LAILAH-DIZHWAR

1.2K 78 2
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
         🌷🌷🌷🌷🌷🌷
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
          🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*🌼👸🏻LAILAH-DIZHWAR🤴🏻🌼*
  *🌷🌷🌷🌷NA🌷🌷🌷🌷*
  *ZAINAB NASEER SARKI*
       *_ (ZEENASEER😘) _*
       🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

'''Editing by : Ameerah Zarewa'''

*© REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄*
                ☆We the best ☆

ViaWattpad@Zeenaseer01
https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&__tn__=H-R

Email:realhausafulaniwritersforum@gmail.com
Facebook:www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITTERSFORUM.com

*139*


Koda Lailah ta fito daga dakin Mami, zaune ta ganta tayi shiru da alama akwai abunda yake damunta.

cikin sanyin jiki ta karasa tare da durkusawa a gabanta, cikin sanyin murya ta furta,
_"Mami xan je part dina saida safe"_

Da sauri ta dago tare da fadin,
_"Toh Lailah baki tsayawa yau kici abinci anan"_

Murmushi tayi tare da fadin,
_"aa bana jin yinwa"_

_"Toh Allah ya kaimu, Lailah karkisa abun cikin ranki, Husna insha Allah zata gyara halin tah"_

Murmushin yake tayi tare da fadin,
_"Babu komai Mami, zai iya yiwa ta gaji shiyasa bata fito ba, kuma kinga tayi baki da yawa tunda mu yan gida ne ai danmu yana nan"_

Cikin jin dadi da yayewar damuwar tata ta furta,
_"Toh, Allah yayi miki albarka ya saukeki lafiya"_
 
Ciki ciki tace Ameen din dan kunya, mayafinta ta yafa ta fuce daga part din, zuciyarta cike da damuwa kuma tana dada godema Allah daya bata juna biyu itama, ko a hanya taga yaro taso daukarsa aka hana ta bata jin dadi, ballan tana dan gidan Dizhwar a hanata shi, gaskiya taji haushi amma tasan lokacine, itama inta haifi nata babu wanda zai daukar mata shi.
Da wannan tunanin ta isa part dinta, inda kuyanginta suka bi bayanta dan jin ko tana da bukatar wani abun,

Fruit salads me sanyi kawai tasa ayo mata dan ta jika makoshinta.

_______
Dizhwar kuwa koda dare yayi kara shiga yayi yaga dansa cike da farin ciki, sai faman washe baki yake yana masa wasa duk da ba Jinsa yake bah.

Kallan Husna yayi da take gefansa zaune tana wani yatsina.

_"Husna yaran nan kuwa yaci abinci, karfa kiga dan yana bacci kiqi tashin shi yaci abinci, kinga zaki cutar min da yaro na"_
 
Banza tayi dashi kanta a gefe dan so take ta dinga ja masa aji.

Jin tayi shiru yasa ya juyo yana kallanta, kafin yace,
_"magana fa nake miki"_

_"Har yanzu ruwan nonon bezo ba, ama yasha madara ai in cikinsa be koshi ba bazai yi baccin bah"_

Juyawa yayi yaci gaba da kallan fuskar yaran yana me kara jin kaunarsa tana shiga cikin ransa.

Ya jima cikin dakin, kamar ya tafi da yaran sannan yayi mata sallama ya fice daga part din.

Kai tsaye part din Lailah ya nufa, inda yana zuwa ya tarar da har ta kwanta.

Shima wanka yayi kafin yazo ya kwanta ya jawo ta jikinsa duk da yasan bacci take.

Da sauri ta mike zaune dan bata da magagin bacci.

Kallan fuskarsa tayi lokacin data kunna fitilar dakin.

Murmushi kawai yake mata kafin yace,
_"Ya kikaga yaro na, naso in kwana dashi amma babu damar hakan, ina sanshi har cikin raina"_

Jin haka yasa ta matsawa jikinsa tare da kwanciya batare data ce masa komai ba.

_"Ya Amar bakice komai bah? "_

_"Masha Allah yaro kam, Allah ya raya mana shi cikin sunna"_

Dadi yaji har cikin ransa tare da rungumeta yana me fadin
_" ameen"_

__________
Yau kwana hudu da haihuwa kullum gida kara cika yake kamar ranar ne suna, yan uwa da jama'ar Allah daga waje, wasu suna ganin yaran wasu kuwa basa gani, haka akai ta zuwa tun da Lailah taje sau daya bata koma ba sabo da abunda aka mata tana gudu karta koma tana ganinsu duk manya ne suyi mata duka su kashe mata dan Cikin nata.

Husna kuwa ji take kamar itace me rikon kujerar mulkin dan gani take ta gama kama gida tunda ta haifi sarki.

Dizhwar ma banda rawar kafa babu abunda yakeyi akan yaran nan hakan nan zai shiga ganinsa saiya shafe awa biyu zuwa uku, abun har mamaki yake ba mutane haka dukkan abunda husna take so shi ake mata.

Haka zalika Memartaba shima da kansa yazo yaga yaran,yayi masa kyaututtuka na musamman dan yana me jin jinin nasa har cikin ransa.

Bangaran su Humaira kuwa babu wanda ya kuma zuwa acikinsu, haka cikin gidan Hajiya Khadijah ce kawai taje Anty Amarya da Fareeda ko a leke.

_______
Tunda Fareeda taji Faisal ya Tare da Zarah hankalinta yayi mugun tashi, ta dinga Kiran Faisal din tana tura masa text kala kala naban hakuri da kuma nadama kan abunda takeyi, dan ko kadan bata jin dadin zaman gidan sabo da irin Soyayyar da take yima Faisal din.

______
Yau ne rana ta Biyar sabo da haka yau Lailah tasa aka dauko yan gidnsu dan suzo su yima Mami barka haka zalika yaune su Zahra sukazo dan yima Dizhwar barka ya kuma koma da Fareeda.

Koda aka kawo su Mama da Anty Yusra dan bata taho da yaro ko daya ba sai Zuhra dake hannunta tana wasa.

Lailah na zaune cikin falonta ita da Zahra suna hira, su Maman suka shigo, cikin farin ciki suka karasa suna me jin dadin ganin Lailah, nan da nan tasa aka kawo musu kayan kwalama da makulashe..

Bayan sun gaisa dasu, da kanta tayi musu iso wajan Mami har Zahra.

Mami tayi musu tarba ta arziki dan taji dadin zuwan nasu sosai, nan suka gaisa suka yi mata barka, sabo da haka sakawa tayi Jakadiya tayi musu Iso zuwa part din Husna.

_______
Asiya kuwa tana cikin dakinta duk abun duniya ya isheta dan haka tashi tayi ta nufi dakin Mommyn tata dan sanar mata da abunda yake damunta.

Kai tsaye ta fito falon nata ganin babu kowa ta huce Babban falo nan ma shiru abun yayi mugun bata mamaki sabo da haka dakin Anty Amarya ta nufa shima bata ciki hakan yasa ta nufi bedroom dinta daba kasafai ta fiya zama ciki ba saide in bata da lafiya.

Cikin sanyin jiki da kuma maganganun da take san mata duk da tasan bazata ji dadin su ba ta nufi dakin.

Ahankali ta murda cikin sa'a kuwa ta jishi a bude.shiga  tayi kuma tayi mugun gamo inda ta kasa koda motsi daya sabo da abunda ta gani yayi mugun bata mamaki, da baya da baya ta fito daga dakin,inda Anty Amarya tayi saurin sakkowa daga kan gadan tana kallanta.



*ZEENASEER*

LAILAH-DIZHWAR page 105 to the endWhere stories live. Discover now