MAYIESHA PART 8

855 48 1
                                    

Cikin murya qasa qasa yafara kiran sunanta amma sam ta gaji ko jinsa batayi.

Sai yayi kokarin janyeta daga jikinshi sannan a hankali ya kwantar da ita.

Ya tashi zaune cikin rashin kwarin jiki  ya taba inda yake masa ciwo.

Yana tashi tsaye sai yaji jiri yana neman faduwa yayi sauri ya zauna.

Yana zaune kusan minti talatin sai yaji motsin mayiesha tana kokarin tashi daga bacci.
Tana bude idanuwanta taganshi a zaune sai tace dashi yayana yaushe ka tashi.

Yace bandade da tashibah

Tace to ya jikin naka yanxu dafatan dai da sauki.

Yace eh kawai dai dan ji nake gani.

Tace eh wahalar tafiya ce nima ita tasakani bacci.

Yace yanxu muna inane.

Tace muna duniyar mune munawwar.
Ya kalleta cikin tsabar jin dadi ta rungumeta yace nagode miki sosai mayiesha da taimakona da kikayi.

Tace muka dai taimaki juna zakace.

Yayi dariya yace kuma hakane yanxu ai kawai sai muyi sauri muwuce zuwa garinmu sbd nasan sbd tsabar saurin wannan raunat din taki zamu iya kaiwa cikin awa daya.

Tace eh hakane amma yakamata kadan huta tukunna.

Yace kada kidamu yanxu ai naji sauki kawai yanxu mu shirya sai mukama hanya.

Tace to shikenan amma dai yau kam bazaka fitabah sbd banason wani abun yasake samunka.

Yayi dariya sannan yace kenan a gabana zaki shirya tayi murmushi sannan tace ai yau tun a cikin ban daki zan shirya.

Yace to shikenan daga nan kiyi alwala sai muyi sallah gaba daya.

Tace to tatashi tsaye sannan ta kalli wani bangare na dakin ta shafa bahij dinta tare da rufe idanta bayan tayi niyyar abunda takeso.
Nan take saiga toilet ya bayyana a gabansu.
Tashiga ciki tayi wanka sannan ta changer kayan jikinta zuwa kyakkyawar doguwar riga sannan ta gyara gashinta sannan tayi alwala tafito.

Yana zau akan gado tana fitowa ta bita da kallo.
Ta kalleshi tayi murmushi sai tace yanxunnan zaka fara mun irin wannan kallon naka koh.
Yayi murmushi yace kawai dai naga kullum sai kyau kike qarawa.

Tace a hakan muna kwata kwata ba kwanciyar hankali a tattare damu.

Yace ai yanxu kam hankalinmu a kwancene tunda saura kadan mu isa gida.

Tace hakane kam yanxu dai kayi sauri ka shirya muyi sallah.

Yace to bari na tayaki tubke gashinki.

Tace ikon Allah yaukuma kaida kanka yace eh mnh.

Tace to shikenan ta zauna yayi tsafi saiga wani irin kyakkyawan ribon dan qarami a hannunshi ya dinga nade gashinta yana sakawa a ciki.
Yana qarewa yace nagama.

Tayi tsafi saiga madubi a hannunta ta kalli gashinta tace amma kam yayi kyau sosai waya koyamaka.

Yace nima ina tubke gashina wasu lokutan.

Tace amma dai kasan idan muka isa garinmu saika rage wannan gashin naka sbd yayi tsayi dayawa harfa yakusa nawa.

Yace to shikenan naji yanxu dai bari nayi sauri na shirya.

Cikin minti goma yafito sannan yace to kitashi muyi sallah.

Tana juyowa ta kalleshi sama har qasa tace ka ganka kuwa kamar wani balarabe.

Yace kedai kullum kinason zolayata to dai nagode.

Bayan sun gama sallah sukaci abunci sannan yace yanxu ina zamu fara tafiya garina kokuma naki.

Tace duk wanda yakamata yace yakamata dai muje naku sbd ni yanxu bazan iya gane gidanmubah sbd shekaru da yawa dole sai nayi bincike.

Tace kuma hakane.

Suma cikin hira sai suka jiyo hayaniya daga dan nesa daga inda suke.

Mayiesha ta waro ido tace mun shiga uku badai wani harin bane aka sake kawo mana.

Munawwar yace muje mugani tace a'a kawai mugudu.

Ya kalleta yace mugudu kuma sai kace wasu matsorata.

Tace nibanyi kama da matsoraciyabah kawai dai sbd mu tsirane kuma kaga kai baka gama warware wabah.

Yace to muyi sauri muje.

Suna fita sai suka hango wasu mutane akan doki sunata faman gudu wasu kuma a kasa suna biye dasu suna ihu.

Nan take na saman dokim suka wuce ta inda su munawwar suke tsaye.

Mayiesha tace inaga fah barayine sukayiwa wadannan talakawan sata.
Yace kuma zai iya yuwa.

Amma dai bari mu tambayesu.
Suka isa gun inda mutanen suke sai yace dasu lafiya kuke ihu kuma gudu.

Sai daya daga cikinsu yayi wani yare wanda munawwar bai ganebah amma daga dukkan alamu yana nufin sata wadanchan suka musu.

Yayi musu alamar dasu kwantar da hankalinsu zasu kwato musu dukiyarsu.

Cikin sauri munawwar da mayiesha sukayi sama suka dingabin barayinnan da gudu.

Har saida suka isa gun inda suke sannan suka fitar da tako binsu suka sha gabansu.

Sai babba daga cikinsu ya tsayar da dokinsa ya fidda takobinsa.

Yanufo ta inda su munawwar suke cikin wani yare yayi musu alamar su barsu su wuce kukuma su kashesu.

Nan take munawwar yace mayiesha kija baya kibarni da wannan dan qaramin kwaron zanji dashi.

Ai kuwa nan take munawwar yayo cikinsa da gudu ya fillewa dokinsa kai sannan suka fara fada.
Tashin farko munawwar ya cire masa hannun hagu.

Barawon ya kurma wani ihu sannan yayiwa sauran barayin alamar su tunkaro su munawwar.
Suda yawa suka nufato inda su munawwar suke amma kawai sai dai kaji kafa da hannu suna faduwa a qasa sauran suna ganin haka suka gefawa su munawwar dukiyar talakawan sannan suka gudu.

Sukuma su munawwar suka dauki dukiyar sannan suka fice daga gurin.

Suna isa gun inda wadannan talakawan suke suka mika musu dukiyarsu.
Cikin jin dadi dukansu suka risina sukayi musu godiya.
Sannan babban cikinsu ya bude buhunsa ya dauko wani dan qaramin dutsen zinari ya basu.

Mayiesha taki ta karba hakama munawwar.
Cikin mutanen suka nuna rashin jin dadinsu akan hakan sannan mayiesha ta karba.
Tace idan bamu karbaba zasuga kamar mun rainane.
Munawwar yace kuma hakane to yanxu dai muwuce kawai.

Sukayi sallama da mutanen sannan mayiesha takira raunat suka hau kanta sannan suka cigaba da tafiyarsu.

By maryam ashutrah

MAYIESHA Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang