Bismillahirrah manirraheem🎆
Gadiya ta tabbata ga ubangijin halittu wanda yayi mutane dakuma aljan💐💐
Ya Allah kabarmu dason annabinka muhammadu rasullilah s.a.w🌼🌼🌼
Ya Allah kabani ikon da kwarin gwiwa na rubuta wannan littafin nawa🎆🎆🎆🎆🎆🎆🎆🎆
Godiya ta nusamman ga ma'abota karatun littafai na Allah ya bar qauna.😘😘😘
Tana zaune a tsakar gida tana girki sai ummanta tafito rike da uniform din makaranta a hannunta.
Tace mayiesha karbi kayannan kije kisaka kiwuce islamiyya kafin kimakara.
Mayiesha tace umma nifa kawai kubarni Allah bason makarantar nan nakeyibah
Umma tace to ai yazama dole kuwa kije makaranta tunda bazaiyyu ace bakya son boko bah sannan kuma bakyason islamiyyar.
Ta karbi kayan tace to umma bari naje na shirya saina wuce.
Umma tace yawwa 'yata kuma dan Allah idan aka tadaku kawai kinufo gida kada kitsaya ko ina
Tace to umma.
Bayan tagama shiryawa ta dauki sababbin littafanta da abbanta ya siyo mata tafito parlour tace to umma natafi saina dawo.Yawwa yer albarka Allah ya taimaka
Tace ameen tafice warta.Mayiesha kenan yarinya yer shekara goma sha takwas da haihuwa.
kyakkyawa ce fara mai gashi har gadon baya komai nata dai dai ma'ana full option.tana zaune tare da iyayenta a wani dan qaramin gida sbd talakawane amma dai ahakan Allah yana hore musu nasakawa a baki.Abbanta yanason tayi karatu amma ita kwata kwata ta tsani hakan shine kawai yake hadasu fada.
Bayan haka tana da aljannu kusan ashirin a kanta shiyasa yaran unguwa basayi mata rainin hankali sbd idan suka tashi zata iya karairaya mutum komai girmansa.shiyasa ko saurayi daya baitaba zuwa neman aurentabah kuma batada saurayi kodaya amma hakan bai dame tabah.
Wannan kenanCigaban labari🎆
Tana kan hanya zuwa islamiyya sai ta hadu da qawarta zalihat tace da ita au dama kema makarantar mu aka sakaki.Tace eh hakane
Kenan zamu dinga zuwa makaranta tare
Tace ba lallaibah sbd nifa bason zuwama nakeyibah
Tace habadai qawas karatu fah yana da muhimmanci.
Myiesha ta harareta zulaihat na ganin hakan takama bakinta tayi shiru sbd tasan idan ta takurama saidai akaita gida summamiya.Suna isa makaranta zulaihat tawuce da ita office din mai makatanta bayan angama mata komai aka sakata ajin su zulaihat.
Suna shiga aji malaminsu yashigo aka fara karatu.
Bayan angama ne yafara tada su sukaranta amma acikin ajin ba wanda ya iya karatunsa anan take kuwa yayi fushi yace dasu dukansu sufito waje suyi kneel down.
Bayan kusan minti goma sannan ya dauko bulala yafara dukansu kowa aka mishi bulala biyar.
Yana kaiwa gun myiesha yace ta bada hannunta tace itafah sabuwar zuwace meyasa kawai sbd bata iya karatubah za'a daketa.
Aikuwa taki ta bata hannunta sai yaje dukanta ta gudu.
Sannan yaje yakai qararta gun malam abbas wato babban malamin makarantar.
Sukazo tare malam abbas yace kibada hannunki a dakeki kamar yadda akayiwa sauran kokuma yanxu nida kaina na dakeki.
Cikin fushi ta bada hannunta malaminsu yamata bulala biyar amma ko ajikinta.Tana juyawa zataje aji sai tace shekarata biyu ba'a dakenibah sai yau wani qaton banza yadakeni aikuwa malam abbas najin haka ya kwala mata kira.
Ta juyo a fusace yace zonan
Tana zuwa kafin ta ankara ya watsa mata dorina a fuska aikuwa nan take aljannunta suka tashi malamin yazo zai qara kai mata wani dukan kawai tayi tsuntsu tayi sama
Dayake shima malamin ba'a barshi abayabah indai ta fannin aljannune shima nan take yayi wata adduah yayi sama
Aikuwa nan kowa na makarantar yafito domin kallon ikon Allah.Tana ganin ya nufita ta qara yin sama zuwa dayan bangaren makarantar cikin fushi da fusata tace idan ka karasonan kwananka ya qare.
Yana jin hakan shima ya nufeta cikin sauri.
Tana ganin hakan tayi sama sai qara sama takeyi kamar wata tsuntsuwa aikuwa kafin ka ankara ta bace basss har aka dena hangota.Malam abbas na ganin hakan ya sauko qasa sannan yake cewa lallai ina mamakin irin qarfin wadannan aljannun yarinyarnan amma kada kudamu zata dawo kowa yaficewarsa.
Cikin surutu irin na mutane kowa ya watse.Nana take akaje aka sanar da ummanta bayan taji wannan labarin hankalinta yatashi sosai sbd acewarta hakan bai taba faruwa da yer tata tilo bah amma suna tsammanin idan tarage fushi zata dawo gida.
Tanata tafiya cikin gajimare sai hankalinta yadawo jikinta cikin tsoro da firgici ta kwala ihu tana dubawa taga tanata wuce garuruwa kala kala masu matukar kyau sai a hankali taga tana saukowa qasa.
Ta sauka cikin wani gari mai matukar kyau da furanni kala kala ko ina wani irin sanyi mai dadi yana tashi amma bakowa a garin sannan ba gidaje daga koramu masu ruwa sai ciyawu kala kala da tsuntsaye sai abubuwan marmari kala kala.
Bayan ta gama kallon ko ina sai tace yau nashiga uku nikuma meya kawoni nan ina umma ta wannan wani gurine haka kawai ta duka ta fasa kuka.
Tana tashi tsaye sai taga wani abu a hannunta kamar qarfe dan qarami a hannunta anyi mishi ado mai kyau na kaloli masu kyau anyi mishi zanen wata tsuntsuwa.
Ta kalle wannan abun cikin mamaki tace wannan kuma wane abune haka mai kyan kallah tana juyashi sai taga tajuya da karfi.
Cikin tsoro tace wannan wani irin qarfe ne haka ta dagashi sama kawai sai taga tayi sama cikin sauri tana saukar dashi qara sai taga tayi qasa da sauri.Tace tabb lallai wannan karfen na tsafine watakil zai taimakamun nakoma duniyata.
Tace amma yakamata na koyi yadda ake amfani dashi kafin nayi kokarin sarrafashi.
Tana fadin haka sai tafara jin yunwa taje ta samu wani bushiya mai kayan marmari kala kala tafara ci har saida ta koshi.
Sannan ta zauna ta kalli wannan dan qaramin qarfen dake hannunta tace yakamata nayiwa wannan qarfen suna tayi tunani nadan wani lokaci sannan tace sunanshi "BAHIJ"
Tana fadar haka sai qarfen yayi dan wani haske tace laaa kenan wannan yana nufin yaji dadin sunanda nasaka mishi yanxu taya zan san yadda ake amfani dashi.
By maryam ashutrah
![](https://img.wattpad.com/cover/175608420-288-k615443.jpg)
YOU ARE READING
MAYIESHA
Short Storylabarine akan wata mace jaruma wacce kwasam bazato ba tsammani ta tsinci kanta a cikin wata duniya. Shin ta hadu da qaddarar tane kokuma mutuwarta. Kubiyoni domin jin yadda ta kasance