LAILAH-DIZHWAR

1.4K 91 5
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
         🌷🌷🌷🌷🌷🌷
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
          🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*🌼👸🏻LAILAH-DIZHWAR🤴🏻🌼*
  *🌷🌷🌷🌷NA🌷🌷🌷🌷*
  *ZAINAB NASEER SARKI*
       *_ (ZEENASEER😘) _*
       🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

'''Editing by : Ameerah Zarewa'''

*© REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄*
                ☆We the best ☆

ViaWattpad@Zeenaseer01
https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&__tn__=H-R

Email:realhausafulaniwritersforum@gmail.com
Facebook:www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITTERSFORUM.com

*137*

Da sauri ta kuma gyara zamanta tare da fadin,
_"Wannan wata irin magana kakeyine, Memartabah kace bakai bah, shikenan kuma kullum tsarinsa za'a dinga bi, mu kai muke aure bashi ba, sabo da haka dole ni bazan taba haihuwa anan bah sai a asibiti ai wannan kauyancine, dan inna mutu baka da asara shiyasa ka fadi haka, ko kuma wani abu ya samu dana"_.

Cike da mamaki yake kallanta, ko kadan bata iya magana bah, bata da Hankali har yanzu.

_"Bashi kuke aure ba, in ke be isa dake ba toh ya isa da wanda kike aure"_

Dizhwar din ya fada

kuma dolanka ko kana so ko bakwa so ni bazan haihu a gida ba kuma agaban ka Asibiti zani, in yaso ka tura min takarda ta can, ko kuma karka dauki dan in yazo duniya"_
   Ta fada cikin masifa har tana kwarewa.

Shiru yayi dan dama yasan kullum yazo wajanta Sai ta bata masa rai, dan haka mikewa yayi zai fita daga cikin dakin.

_"Ina kuma zaka? "_
Ta fada tare da mikewa tasha gaban sa.

Batare daya bata amsaba kawai ya bita da kallo.

_"Ya muna magana zaka wani tashi ka tafi, baka bani amsa bah, kuma ina da bukatar kudi"_

Da sauri ya kalle ta tare da fadin,
_"Me kuma zakiyi da kudi"_

Zaro ido tayi cikin mamakin tambayar da yayi mata,
_"Wannan wata irin tambaya ce, ciki fa gareni, ina san in kuma wata siyayyar ne"_

_"Siyayyah, Siyayyah bata karewa a wajanki, tunda kika samu cikin nan kike siyayyah, a kallah kin kashe kudi ta Siyayyar Baby kusan 3million, waike wata iriya ce, wallahi babu wani kudi da zan kuma baki, banda kudin da nake baku ina kike kaiwa, wata uku da suka wuce kowa aka saka masa 2Million cikin account dinsa me kikayi dasu, babu abunda kike siya, komai ana kawo muku, duk bayan wata biyu sai an canza muku komai da komai da kuke bukata,kina ci kina sha kina da sutura, ki bar min kudina na bawa mabukata amma kinki, bazan bada ba, kuma na gama magana that's my last decision, a gida zaki haihu, kuma a gabana, dan bana san ayimin abunda ba daidai ba da dana"_
  Yana fadar haka ya fice daga dakin.

Yana fita ta rike kugu tare da fadin,
_"Kan ubancan, ana wata ga wata, Lallai Dizhwar yana san kwafsamin, Tafdijan!"_
  Ta fada.

da sauri ta janyo wayarta tare da zama ta shiga kiran Anty Salma dan sanar mata da sabuwar gwaramar data taso musu.

Bugu biyu ta dauka,
_"Ya akai Uwar biyu, uwar gidan Memartaba"_
Anty Salma ta fada.

_"Hmm, Anty akwai matsala fah"_

_"Tame? "_
Ta tambaya.

Nan ta kwashe dukkan abunda Dizhwar ya fada dan gane da haihuwar tatah.

_"Dankari! "_
_"Karki samu damuwa, insha Allah babu abunda zai gagara kede ki zauna cikin shiri, gobe ne fadan karshe"_

_"Anty Ki gayama su Ummi (Umman Husna) kar tace ba'a gaya mata bah"_

LAILAH-DIZHWAR page 105 to the endWhere stories live. Discover now