Bayan wani lokaci.
Abba yana zaune a shagonsa yana kirgan wasu yen kudade.
Shikuma munawwar Yana cinikin kaya da wasu yen mata.bayan sun gama sai daya daga cikinsu tace idan bazaka damubah zan iya samun number wayanka.
Yace banida waya
Tace babban yaro irinka bakada waya.
Yace ehh sai abba yataso yace yen mata wannan fah mijin aurene yana da iyali dan Allah kutafi.
Cikin mamaki suka wucewarsu suna cewa amma ai wannan baiyi kama da mai matabah.Abba yace kadena biyewa wadannan yen matan yen iskane saisu lalatawa mutum tarbiyya.
Munawwar yace inshallah abba bazan sakebah.
Suna zaune shida abba a shago saisuka fara jin hayaniya a waje suna fitowa sai sukaga wani barawone yayi sata yanata gudu mutane nabinsa.
Cikin sauri yana isowa gefen shagon su abba,sai munawwar yabishi da sauri yarike shi.
Cikin bacin rai yakaiwa barawon wani irin naushi sai kawai ganinsa akayi kwance a kasa ya suma.
Mutane suka iso gurin sunata yiwa munawwar godiya daya samu ikon kama barawon.
Saiga wata hajiya fara kyakkyawa mai jiki ta iso gurin itada qawayenta
Munawwar ya dauki jakar daga hannun barawon ya mika mata yace hajiya ga jakarki.
Ta kalleshi tayi masa godiya sannan tace dan saurayi ya sunanka yace sunana munawwar.
Ta dauko wasu yen kudade daga jakar ta mika mishi yaki ya karba.
Tace ka chanchanci hakanne dan Allah kada kaki karba bazanji dadibah.
Sai kawai ya karba yayi mata godiya tashiga mota itada qawayenta suka fice.
Shikuma yakoma shago.Yana xuwa sai yake nunawa abba kudin.
Abba yace ai wannan kudine masu yawa har dubu goma.Ya mikawa abba yace gashi sbd nikam bansan mezanyi dasubah.
Abba yace a'a munawwar wannan hakkinkane bai kamata na karbaba.
Yace to ni yanxu abba yazanyi dasu.
Yace kaga yakamata kasamu koda yer qaramar waya irin ta dubu uku saika siya sbd yakamta ace ka iya waya sannan kuma idan ina wani gun zan iya kiranka.Yace hakane amma zansiyawa qanwata sbd itama mudinga waya.
Abba yayi murmushi yace to ba damuwa idan muka tashi aiki sai muje na rakaka kasiya har da layi da komai.
Suna tashi daga kasuwa abba ya rakashi gunda ake siyarda wayoyi suka siya guda biyu da layuka akayi musu rijista sannan suka wuce.
Suna cikin adedeta zasu koma gida sai munawwar ya hango mai kaji.
Nan take yacewa mai adedeta din daya tsaya.
Yafita yaje yasiyo kaji guda biyu gasassu da kuma lemun kwalba guda hudu dakuma abubuwan hada shayi irin madara da lipton da kuma bredi da suga duka sannan ya wuce zuwa adedeta,suka fice zuwa gida.
Suna isa gida suka shiga da sallama mayiesha na parlor itada umma tana kwance saman kafafuwan umma sai zuba mata surutu takeyi suka jiyo sallamar su.
Da sauri mayiesha ta fita tayi musu sannu da zuwa sannan ta taya munawwar karban kayan dake hannunshi.Suna isa parlor suka zauna sai munawwar ya gaida umma
Cikin farin ciki ta amsa sai ya mika mata kayan shayi da ledar kwai yace umma gashi gobe da safe shayi zamusha da wainar kwai.
Tace to shikenan dana Allah ya kaimu sai kuma ya mika mata ledan kaza yace wannan keda abba nikuma wannan nida qanwata.
Ta karba tace Allah yayi maka albarka munawwar dama ace inada da irinka danaji dadi.
Nan take ya bata fuska ya kalli abba yace kaji fah abunda umma take cewa kenan niba danta bane.
Umma tace ai nikam ban isa nace haka bah wasa nake maka.
Yayi murmushi sannan tace yer qanwata akwai abunda nasiyo miki rufe idanki.
Su umma suka tashi suka fice zuwa daki dan acewarsu bazasu zauna suka kallon shiririta irin ta ya'yan nasubah.
Tana rufewa sai ya dako wayan yace to bude idanki.
Tana budewa yace surpriseTa karbi wayar cikin jin dadi tace kaii amma natayaka jin dadi ka siya waya.
Yace ke batawa bace takice gatawanan.Tayi tsalle ta rungumeshi yace nagode yayana.
Yace yanxu kinga koda idan ina kasuwa zan iya kira naji yakike.
Tace hakane.
Kuma kinga iri daya na yimana.
Yanxu dai yunwa nakeji ki dauko mana plate muci kazarmu.
Tace to.Hajiya salamatu na zaune a parlor sai tunanin take tayi saiga hajiya zinaru tashigo parlor din.
Ta zauna kusa da hajiya salamatu tace hajiya lafiya tunda muka dawo kasuwa nakasa gane miki.
Hajiya salamatu ta kalleta tace wlhy hajiya zinaru tunda na kalli wannan yaron wanda ya taimakeni a kasuwa sai ya tunamun da dana wanda yabata.kuma gashi sunansu daya bayan hakan suna dan kama.
Hajiya zinaru tace tabbas hakane sbd nima dana ganshi saida naji gabana ya fadi.
Hajiya salamatu yace to kodai shine dana wanda ya bata.
Hajiya zinaru tace haba hajiya ki kalli wannan fah dan talakawane daga ganinshi kuma danki ai ba wanda yasan ko wace ma duniyar yake.
Tace hakane amma zanso naje naji tarihin sa.
Hajiya zinaru tace to kinsan mezai faru zan saka anemomuna inada suke zama idan yaso sai muje chan kinga yafi mutunci
Amma dan Allah kisaki ranki.
Tace to naji.
Washe gari da safe bayan dukansu sun shirya fita sai mayiesha tace yaya nikam bansan inda na ajiye hijabina na makarantabah kuma gashi tun jiya dana wanke uniform dina ban wankeshibah.
Yace to saiki saka wani mana
Tace uniform daya nakeda.
Amma kudan jirani bari naje nan gidansu qawata fatima idan bata wuce makarantabah saina aro mara guda daya.Sai yace to kiyi sauri kafin abba yafito.
Tana fitowa tawuce zuwa gidansu fatima tana shiga sai tayi rashin sa'a batanan.
Sai maman fatima tace amma bari naduba miki.Tana dauko mata ta bata sai mayiesha tayi godiya tayi saurin komawa gida.
Tana saka hijab din munawwar yace uniform dinnan na makaranta yana miki kyau.
Tace ai kai komai idan nasa haka kake cewa saiga abba yafito yace to kuwuce muje kada ki makara.
Umma tace to Allah yabada sa'a
Dukansu sukace ameen.
By maryam ashutrah

ВЫ ЧИТАЕТЕ
MAYIESHA
Короткий рассказlabarine akan wata mace jaruma wacce kwasam bazato ba tsammani ta tsinci kanta a cikin wata duniya. Shin ta hadu da qaddarar tane kokuma mutuwarta. Kubiyoni domin jin yadda ta kasance