LAILAH-DIZHWAR

2.2K 139 38
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
         🌷🌷🌷🌷🌷🌷
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
          🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*🌼👸🏻LAILAH-DIZHWAR🤴🏻🌼*
  *🌷🌷🌷🌷NA🌷🌷🌷🌷*
  *ZAINAB NASEER SARKI*
       *_ (ZEENASEER😘) _*
       🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

'''Editing by : Ameerah Zarewa'''

*© REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄*
                ☆We the best ☆

ViaWattpad@Zeenaseer01
https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&__tn__=H-R

Email:realhausafulaniwritersforum@gmail.com
Facebook:www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITTERSFORUM.com

*END*

Haka Lailah akaita cin kwa-kwa Dizhwar kuwa yana nan yaki motsawa daga inda yake, yana rike da ita tana faman kakkafewa yayi mugun tausaya mata ji yake kamar ya maida ciwon jikinsa.

Cikin ikon Allah 5am na ranar Litinin ta haifi yarta santaleliya mace.

Ana cirota ko zani ba'a saka mata ba Dizhwar yayi maza ya amsheta yana kallanta cikin kuka yake godema Allah yana kara rungumetah ajikinsa kamar zai maida ita ciki.

Lailah kuwa jin kamar an cire mata kaya yasa ta kwanta kan pillow tana hutawa.
Jakadiya ita tayi wannan aiki da kanta, yayin da Mami ta koma waje ta zauna dan ganin Dizhwar  yaki basu waje.

Da er ya bawa jakadiya ta sakata cikin towel Mami dake waje aka kaima, cikin yima Allah godiya itama ta dauketa tana kukan farin ciki da murna.

Shikuwa koda Jakadiya ta fita rungumetah yayi yana shi mata albarka yana kukan farin ciki.

Shiru tayi dan har yanzu bata gama dawowa daga hayyacinta ba, lallai yau ta kuma tabbatarwa Allah da girma yake, wato haihuwar da ake fada dama haka take, tabbas inde yaro bai yima iyayansa biyayyah ba ya shiga uku, dole mutum ya tabe dan uwa tafi bakin komai,
(Allah yasa mu dace).

Banda sannu, babu abunda yake jero mata, da kuma kalaman Soyayyah masu dadi da kuma sanyaya zuciya.
hakan yasa itama ta rungumeshi tana kukan farin cikin tare da kara yima Allah godiya daya bata Dizhwar din a matsayin mijinta me kaunarta.

Ahaka su Mami suka tarda su, inda ta korashi waje.

Wanka yaje yayi ya nufi masallacin cikin farin ciki, yana me tausayin kansa, inama Jafar yana nan yau shima yaga Babynsa yaga abunda Lailah ta haifa masa, a ranar yayi kukan rashin Jafar sosai dan yaso yana nan aka haifa masa da shima.

_____
Kafin safe an yima yarinya wanka an saka mata tufafinta masu kyau da tsada tana kwance kan dan gadanta duk wanda yazo nan yake ganin ta kwance.

Nan da nan gida ya cika da yan barka, kamar  masoyan Dizhwar din zuwa na Lailah sabo da duk da kankantar ta ta kasance tana da tausayin mutane da kuma kyauta.

Su Mama ana gaya musu suka taho haka Aminu da iyalansa, Anty Yusra da Asiya ji sukai kamar suyi tsuntsuwa suzo suga yar gidan Lailah haka su fareeda.

Maman Jafar itama tazo tana jin labari, jama'a ba'a magana kowa saida yasan da wannan haihuwa haka suma Zeenaseer's fans😉.

Ranar kowa cikin farin ciki yake a wannan gidan,itama me jego tayi wanka tayi kyau abunta, motsi kadan idanta yana kan yarinyar nan da take ta faman bacci abunta.

Su Humaira kuwa yan kusa suna nan duk sun zo, kowa yaga babyn dai yayi santi tah.

______
Washe gari gida cika yayi da mutane, daga gari gari duk sun zo dan ganin Dizhwar's Princess din.

Asiya itama kamar ta cinye yarinyar nan sai santi take yi, dan ajje Ayman tayi ta dauke ta.

Haka Itama Zahra ji take dama yarta ce.

Kowa de yana kaunar yar babyn tamu😉.

______
Ranar suna gida cika yayi da yan suna, tsayawa lissafa wanda suka zoma aikine, dukkan wanda ya dace yazo sunan nan, yarinya taci sunan hajiyar jafar kamar yanda Lailah tayi akawari an saka mata *Nana Bilkisu* Babanta ya zaba mata sunan da za'a dinga kiranta wato *Aamanee (Good wish)*

Taro yayi taro anci ansha, ansha rabon abubuwa kowanne liqe da hoton yarinya, Haka ta samu kaya bila'a dadin, haka babarta.

Kakanta mota ya bata kyauta guda, yayin da Faisal ya bata kyautar gida, haka Mutane suka dinga mata kyautuka masu dumbin yawa da kuma tsada.

Haka aka watse cikin farin ciki da kuma kwanciyar hankalin.

______
Ko yan kurkuku saida sukaji dadin ranar sunan nan, dan suma sunci abinci mekyau kamar yanda Lailah ta bukata.

Husna da taji wannan labari tayi kuka sosai, kuma bata taba yin nadama akan abunda take aikatawa ba sai yau, tayi nadama sosai dan batayi tunanin lailah zata haifi abunda ke cikinta lafiya bah, tabbas tayi imani babu wanda ya isa yayi abunda Allah beyi ba, sabo da haka yanzu ta gane gaskiya kuma tana me yin tarin nadama acikin rayuwarta tana fatan Allah xai yafe mata dukkan abunda take aikatawa acikin duniyar nan.

______
Yarinya ta taso cikin gata da kuma soyayyar iyaye yan uwa da kuma masoya, haka ta tashi cikin tarbiya san mutane da kuma biyayyah duk da kananin shekarunta, tayi wayo sosai dan har ta shiga makaranta, tana da shekara hudu mamanta ta je tayi karatunta na degree a qasar Turkey (MBBS)wato medicine👩‍⚕ta fito matsayin babbar likita,Bayan ta kammala ta kuma haifar yan biyu Hassan da kuma Hussein.

Haka Ayman ya dawo hannun Lailah da zama kamar yanda Mamanshi tayi alkawari duk da Hajiyar Jafar ta goyi bayan hakan amma da farko Mami kin yarda tayi, akan kaishi kano yayi hutu in lokaci yayi ya dawo gida.

shima suna bashi kulawa sosai dan yana tunanin lailah da Dizhwar ne iyayansa ya saba da Aamanee sosai haka yana sonta in kaga Ayman zakaga Aamanee.

Bayan Asiya ta yayeshi aka sha bikinta da Aliyu inda suka tare anan zamfara.

Fareeda ta haifi danta namiji haka itama Zahra.

haka itama Asiya ta haifa ma Aliyu yaro namji.

itama zakiyya yaranta biyu yanzu.

Abunde sai wanda ya gani, yanzu duk sun hade kansu suna cikin zaman lafiya da kuma soyayar juna.

Kamar yanda Lailah tayi alkawari Aamanee nada kwana goma ta dauketa ta kaita har wajan Husna ta nuna mata yar tatah, sannan tayi mata nasiha me tsuma jiki, wannan karan taji kuma ta dauka tayi godiya ta kuma roki lailah ta yafe mata.
haka ta yafe mata duniya da lahira.

Haka LAILAH-DIZHWAR suka kasance cikin farinciki na har abada tare da yaransu, yan uwa da kuma abokan arziki.


Toh jama'a duka duka anan na kawo karshan wannan yar basirar tawa da Allah yayi min, kuma ina me gode masa daya bani ikon kammalashi lafiya batare da wata matsala ba.

*Godiya ta musamman ga mahaifiyata*

*Sannan ina mika godiya ta musamman ga Babbar aminiyata kuma. masoyiyata wato Ameerah Zarewa,Allah ya saka miki da alkairi bisa gudun mawa da kika bani wajan yin wannan typing Nagode sosai Allah ya saka da alkhairi Ubangiji ya kawo miji na gari*

*Sannan ina mika godiya ga dukan masoyana ko aina kuke ina tare daku, Allah ya barmu tare ubangiji ya hada fuskokinmu a gidan aljanna❤*

*Godiya ga dukkan grps da ake posting novels dina, kuma godiya ta musamman ga dukkan hausa writers❤*

*Sai kuma Allah ya kara hadamu anan gaba inda rai da rabo*

*Alhamdulillah!  Alhamdulillah!!  Alhamdulillah Allah kuli halin*❤

*Allah ya sada mu da alkhairinsa..ya yafe mana kuskuranmu Ameen*🙏🏻


*ZEENASEER*

To już koniec opublikowanych części.

⏰ Ostatnio Aktualizowane: Sep 16, 2018 ⏰

Dodaj to dzieło do Biblioteki, aby dostawać powiadomienia o nowych częściach!

LAILAH-DIZHWAR page 105 to the endOpowieści tętniące życiem. Odkryj je teraz