Yace daga dukkan alamu zata taimaka mana sosai a cikin tafiyar mu.
Yace kije kishafa ta manah sannan yakamata kibata suna.Taje gun inda tsuntsuwar take ta shafata sai tsuntsuwar ta rufe idanuwanta sai mayiesha tace inaga zankirata raunat.
Munawwar ya kalleta sannan yace kenan ni tawa tsuntsuwar runat kekuma taki raunat.
Tace eh hakane daga yanxu zandinga kiranki raunat ai kuwa kamar tsuntsuwar taji abunda tace tayi qara mai sauti sosai sannan ta tashi sama ta tafiyarta.
Tana wucewa sai munawwar yace yanxu na biyu shine na koya miki yadda zaki sarrafa takobinki.
Yana koya mata daki daki yadda zatayi itakuma tana saurin koya sbd duk abunda yakoyamata da wuri take iyawa.
Bayan sun gamane sai yace da ita kizo muje na nuna miki wani gurin.suka jera suna tafiya sai surutu take zuba mishi.
Ya kaita gun wani dutse mai girma sosai ya tsaya sai tace wai dama dutsene kakeso kanunamun to meye abun birgewa anan.
Yace kitaba dutsen tace idan na taba mezai faru
Yace to kidai taba tukunna.Tana tabawa sai dutsen yafara tsagewa yana gama tsagewa sai ga wani guri mai kyan gaske ruwa suna zuba ta ko ina ga fulawowi masu kyau da kala kala.
tace amma wannan gurin yayi matukar birgeni sosai suna shiga ciki yace zaki iya cin komai da kika gani anan sannan kuma zaki iya taba komai amma banda wadannan koren ciyawarTace idan kuma nataba mezai faru yace mutuwa zakiyi
Tayi dariya sanan tace tunda nazo wannan gun bantaba ganin wani abu mai cutar wa bah to meyasa yanxu zakacemun wai wannan ciyawar tana cutarwa.
Sai yace sbd ciyawar aljannu ce.
Tace to shikenan naji bazan tababa.
Suna cikin tafiya sai tace nifa saina taba naga mezai faru.Yana cikin tafiya saida ta tabbatar hankalinsa ya dauku sannan taje ta taba koren ciyawar
tace amma wadannan ciyawun akwai taushi da kanshi mai dadi.Munawwar na juyowa yaganta tana taba koren ciyawun yasaki wata irin qara yaje gunda take da sauri.
Tace kada ka damu lafiyata qalau nake ba abunda yasameni.
Ya janyo hannunta cikin fushi suka fita daga gurin.
Aikuwa suna fitowa tace munawwar kaina yanamun zafi aikuwa kafinya ankara kawai saita fadi sumammiya.Cikin firgici yayi sauri ya dauketa yayi sama da ita basu sauka a ko inabah sai cikin dakinsa.
Yayi saurin hada magani ya bude dukkan jikinta yana shafa mata.nan take yayi sauri yafita waje cikin murya mai sauti yakira sunan tsuntsuwarshi ma'ana runat.
ta iso gunsa da sauri yace taje ta samomishi ganyen furen fulawar ruwa.
Aikuwa ba bata lokaci ta kawo mishi yana karba yayi saurin jikashi da ruwa ya kunce gashinta yana zuba masa ruwan amma dukda hakan bata farfadobah.
Yatabi zuciyarta kuma sam bata bugawa.
Nan take yasaki wata irin qara ya hau kuka yana cewa haba mayiesha meyasa zaki mutu kibarni nikadai a cikin wannan duniyar da ba kowa a cikinta.Yana ta kuka yana bubbugata.
Nan take yaji tayi ati shawa.
Yana kalonta sai yaga tana numfashi sama sama jikinta yana sakin wasu irin kuraje manya manya.
Nan take yayi sauri yaje ya dago fuskarta sannan yasaka inwak dinshi a goshinta sai wani haske yadinga fitowa daga jikin inwak din yana shiga jikinta.Aikuwa nan take bahij dinta yadau wani irin haske sosai yama haskake dukkan jikinta.
Tare da qarfin tsafin inwak da bahij nan take kurajen suka bace gabaki daya.
Yanata kallonta yana cewa mayisha kitashi dan Allah kada kimutu kibarni cikin duniyar kadaici.
Sannu sannu sai ta bude idonta suka sauka cikin nashi ta daga hannunta sai kuma ta saukar nan take wanni bacci ya dauketa.Sai munawwar yatashi yaje yayi alwalla yayi sallah sannan yadinga yi mata adduoi bayan kusan awa biyu sannan ta farfado.
Yana xuwa gun inda take tace dan Allah ka gafar ceni munawwar tabbas na kasance wadda batada godiya kokadan.
Sannan bayan duk taimakon da kayimun gashi inason na bijire maka.
Yayi murmushi yace ba komai mayiesha Allah dai yabaki lafiya.
Tace ameen sannan ta saukar da idanuwanta akan jikinta sai taga ba kaya a jikinta daga ita sai tajeruwar riga tasaka wani irin ihu ta lukume cikin bargo.
Munawwar yace lafiya dai mekuma ya sameki.Tadago kanta daga cikin bargo tace meye dalilinka na ciremun tufafi yace nashafa miki maganine.
Tace kashafamun magani
Kana nufin ka shafi jikina.
Yace ai taimakonki nayi.Sai tayi sauri ta rufe idonta nan take tufafi suka bayyana a jikinta sannan ta tashi tsaye tanajin kunyar hada ido dashi.
Tace zantafi dakina.
Yace kibari har kigama warkewa sbd ban yadda nabarki kekadaibah.
Tace to sbd me
Yace watakil ciwon zai sake tashi.
Tace kenan kana nufin a daki daya zamu dinga bacci.
Yace eh hakane
Tace to ai babu kyau mace da namiji sukwana a guri daya
Yayi murmushi sai yace ai kuma wannan larura ce.
Tayi shuri sannan tace yanxu dai kabarmun dakin nadan shirya
Yafita itakuma tashirya sanan tayi sallah.
Tana gamawa sai tafito waje ta ganshi zaune yana wasa da runat.Yace yanxu yakike ji tace ba abunda nakeji kawai cikina yakemun zafi.
Yace to muje nadubaki
Ta harareshi sannan tace kamar ya kadubani kenan na bude maka cikina kome kake nufi.
Yayi dariya sannan yace ba haka nake nufibah.
Suna shiga daki sai ta kwanta shikuma ya aza inwak dinshi akan cikinta sai yayi haske sosai sosai.
Sai yace to shikenan nagama dubaki kuma lafiyarki qalau kawai yunwace kikeji bari na hada muna abunci.
Yana rufe idansa saiga abunci masu lafiya kala kala a gabansu.
Sukaci saida suka koshi sannan yace yanxu ki kwanta kidan huta tunda dare yayi.
Ta kalleshi sai tace to kaikuma ina zakayi bacci yace a kasa zan kwanta
Tace to shikenan nagode da kula dani da kakeyi da badan kaibah da yanxu namutu.
Yayi murmushi yace ba damuwa kawai dai kidinga yin abunda nace dan Allah sbd kinga nafiki sannan wannan gurin.
Tace kayi hakuri inshallah bazan sakebah.
Yace to saida safe suka kwanta.
Duk bayan wani dan lokaci yakan tashi yaga yatake sannan yakoma bacci.
By maryam ashutrah
YOU ARE READING
MAYIESHA
Short Storylabarine akan wata mace jaruma wacce kwasam bazato ba tsammani ta tsinci kanta a cikin wata duniya. Shin ta hadu da qaddarar tane kokuma mutuwarta. Kubiyoni domin jin yadda ta kasance