MAYIESHA PART 13

727 46 0
                                        

Hajiya salamatu na zaune tare da hajiya zinaru a balcony din gidan saiga kira yashigo wayan hajiya zinaru.

Tana dagawa sai tace hello umar kasamo adireshin gidanne.
Yace eh hajiya tace to katuromun ina jira.
Yace to hajiya yanxunan zan turo miki
Tace to nagode.

Ta kalli hajiya salamatu tace ansamu adireshin gidan mubari har zuwa maraice haka sannan mutafi.

Tace to Allah ya kaimh kuma Allah yasa shine dana munawwar.
Tace ameen.

Ana tashi daga makaranta sai hafsat tacewa mayiesha anjima da qarfe hudu akwai walima a gidansu ta saukar qanena ina fatandai zakixo.

Tace eh zanxo inshallah kibani number dinki idan na isa saina kiraki.
Tace aww kinyi wayane.
Tace ehh yanxu inada waya.
Tabata number din sannan tashiga adedeta tafice zuwa gida.

Tana zuwa gida take sanarwa umma tacewa zataje walima gidansu hafsat.
Umma tace to shikenan kinga bari nabaki cikon kudin tasi'u tela kikai masa saiki anso dinkinki dake gunsa.

Tace to umma.

Tana karbar kudin taje ta karbo dinkinta sai ta biya ta gidansu fatima ta kaimata hijabinta.

Tana kan hanya zata wuce gida saiga wani mai mashin yasha gabanta.

Yace yen mata sannu fah

Ta watsa masa harara tace yawwa

Yace amma ke kyakkyawace.

Tace ai nasani basaika fadabah.

Yace kinga baikamata nayi magana dakebah anan ba mutuncinki bane kiyimun kwatancen gidanku sai nazo.

Tace lafiya dai kakeson sanin gidanmu

Yace akwai maganarda nakeson muyine.

Tace malam kafadi koma menene anan kana batamun lokaci.

Ya sauko daga mashin dinsa sannan yace ina ganinki ne kawai sai naji mashin soyayyarki ya harbi zuciyata.m a'ana naji inasonki.

Ta kalleshi sama da qasa tace to nagode amma ina da wanda zan aura sbd ansaka rana.

Yace to ai wannan ba matsala bane.
Tace mekake nufi idan ba iskanci kakeso danibah yaza'ayi nace maka inada wanda zan aura sannan kacemun wannan ba matsala bane.
Kaga kawai kaja akwalan mashin dinka kafice daga nan.

Yace haba yen mata wlhy inasonki na hakika

Tace idan kakara cewa kana sona saina hada maka jini da majina .

Tace a'a basai anyi hakabah Allah ya huci zuciyarki sai anjima.

Ta fice warta shikuma yaja mashin dinsa yayi gaba.

Tana zuwa gida ta fara shiri tayi matukar kyau sosai tasala lace dinta blue riga da skirt kayan sun kwanta a jikinta sosai.

Tana gama shiryawa tafito tacewa umma to nikam natafi.

Tace Allah ya tsare munke ya'ta dan Allah banda fada.

Tace ai umma nadena saina dawo.

Tace to a sauka lafiya.

Tana fitowa saita kira munawwar yana dauka tace yayana zanje walima gidan qawata

Yace kada kidade sbd banason nadawo gida bakinan.

Tace to shikenan bazan dadebah yakashe wayar.

Qarfe biyar da rabi ta dawo gida.umma tace yanxu kitashi kije ki azamun sanwa sbd yau banajin dadin jikina sosai.
Tace to umma.

Tatashi tafice zuwa kitchen.

Umma na zaune tsakar tana hutawa sai taji ana sallama tans juyowa taga ai qawar tace abida.
Ta amsa sallamar tare dayi mata maraba.
Tana zaunawa sai tace dama naje gidan hadiza ne nayi mata barka shine nace bari nazo nan na ganki tunda mun kwan biyu bamu hadubah.

Umma tace hakane gsky Nagode sosai Allah yabar zumunci bari nakira mayiesha ta kawo miki ruwa.

Ta kwalawa mayiesha kira tana fitowa ta gaida qawar ummanta sai umma tace ki kawo mata ruwa mai sanyi nasan ta kwaso rana.

Tace to umma.

Tana wucewa sai abida tace lallai safara'u (sunan umma na ainihi)yanxu ashe mayiesha tayi irin wannan girman amma har yanxu kin zauna kina kallonta.
Kuma yakamata ace tana gidan miji ai.

Umma tace ai aure lokacine kuma idan yazo zatayi banason na dagawa ya'ta hankali nafison a duk lokacinda ta samu wanda takeso sannan muyi mata aure cikin kwanciyar hankali.

Tace to kuma hakane Allah ya kawo nagari.

Umma tace ameen.
Suka danyi hira nawani dan lokaci sannan ta fice.

Qarfe shida saiga su abba sun dawo daga kasuwa.
Dukansu suna zaune suna hira sai akayi sallama.

Suna dubawa sai sukaga wasu mata su biyu daga ganinsu kaga yen hutu.

Suka shigo da sallama.
Dukansu suka amsa sai umma ta dauko musu tabarma ta shimfida musu.

Suka zauna suka gaisa dukansu.
Sai umma tace kuyi hakuri amma ban shaidakubah.

Hajiya salamatu tace eh hakane baku sanmubah amma muna tafe da wata maganace mai muhimmanci

Umma tace muna saurarenku.
Tace wannan yaron munawwar dan Allah dankine ina nufin kekika haifeshi.

Umma ta kalli abba shima ya kalleta.
Sai abba yace meyasa kuke son sani.
Sai hajiya salamatu tace domin shekaru da yawa da suka shude akwai dana mai suna munawwar wanda yabace kuma har yanxu bamusan inda yakebah.

Abba yace tabbas munawwar ba danmu bane kuma shima ya dade rabonsa da mahaifansa.
Nan ya kwashe dukkan labarin yafada mata.

Cikin kuka mai ban tausayi hajiya salamatu tace wlhy danane munawwar.

Munawwar ya kalleta yace wace hujja kikeda akan hakan.

Itama ta kwashe labarin komai ta fada musu.

Munawwar yace tabbas sunan mahaifina alhaji abdulhakeem kuma sunan mahaifiyata hajiya salamatu.

Nan abba yace Allah mai iko ashe da rabon zaku sake haduwa.

Munawwar cikin kewar mahaifiyarsa yaje ya rungumeta suna ta kuka dukansu.
Bayan wani dan lokaci sai munawwar ya kalleta sannan yace ummata meyasa bangane kibah tace sbd watakila tun kana qarami rabonka dani sbd bana yawan zama a gida sbd ina zuwa qasashen waje kasuwanci kuma kafi sabawa da mahaifinka.

Yace to yanxu ina mahaifina meyasa bakuzo tare bah.
Nan take wasu sababbin hawaye suka fara zubo mata tace ai mahaifinka yayi shekara biyar da rasuwa sbd fama da yayi da ciwon zuciya sbd rashinka.

Munawwar yasake fashewa da kuka yace Allah yaji qanshi da rahama.
Dukansu sukace ameen.

Hajiya salamatu ta kalli umma da abba tace bansan wace irin godiya zanyi muku tare da yer ku bah sbd kunrike munawwar da amana.
Sannan kunyi mishi halacci sannan kuma kuka maidashi mutum ta hanyar kula da addininsa da kuma koya masa kasuwanci domin yarike kansa.

Abba yace ai bakomai hajiya muma sbd muna neman sakamakone daga ubangiji dakuma samun lada shiyasa.

Mayiesha tace kenan yaya munawwar qarshen zamanmu yazo tunda yanxu tafiya zakayi tare da ummanka.

Munawwar yace ai koda kuwa naje tare da ita muna tare sbd yanxu mun zama yen uwa sbd inada wasu iyayen anan.

Mayiesha ta tashi cikin kuka ta wuce daki.

Munawwar na ganin haka yabi bayanta.

Abba ya kalli hajiya salamatu yace ai wlhy sun saba sosai fiye da yadda kike tsammani bacci kawai yace rabasu.

Hajiya zinaru tace tabbas kuwa sbd munga alaman hakan yadda hankalinsa yatashi daya ganta tana kuka.

Amma inada shawara.

Hajiya salamatu tace kifada.

Tace mazai hana a hadasu aure tare.

By maryam ashutrah

MAYIESHA Where stories live. Discover now