This page is dedicated to my best friends Allah yaqaro muku shekaru masu yawa.
Sannan kuma ina godiya ya ma'abota karatun wannan littafin mai suna MAYIESHA
Da fatan kuma yana qayatar daku sosai.much luv🎆🎆🎆🎆
Tayi knocking ba'a budebah ta qar knocking harsau uku nabila bata budebah tace watakil har tayi bacci tajuya zata fice sai aka bude kofar.
Nabila tace lafiya
Dama ice cream ne nace na kawo miki
Nabila ta karba sannan tace thanks ta shige daki ta rufe.
Mayiesha tace Tabb wannan yarinyar akwai rashin kunya.
Ta haura sama munawwar yace yawwa akwai maganarda zamuyi.
Ta zauna sannan yace kinga admission dinmu na london zai dan dade kafin yafito sbd haka zamu fara karatu anan kinga idan ya fito kawai sai muwuce.
Tace kuma wannan shawarar tayi.
Sbd haka nayi magana da abokina gobe zamuje wata university nan kusa ayi duk abunda yakamata.
To Allah yakaimu goben yace ameen.
Da safe tana kitchen suan hada breakfast shikuma munawwar yana parlor yana kallon morning news itakuma nabila tana daki sai faman bacci takeyi.
Munawwar yatashi yaje kitchen yana shiga yen aikin duka suka duka suka gaidashi ya amsa sannan yace mayiesha zo kiji.
Ta iso gunshi ya janyo hannunta suka fito waje sai yace wai anya yarinyar nan tayi sallar asubah kuwa.
Tace aww wai nabila tabb inaga fah bata tashibah amma bari naje nagani.
Tafice zuwa dakin nabila ta shiga da sallama ta hangota kan gado tayi rubda ciki sai shakan bacci takeyi.
Ta isa gunta sannan tace nabila
Nabilaa!!
Tana bude idonta tace wai meye haka ina bacci zaki tadani lafiya.
Kinyi sallah
No banyibah tana fadan haka ta juya kwanciya
Mayiesha tace kitashi mana kiyi sallah idan yaso saiki koma baccin.
Nabila tatashi zaune tace wai lafiya kikeson takuramun ni ina takuramiki me kodan sbd ina gidanki.
Mayiesha tace Allah ya baki hakuri ta fita.
Ta tarar da munawwar a parlor tace taki ta tashifah wai ina takura mata.
Yace aikuwa idan har zata zauna a gidannan to wlhy sai tayi sallah ya tashi a fusace ya nufi dakinta.
Mayiesha kam kawai kallonshi tadingayi.yashiga dakin nabila yace nabilaa!! Tatashi da sauri yace kitasho kiyi sallah kina jina koh.
Tace wai meyasa kukeson takuramun kawai sbd nazo gidanku.
Yace antakura miki din dalla malama kitashi.
Tatashi cikin fushi tashiga toilet
Shikuma yafito waje ya tadda mayiesha a bakin kofa.
Mayiesha tace ai daka bita a hankali
Ai wannan yarinyar binta a hankali bazaiyi aikibah ke ai a hankali kika bita amma bai hana taki tashibah.
Suka zauna a parlor sukayi breakfast amma har suka qare nabila bata fitobah.
Mayiesha tace bari naje nakira nabila ta karya
Ki kyaleta idan taji yunwa ita da kanta zaka fito ta samu abunda taci.
Yanxu dai kitashi mu shirya muje koyan mota sbd kinga anjima kadan zan fita.
YOU ARE READING
MAYIESHA
Short Storylabarine akan wata mace jaruma wacce kwasam bazato ba tsammani ta tsinci kanta a cikin wata duniya. Shin ta hadu da qaddarar tane kokuma mutuwarta. Kubiyoni domin jin yadda ta kasance
