LAILAH-DIZHWAR

1.3K 97 7
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
         🌷🌷🌷🌷🌷🌷
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
          🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*🌼👸🏻LAILAH-DIZHWAR🤴🏻🌼*
  *🌷🌷🌷🌷NA🌷🌷🌷🌷*
  *ZAINAB NASEER SARKI*
       *_ (ZEENASEER😘) _*
       🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

'''Editing by : Ameerah Zarewa'''

*© REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄*
                ☆We the best ☆

ViaWattpad@Zeenaseer01
https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&__tn__=H-R

Email:realhausafulaniwritersforum@gmail.com
Facebook:www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITTERSFORUM.com

*131*

________
Yau akayi sadakar uku, gidan cike yake da baki na nesa dana kusa, kama daga kan dangin Abbanshi, abokansa dana iyayansa, da sauran jama'a wanda akayi zaman mutunci dashi.

In kaga Dizhwar da Asiya sai kayi tsammanin sunyi cuta ta tsawan shekara har ita kanta Lailah.

Babu me iya lallaba Asiya ko Dizhwar din suci wani abun sai Lailah, ita ke iya kwantar musu da hankali ta sama musu nutsuwa haka tana kula da Ayman yanda ya kamata, tunda akayi mutuwar nan bata samun hutu.

Zahra jiya tazo yauma ta dawo da ita da yan gidansu haka faisal, Su Anty Amarya da Fareeda sau daya suka zo, ranar kuma suka koma, Hajiya Khadijah ce kawai ta kwana itama yau zata tafi, haka yan gidan su lailah tun jiya suka zo.

Husna ce kadai bata zo gidan gaisuwar nan bah, hakan kuma babu wanda ya damu da rashin zuwan nata, dan da zuwan da rashinsa duk daya suke.

______
Koda yamma tayi, dan anyi La'asr, Lokacin su Mama suke san tafiya dan Abba ya takura bazasu kara kwana bah, hakan yasa hankalin Lailah ya tashi dan ita tafisan su bari sai gobe sa tafi amma yanzu ai shigar dare zasuyi ga yara harda karamar jinjira.

Fita tayi inda yake zaune, bayan ta gaidashi ya shiga mata sallama, rokansa ta shigayi da Allah da annabi sannan ya yarda gobe da sassafe za'a kaisu tasha.

Sannan ta dawo cikin murna, daki ta shiga inda Su Humaira suke zaune dan suma duk gobe zasu tafi, zama tayi tare da fadin,
_"Anty Yusra kuyi hakuri nayima Abba magana yace ya yarda goban da safe zaku tafi"_

Murmushi kawai yusra tayi, itama tafi san tafiyar duk da babu abunda suka nema suka rasa a nan din, an amshesu hannu bibbiyu tamkar yan gidan.

Sakko Ayman tayi dake bacci abayan tah.

Nina tasa ta miko mata mug dinsa danta bashi ruwa.

Cike da soyayyah take kallansa tare da saka masa kan fidar a baki, yana motsa ahankali tare da rufe idansa.

Humairah kallanta kawai take dan yanda take kula da yaran tamkar danta.

Jin ya kware tayi saurin ajje fidar tare da sakashi kan kafadarta tana shafa bayansa tare da hura masa iska a kunansa tana jijjigashi, hankalinta duk ya tashi.

_"Sai yanzu ya tashi"_
Yusra ta fada tana kallansu itama.

Yana kan kafadarta ta furta,
_"Eh ai akwaishi dayin bacci"_

Murmushi tayi me cike da tausayinsa,
_"Ai har yanzu jaririne tukun yana fara wayo zai daina baccin, dan ma yaran yana da hakuri bashi da rigima"_
  Yusra ta fada tana kallanta.

Hira suke sama sama kafin su kwanta.

Mikewa tayi tare da fadin,
_"Bara inje in kaishi yasha"_
Ta fita tna fada.

LAILAH-DIZHWAR page 105 to the endOpowieści tętniące życiem. Odkryj je teraz