Tana cikin tunanin ta yadda zata fara sarrafa wannan qarfe (bahij) sai taga wani kyakkyawan saurayi dan kimanin shekara ashirin da bakwai yana nufota ta gun inda take.
Tana ganinsa bata tsoratabah saboda ita ba abunda yataba bata tsoro a rayuwarta.
Bayan ya iso gun inda take sai ya kalleta cikin mamaki yace baiwar Allah meya kawoki nan.
Ta kalleshi cikin rashin yarda sbd tana ganin kamar cutar da ita zaiyi tace nima kawai na tsinci kaina ananne.
Ya zauna dan nesa da ita kadan yace kece mutum na biyu danagani anan wannan gurin nine na farko.
Ta kallesa tace to kai bawan Allah meya kawoka nan.
Ya kalleta da damuwa a tattare dashi yace
ni sunana Munawwar abdulhakeem nidan wani attajiri ne mai suna abdulhakeem mai dala muna zama a garin kaduna.
sannan kafin mahaifana susameni sunsha matukar wahala sbd saida suka shekara goma da aure sannan suka haifeni.
bayan sunsha neman magani kala kala daga qarshe sukaje wani qauye gun wata bokanya inda tabasu magani akan zasu samu da' amma da sharadin idan suka haifeni nakai shekara goma sha biyar zasu zasu bar matani.
Cikin damuwa da tashin hankali kuma sbd iyayena sunason su haihu takowace hanya domin su samu magaji sukace zasuyi yadda tace.
bayan wata daya mahaifiyata ta samu cikina bayan an haifeni sukaci gaba da raino na cikin kulawa da lelena suka shagwabani sosai.
Shekaru na tafiya har nakai shekara goma sha biyar.
A ranar da nacika shekara sha biyar ne sai bokanyar tazo gun iyayena akan alkawarinda sukayi mata.
Sukuma har sun manta da wannan alkawarin cikin rashin amincewa mahaifina yace bazai bata nibah haka ma ummata.
Cikin fushi bokanyar tace tunda suka qarya mara alkawari to itama bazata barsu da nibah sai ta rabasu dani haka tafadi wani abu na tsafi nan take aka namemi aka rasa.
Ina farfadowa na ganni anan cikin wannan gurin shekara ta goma sha biyu anan.
Anan na girma nikadai ba mutane nayita kokarin fita daga wannan gurin amma qarfin tsafina baikaibah sbd wannan gurin kewaye yake da qarfin tsafin aljannu.
Ta kalleshi cikin tausayi tace dama kanada tsafi ne yace eh amma da taimakon wannan dan qarfen da kike gani.
Yanuna mata cikin mamaki tace ai wannan irin qarfe nane ta nuna masa nata cikin mamaki yace tabbas nasan komai daren dadewa watarana Allah zai kawomun mafita kuma kece.
Ta kalleshi cikin mamaki tace nikuma
Yace ehh tabbas zan koya miki yadda ake amfani da tsafin wannan qarfen
Tace sunanshi "bahij"
Ya kalleta cikin mamaki yace bahij kumaEh nina saka masa wannan sunan
Yace kuma yayi dadi amma kafinnan inason kifadamun kekuma meya kawoki wannan gurin.Ta bashi labarin duk abunda yafaru nan take.
Sai yace kibani wannan bahij din naki na kalla sbd da naga kamar yafi nawa qarfin tsafi.
Ta kalleshi cikin rashin yarda tace bazan bakabah
Yace nasan bazaki yarda danibah nan take amma wlhy banida niyyar chutar dake kuma inason mutaimaki juna mufita daga wannan duniyar izuwa tamu duniyar.
Tace to shikenan inshallah zan baka duk wani maimako da kake bukata daga gareni ta mika masa bahij dinta.
Ya karba sannan ya kare masa kallo yace da ita wannan bahij din naki tabbas yana dauke da tsafi kala kala kuma masu qarfin gaske sbd kinga harda wannan tsuntsuwar da take ajinkinsa babushi anawan.
Tace hakane amma yanxu yaushe zamu fara gwajin.
Ya kalleta yace yanxu dai kibari har gobe tunda kinga yanxu dare yayi tace to a ina kake bacci
Ya kalleta sannan yayi murmushi yace aduk inda naso.Cikin mamaki tace ban ganebah
Yace to kitaso muje na gwada miki.
Suna cikin tafiya har suka isa gurinda yakeda fili sosai sannan ya kalleta yace kikalli yadda zanyi daki anan saboda kema kiyi nakin.
Tana kallonsa ya rufe idanshi ya bude sannan ya juya wannan dan qaramin qarfen hannunsa sai kawai sukaga daki a gabansu.
Cikin mamaki ta kallesa tace tabb kenan wannan abun har daki yakeyi.Yayi murmushi sannan yace komai yanayi yanxu dai ki gwada yin naki dakin.
Tace to ai bansan yadda zanyibah
Yace kawai kirufe idanki sannan kifadi abunda kikeso sai kijuwa bahij dinki.
Nan take ta rufe idan ta sannan ta bude sai ta juya bahij dinta nan take sukaga daki mai matukar kyau a gabansu.
Tace tabdi kaga har dakina yafi naka kyau
Yayi murmushi sannan yace ehh saboda bahij dinki yana da matukar qarfi shiyasa yanxu kishiga shiki ki kwanta saida safe.
Tace to saida safe tashiga cikin dakin.
Ta kalli ko ina dakine babba sosai ta ko ina haske yana tashi da kamshi mai matukar dadi sannan an kawatashi da abubuwa na kawa kala kala har wadanda idanuwa basu taba ganibah ga wani babban gado na alfarma a ciki.Tace lallai wannan dakin yana da matukar kyau na gaske.
Taje gun gadonta ta zauna sai ta kalli bahij dinta tare da rufe idanuwanta sai kawai tufafinta suka chanja izuwa na bacci masu matukar kyau.tace yanxu taya zanyi sallah kenan kuma gashi ba agogo ballantana nasan lokaci sannan kuma gashi ba ban daki anan.
Nan take ta tashi ta nufi kofar dakinta tana bude kofa sai taga ko ina yana haske ga farin wata sai kyalli kake gani ta ko ina sai wani kukan tsuntsaye mai dadin sauti.
Ta juya ta kalli dakin munawwar sai tanufi dakin tashiga da sallama yana zaune akan sallaya yagama sallah yana lazumi.
Taje ta samu guri ta zauna yana gamawa sai ya juyo ya kalleta nan take zuciyarshi ta buga da qarfi a cikin ransa yace bantaba ganin mace kyakkyawa mai halitta basu kyau bah irin wannan yarinyar bah.dukda ban taso cikin duniyar mutane bah amma nasan wannan ko a cikin duniyar mutane ita ta dabance.
Yana cikin tallonta ta gane ita yake kallo nan take ta rufe idonta sai kawai ka ganta da mayafi tarufe dukkan jikinta.
Yayi murmushi ganin hakan sannan yace yana ganki a dakina keda yakamata ace kina bacci.
Tace eh hakane amma inason nayi sallah ne kuma bansan inane gabas bah sannan kuma bansan yadda zan dinga gane lokutan sallah bah.Yayi murmushi yatashi yazo kusa da ita yace to muje na nuna miki.
Suka tashi har sunkai bakin kofa zasu fita saiga wata yer qaramar tsuntsuwa kyakkyawa tazo gunsa yana ganinta yayi murmushi yace wannan itace runat tsuntsuwa tace tana ciremun kewa sosai kuma na aminta da ita.
Myiesha ta kalli runat tayi murmushi sannan tace sunana myiesha da fatan zamu zama qawaye sai tsuntsuwar tayi wani dan sauti mai dadi.
Munawwar yace tana kuwa sonki yace da tsuntsuwar runat kijirani a dakina yanxu zanje nadawo kinji.
Runat ta fira zuwa dakinshi sukuma suka wuce zuwa dakin myiesha.
By maryam ashutrah

CITEȘTI
MAYIESHA
Proză scurtălabarine akan wata mace jaruma wacce kwasam bazato ba tsammani ta tsinci kanta a cikin wata duniya. Shin ta hadu da qaddarar tane kokuma mutuwarta. Kubiyoni domin jin yadda ta kasance