abbana ina su Zuhra da Ya Ahmad"_

_"Duk suna nan lafiya kowa yana nan cike da kewarki"_

Kamar tayi kuka, tana san ganin Mama amma babu dama gashi bata magana balle a bata wayar, kwallah ce ta cika mata ido, ahankali ta furta,
_"Nima ina kewarku, dan Allah Anty akawomin Nina kema yaushe zakizo? "_

_"Ayyah Lailah ki kwantar da hankalinki, anayin hutu zan kawo Miki Nina, kuma ki dinga kula da kanki sosai kina yima mijinki biyayyah Lailah kinga kina da kishiya dole sai kina kula"_

Ta gane me take nufi, cikin kunya ta furta,
_"Insha Allah Anty, zan dinga yi"_

_"Yawwah Lailah, Mama tana gaida ke,suma su Nina haka"_

_"Ina amsawa ki gaida su"_
Sallama sukayi, sannan ta kira Aliyu dan ya turo mata number Hibba.
  Dan Anty Yusra ta fada mata ita ta kira su.

Bayan nan kiran Asiya tayi dan dazu basuyi wayar a nutse ba, sun jima suna hira kafin daga bisani suyi sallama.

Tana gama wayar Taji sallama, amsawa tayi tare da mikewa tsaye, ganin Humaira yasa ta sakin murmushi ita da jakadiya.

Zama tayi suka gaisa itama jakadiyar haka.

Ruwa da lemo aka kawowa Anty Humaira.

_"Lailah yakike ya Amarci"_

Dariya kawai tayi tana mejin kunya kalmar, dan gani take kamar kowa yasan abunda ya faru tsakaninta da Dizhwar din.

_"Kinji Asiya ta haihu ko? "_
Humaira ta fada tana kallanta.

_"Eh yanzu muka gama waya da itama"_

_"Ohk, nima ba yanzu zani ba sai ana Suna saura kwana uku, sabo da haka ki Lallaba Ya Dizhwar din ,saimu tafi tare"_

_"Insha Allah"_
Ta fada dan itama tana san zuwa.

_"Jeki saka hijab dinki zamuje dake ki gaida su Baba dasu Hajiya Babba"_

_"toh"_
Tace tare da mikewa ta shiga dakin.


*ZEENASEER*

LAILAH-DIZHWAR page 105 to the endWhere stories live. Discover now