LAILAH-DIZHWAR

1.5K 101 4
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
         🌷🌷🌷🌷🌷🌷
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
          🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*🌼👸🏻LAILAH-DIZHWAR🤴🏻🌼*
  *🌷🌷🌷🌷NA🌷🌷🌷🌷*
  *ZAINAB NASEER SARKI*
       *_ (ZEENASEER😘) _*
       🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

'''Editing by : Ameerah Zarewa'''

*© REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄*
                ☆We the best ☆

ViaWattpad@Zeenaseer01
https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&__tn__=H-R

Email:realhausafulaniwritersforum@gmail.com
Facebook:www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITTERSFORUM.com


*125*


________
Lailah kuwa koda suka dawo daki ta shige, Babu kowa sai Asiya tana bama Ayman Nono, Zama tayi tare da cire Hijab dinta tana kallan su ita da dan nata.

_"Da fatan an dace? "_
Asiya ta fada tana kallan Lailah.

_"Alhamdulillah"_
ta fada cike da farin ciki.

_"Masha Allah, gaskiya Lailah kinyi namijin kokari, Allah ya kara imani, dan gani nake konice ba lallai na hakura cikin sauki ba fah"_

Batare da tace komai ba ta mike tare da komawa kusa dasu tana lekashi.
  idansa biyu ya kama Nono sai sha yake.

Ahankali tasa hannu ta dan janyeshi daga jikin Nonan tana Murmushi  dan ganin yanda zanyi,

Dariya tayi ganin yana shade bakinsa, sai ta maida kanshi wajan ta dago tare da kallan Asiya.

_"Asiya dan Allah in kika dauki Yaran nan ya kikeji acikin ranki"_

_Uhmm! kamar ya kenan? "_
  Asiya ta tambaya tana canza masa zama.

_"I mean wani irin feelings kike ji gama dashi, nifa dani nake kamar baki damu dashi bah"_

Kallan Lailah tayi ido cikin ido tare da fadin,
_"Lailah kenan, kinsan yanda Uwa take ji akan danta, toh duk wata soyayyah da kike gani a fadin duniyar nan,bata kai ta soyayyar uwa da da bah,duk Uwar data ce bata san danta, wallahi karya takeyi, so ne wanda yake bin dukkan jinin jiki, sone da ba'a  hada shi da ko wane irin so Lailah, kema mace ce, kuma kina da aure ina fatan Allah ya baki da kiji yanda son yake"_

Tana san taji ana maganar Yaro Rayuwarta.

_"Asiya nifa ji nake, inna haihu bazan iya bawa kowa dana ba, sabo da son da nake masa, ma sai inga har ajjeshi kike ki tafi ki barshi"_

Dariya Asiya tayi tare da fadin,
_"Lailah inma na ajje shi xanzo in daukeshi, sabo da nasan nawane, kuma ba wanda zai shayar min dashi mundin ina Raye"_

Kallanshi ta kuma yi tare da shafa kyakkyawar sumarsa.

Ta mike ta canza kayan jikinta tare dayin alwala.

Zuwa tayi tahu gadan ta kwanta.

_"Lailah bakici abinci ba kika kwanta"_

Juyowa tayi tare da fadin,
_"Cikin bana jin yinwa, jikina ciwo yake, duk wannan fitinan nan yayan naki ya gajiyar dani"_

Dariya Asiya tayi, yayin da itama Lailah dariya ta juya.

_"Wallahi nazatama a wajansa zaki kwana"_
Asiya ta fada.

Batare data juyo ba ta furta,
_"Na barwa Anty Husna daran kam, danni bacci nake ji"_

________
Washe gari tunda safe Jafar ya gama shirinsa na tafiya, cikin manyan kaya, ya fito yayi kyau dashi sai kamshi yake, dan de ya danyi rama kadan.

LAILAH-DIZHWAR page 105 to the endWhere stories live. Discover now