Sai malam yaci gaba da cewa kasan a addinance tsafi haramunne kuma kaga bazaiyu kuci gaba da amfani dashibah kenan.
Munawwar yace to malam idan dai hakane na yarda a salwantar dashi
Mayiesha itama tace ta amince.
Sai dukansu suka cireshi daga hannuwansu suka mikawa malam.
A gaban su ya ajiyesu a qasa sannan ya dauko wasu ruwa daga aljihunsa yayi musu adduah sai ya zuba nan take sai suka chanja kala zuwa baki sai hayaki suke fiddawa.Bayan dan wani lokaci kawai sai suka bace.
Malam ya kallesu sai yace yanxu inshallah Allahu aljannun sunbar jikinku har abada.
Abba yayiwa malam godiya sosai
Sai munawwar ya kalli abba yace abba dan Allah ina rokon wata alfarma kafin nakoma garina.
Abba ya kalleshi yace to munawwar fada naji Allah yasa zan iya.Yace inason ka rokarmun malam dana dinga zuwa gunshi yana qaramun ilimi akan addini.
Malam abbas yayi murmushi yace naji dadin wannan maganar taka munawwar kuma inshallah zandinga kara maka karatu har kayi nisa sosai sannan kuma a kyauta ba zaka biyani komaibah.
Munawwar yayi godiya sosai.
Sai umma tace kema mayiesha komawa islamiyya zakiyi
Mayiesha tayi murmushi tace to umma inshallah zan dinga zuwa.
Sukayi sallama da malam ya tafi.
Bayan kwana biyu suka fara zuwa makarantar a tare suke zuwa kullum idan mayiesha ta wuce aji shikuma yaje office din malam abbas domin karatu.
Sannan kuma yana ganewa sosai shiyasa karatun nasa yake yin sauri sosai haka ma mayiesha tana da dagewa yanxu gurin karatu sbd har malaman suna mamakin hazaka irin ta mayiesha.
Washe gari yana kwance yana baccinsa cikin kwanciyar hankali saiga mayiesha tashigo da sallama tace yayana har yanxu baka tashibah.
Taji shuru ba magana sai taje ta dauko tsintsiya kwaya daya taje dai dai kunnensa tana sakawa.
Aikuwa yanajin an tokareshi ya bude ido yana ganin mayiesha ce tace tashi muje mu karya tun dazu kai ake jira.Yace aww dama kece kike tokarata a kunne ta tashi da sauri ta nufi kofa shikuma yabita da gudu.
Tana isowa parlour ta buya bayan umma tace umma kinga yaya Munawwar.
Yana fitowa yace umma kiyiwa yarinyar nan magana tadena damuna waifa ina bacci tazo ta sakamun tsintsiya a kunne.Umma tace mayiesha bakida gsky meyasa zakiyi haka.
Tace umma idan bahaka nayi mishibah bazai tashibah.
Sai ga abba yashigo parlor yace waton tunda safe kunfara fadan kenan.
Sukayi murmushi sukace abba ina kwana.
Abba yace lafiya qalau yarana dafan kun tashi lafiya
Munawwar yace nikam a'a tunda mayiesha a firgice ta tadani.
Abba yace mayiesha kidena neman tsokana fah yanxu dai kuzauna muyi karin kumallo.
Mayiesha tace umma nidai yau idan akwai dimamen tuwo shi zanci bazansha kokobah.
Umma tace to kiduba a kitchen akwai saura.
Munawwar yace nima umma dimame zanci.
Umma tace to ai bazai isheku kubiyu bah
Yace nine babba kawai tabarmun
Mayiesha tace tabb bazaiyubah bari kagani tayi kitchen da sauri aikuwa yabi bayanta.
YOU ARE READING
MAYIESHA
Short Storylabarine akan wata mace jaruma wacce kwasam bazato ba tsammani ta tsinci kanta a cikin wata duniya. Shin ta hadu da qaddarar tane kokuma mutuwarta. Kubiyoni domin jin yadda ta kasance