Umma na zaune a bakin murhu tana girki tayi tagumi tana tunani sai taji ana kwankwasa kauren gidan.
Tayi sauri tasaka hijabinta sannan taje ta bude kofar sai taga abban mayiesha ne da malam abbas.
Tayi musu maraba sannan ta dauko tabarma ta shimfida musu.Bayan sun zauna sannan take gaida malamin.
Cikin sakin fuska ya amsa sannan yafara da nayi bincike na akan batar mayiesha kuma nagano tana wata duniya wadda bakowa a cikinsa sai wani dan saurayi wanda yadade a cikin ta tun yana qarami.
Amma wannan ba abun tada hankali bane sbd suna iya kokarinsu domin su kubutar da kansu daganan sbd haka suna bukatar adduah sosai sosai.
Umma tace amma kasan mace da namiji su kasance a guri daya sukadai babban hatsari ne
.
Malam abbas yace kada kidamu da izinin Allah ba abunda zai faru.Abba yace to shikenan malam zamuyi iya kokarinmu gurin yin adduah kuma dan Allah kutayamu
Malan abbas yace inshallah zamu yi hakan to nagode zan tafi yanxu.
Umma tace nakusa qarasa abunci bazaka bari ya idar bah
Yace a'a a koshe nake wlhy na gode da karramawa.sukayi sallama yawuce warsa.
Washe gari da safe ta tashi tana waige waige sai kawai ji tayi ance ya jikin naki da fatan da sauki.
Tace kawai dai inajin kasala ne
Yace kada kidamu idan kikayi wanka kakici abunci zaki murmure.Tace nagode sosai dan uwa yadda kake kula dani
Yace ai dole nakula dake sbd kekadai ce zaki iya fudda ni daga nan.
Tace awww sbd wannan kenan kake kula dani koh bawai sbd ka damu danibah
Yayi murmushi wanda ya fidda asalin kyansa yace ba haka bane
Yanxu kitashi kishirya mujeTace ina zumuje
Yace training mnh
Tace laaa dama kanajin turanci
Yace eh inaji sbd lokacinda nake gida ina zuwa makaranta amma kadan kadan nakeji yanxu sbd nadade banyibah
Tace nima haka sannu sannu nakeji sbd ni kam ko a gida ma banason zuwa makaranta
kuma gaji makarantar gwamnati nakeyi sbd ni yer talakawace.Yayi murmushi sannan ya mika mata hannunsa yace kawo hannunki na tayaki tashi.
Tana mika masa hannunta ya janyo ta tashi sannan yace to kije dakinki ki shirya nima zan shirya tace to shikenan.
Tana fitowa saita rufe idanta sannan ta bude amma bataga dakintabah.
Tayi mamaki sosai sannan ta taba bahij dinta ta rufe idanta amma duk da hakan ba daki ba alamarsa.
Tace nashiga uku kada dai ace bahij dina yadena aiki.
Tace bari dai naje nafadawa munawwar tana shiga dakinsa sai ta ganshi cikin shigar yen india yafito sak kamar salman khan ta saki baki tana ta kallonshi har saida ya lura da akwai mutum a cikin dakin.
yana juyowa sai yanufo dinda take yace lafiya baki shiryabah sannan ta dawo hankalinta.
Ta kalleshi tace kayi kyau sosai
Yayi murmushi yace to nagode meya hanaki shiryawa
Tace bahij dina yaki yayi aiki nayita kwadawa.
Yace to inaga sbd bakiji sauki bane shiyasa amma duk da hakan bai kamata ace baya aiki bah.
Amma mugani ta bashi bahij dinta ya kalleshi da kyau sannan yahada bahij dinta da inwak dinshi sai kawai ya saki wani haske.
Yace kinga yana haske yanxu.Ya shafa bahij dinta a fuskarta tare dayin bismillah sai kawai haskenshi ya qaru.
Yace gashi yanxu inshallah zaiyi aiki.
Ta karba sannan tafita ta sake kwadawa sannan yayi aiki
Ta kalleshi tare da murmushi tace nagode bari nayi sauri nashirya yace to ina jiranki.
Tana shiga dakinta tayi sauri ta shirya tayi kyau sosai sannan tafito.
Tana fitowa daga daki ta tunkaroshi ya kalleta yace amma kinyi kyau sosai.
tayi murmushi tace ai kafini kyau.
kananan kaida runat kenan
yace eh ta kalli runat tace sannunki runat.
sai runat tayi dan wani kuka kadan alamun taji abunda mayiesha tace
sai mayiesha tayi murmushi tace yanxu dai muci abunci sai muje training.Suna gamawa suka wuce inda suke koyan takobi.
Yaukam sosai ya koya mata tunda har gwabzawa sukayi a tsakaninsu.
(Bayan sati daya.)
Munawwar yakoya wa mayiesha fada ta iya sosai dan har tanason tafishi iyawa sbd wani lokacin idan tagama sallar asubah bata komawa bacci takan dingayin training itakadai.
Suna zaune suna cikin hira sai munawwar ya kalleta yace gobe inshallah nakeson mubar wannan wajen
Ta kalleshi tace amma fa nikam ina tsoro.
Yace kada kidamu kawai kidinga adduah shine kawai.
Tace amma zanyi kewar ka sosai idan muka rabu sbd yanxu fah kusan watan mu daya tare na shaku dakai sosai.Yace ai bamu rabubah sbd zamu dinga kaiwa juna ziyara.
Tace kuma hakane.Washe gari da sassafe munawwar yaje gun mayiesha sukayi plan akan yadda zasuyi tafiyar su sannan kuma ya daura mata sarka a wuyanta dakuma wasu yen hannu na gwal masu matukar kyau sai haske sukeyi.
Tace amma ina kasamu wadannan abubuwan.
yace runat ce takawomun nima bansan daga ina tasamubah shiyasa nace bari na baki a matsayin kyauta.
Ta rike hannunshi tace na gode sosai dan uwa Allah yabar zumunci.
Yace ameen ba damuwa yanxu kitashi mutafi tace to shikenan amma yazakayi da runat
yace munyi ban kwana da ita sbd bazaiyi ta biyo mubah sbd ba lallai ta iya rayuwa a duniyarmubah.
Tace hakane amma nima inason nayi maka kyau ta kafin mutafi.
Yayi murmushi yace to tame kenantace tsaya ka gani ta rufe idanta nadan wani lokaci sannan ta bude saiga wani abu kamar camera tace inason muyi hoto anan kafin muwuce sbd kadinga tunawa dani idan ka gani.
Yayi murmushi sannan yace to mudauka sukayi hoton sannan ta bashi tace gashi a matsayin kyauta daga gareni.
Ya karba tare dayin murmushi yasaka a cikin kayansa sannan suka fita zuwa wani babban fili.
Ya kalli ko ina sannan kawai ya tsinci kansa yana hawaye.
Ta kalleshi tace lafiya meya sakaka kuka.
Yace kawai zanyi kewar wannan gurinne sbd anan nagirma tare da tsuntsaye nasaba da wannan gurin koda ace inason nakoma duniyarmu amma still wannan ma duniyatace.Tace kayi hakuri ta lallasheshi sannan yace to mutafi.
By maryam ashutrah

VOUS LISEZ
MAYIESHA
Nouvelleslabarine akan wata mace jaruma wacce kwasam bazato ba tsammani ta tsinci kanta a cikin wata duniya. Shin ta hadu da qaddarar tane kokuma mutuwarta. Kubiyoni domin jin yadda ta kasance