LAILAH-DIZHWAR

1.4K 79 2
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
         🌷🌷🌷🌷🌷🌷
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
          🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*🌼👸🏻LAILAH-DIZHWAR🤴🏻🌼*
  *🌷🌷🌷🌷NA🌷🌷🌷🌷*
  *ZAINAB NASEER SARKI*
       *_ (ZEENASEER😘) _*
       🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

'''Editing by : Ameerah Zarewa'''

*© REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄*
                ☆We the best ☆

ViaWattpad@Zeenaseer01
https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&__tn__=H-R

Email:realhausafulaniwritersforum@gmail.com
Facebook:www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITTERSFORUM.com

*141*

_"Fareeda me yasa zaki ce haka, dan Allah kiyi hakuri mu koma tare, Mun damu ki dawo gidan kada kice haka kinji"_
Faisal ya fada yana kallanta.

Batare da ta kuma magana ba ta mike tare da barin dakin, Faisal din yana kiranta amma saita karasa fita da gudu tana kuka.

Da sauri ya maido kallansa wa Dizhwar din.

Kallansa Dizhwar yayi tare da fadin,
_"Ka kwantar da hankalinka, da alama akwai abunda yake damunta, amma insha Allah zanyi mata magana, nayi maka alkawarin da kaina zan kawo maka ita"_

Dadi faisal yaji duk da yana cikin damuwar abunda yaga Fareedar tanayi.

Godiya yayi masa tare da kara bashi girma kafin yayi mai sallama ya kira Zahra dan su tafi.

Su Mama suma basu jima ba suka tafi gida.

______
Fareeeda koda ta shigo part dinsu dakinta ta shiga tana kuka.

Abun Mamaki Anty Amarya ta gani zaune kan gadanta da alama jiranta take yi dama.

Da sauri ta mike ganinta tana fadin,
_"Yawwah Fareeda daga ina kike?"_

Cikin kuka ta furta,
_"Meya kawoki cikin dakina, ki fita ki bani waje tun kafin inyi miki abunda bazaki manta bah"_

Anty Amarya da ranta yayi mugun baci ta furta,
_"Wai fareeda Kina da hankali kuwa, ya za'ai ina miki magana kina min wani abu kamar Sa'ar ki, na gaya miki sharrin shaidan ne, dukkan abunda nake miki bakya gani, dan yau nayi kuskure sau daya saiki daga hankalinki"_

Abun ya kuma batama Fareeda rai hakan yasa taci gaba da kuka.

Da sauri Anty Amarya ta matso kusa da ita tana fadin,
_"Dan Allah ki rufamin asiri yata dan Allah"_

Dago da idanta tayi da sukayi jajir tana kallan Tah, cikin rawar murya ta furta,
_"In har kika fadamin gaskiya tsakaninki da Allah wanene Mahaifina, nayi miki alkawarin har duniya ta nade daga bakina babu mejin wannan maganar saidai in kamaki akayi"_

Cikin rudewa da tashin hankalin Anty Amarya ta furta,
_"Fareeda memartabane mahaifinki, shine babanki, kawai dan kin ganni haka tau shikenan sai aka ce miki haka nake, yanzun ma kawai tsautsayine"_

Hakan yasa ta kuma fashewa da kuka,
_"Wallahi in har bazaki fadamin gaskiya ba saina tona miki asiri kowa yasan ke wacece"_
  Tana fadar haka ta mike tare da ficewa daga cikin dakin.

Binta da kallo Anty Amarya tayi tare da fadin,
_"Baki da hankali yarinya, zan nuna miki koni wacece"_
Ta fada cikin zuciyarta.

________
Dizhwar ne ya shiga dakin Husna da dare danyimata sallama yana san zuwa ya kwanta.

Kwance ya ganta tana chat yaran yana gefe yana bacci.

Batare daya kulata ba ya dauki yaran yana kallansa.

LAILAH-DIZHWAR page 105 to the endWhere stories live. Discover now