Tana juyowa sai taga audu kafinta ne wanda duk unguwarsu ba wanda yakaishi iya kafinta.
Tace ina wuni
Yace lafiya qalau dama dazu nine na aika akiraki kuma sai yaron yake cewa wai yayanki yahana kifito.
Kuma a sanina kekadai mahaifanki suka haifa bakida yaya.Tace inadashi mnh amma nidai abar wanchan magana dafatan dai lafiya.
Ya dan shafi keyarsa sai yace ehh to dama ina tafe da wani sakone kuma dafatan zaki amince dashi.
Tace fadi ina sauranka.
Yace wato nadade inasonki mayiesha kawai narasa yadda zan tunkarekine da maganar.
Ta kalleshi tace so kuma
Haba audu kafinta nizaka kalla kace kana sona bayan a unguwar nan ba wanda baisan halinka na biye biyen mata bah.
Yace ai wannan halinane na da amma yanxu nadena.
Tace kaga malam audu kokuma nace audu kafinta kabar kofar gidannan tun kafin na sare maka kanka da wannan takobin,dan iska kawai kawani sako turarenka mai warin tusa kazonan wai kana sona.
Yana jin haka yace Allah ya huci zuciyarki nabarki lafiya.
Ya ficewarsa.Itakuma tashiga gida takira yayan nata yana fitowa tsakiyar gida sai ya ganta da takubba guda biyu a hannunta yace to bani daya.
Tana mika mishi tace yau zan koya maka hankali yayi murmushi yace to shikenan ai saimu kwada.
Taje daki ta saka riga da wando sannan tafito.
Yana yi mata kallo daya ya kauda fuskarsa.
Nan sai suka fara fadan aikuwa saijin qarar takobi kakeyi.
Umma na bacci a daki taji hayaniya yayi yawa tace to Wannan hayaniyar kuma ta mecece baridai naje na gani.
Tana fitowa tsakar gida sai tagansu sai faman kaiwa juna hari sukeyi.
Tasaka salati tace yau nashiga uku yaki kuma a gidan nawa.
Suna jin hakan suka tsaya sai mayiesha tace umma kawai muna gwaji ne.
Tace kinci uwaki da gwaji yanxu idan dayanku yaji ciwo aini za'abari da jinya.
Munawwar yace umma ki kwantar da hankalinki dukanmu mun kware fah ba wanda zaiji ciwo.
Tace munawwar kamamun bakinka wlhy dukansu kufita idona kada na saba muku.
Yanzunnan ki mayar da wadannan takubban inda kuka samosu kafin raina ya baci.
Suka kalleta a tare umma tace daku nake magana fah.
Sai mayiesha ta turo baki ta karbi ta munawwar ta saka hijabinta zuwa mayarwa.
Da daddare suna zaune a tsakiyar gida suna shan iska sai abba yace yawwa munawwar dama na yanke hukuncin tunda kaga zaune kake a gida yakamata mufara zuwa kasuwa tare.
Munawwar yace to nikam abba ai ban iya kasuwanci ba.
Abba ya kalleshi yace ai yauda gobe idan kana ganin yadda akeyi zaka koya.kuma sana'ata bawata babba bace ina siyar da yen kunne ne da sarkoki da kuma turaruka.amma fa ba zinare bah.
Munawwar yace to abba inshallah zan zama mai dagewa naga na koya Allah yabamu sa'a
Dukansu sukace ameen.
Abba yace kuma yanxu katashi muje gun mai aski ya rage maka wannan gashin naka kamar na mace.
Munawwar yace to abba
Mayiesha tace kenan abba nikadai za'a dinga bari a gida.
Umma tace tunda ni ba mutum bace ba koh.
Mayiesha tace ni umma ba haka nake nufibah.Abba yace ai makarantar boko zaki koma tunda dama aji nakusa da qarshe kike a secondary yafimiki.
Tace to shikenan abbana.
Yace yanxu gobe ki shirya idan zamu wuce kasuwa sai muwuce dake na biya miki kudin makaranta kawai kici gaba da zuwa kuma wlhy idan naji bakya kokari ranki sai yayi matukar baci.
Tace inshallah abba zandinga kokari.
Washe gari da sassafe dukansu suka tashi sai shirye shirye sukeyi.bayan sun gama suka karya kumallo sannan suka nufi makarantar su mayiesha.
Bayan abba yabiya kudin makaranta ta wuce aji.
Sukuma suka wuce kasuwa.
Tana shiga aji sai taga hafsat chan qarshen benci tana zaune.
Taje gunda tace hafsat take cikin mamaki hafsat tace mayiesha yau kuma kece a makaranta.Tace wlhy kedai nice ina sauran qawayenmu bangansu bah.
Hafsat tace suna sashen yen ss3
Tace tokekam yana ganki anan tace nima repeating abba na yasaka akamun wai tunda banida kokari sosai bazai bari naje aji na gababa.
Tace kinga kenan dagani harke yakamata mudage dantse domin muyi karatu sosai tace hakane kam gsky.Allah yabamu sa'a mayiesha tace ameen.
Bayan an tada su daga makaranta mayiesha ta tari mai adedeta yakaita gida.
Suna isa ta dauki naira dari ta mika masa tace kabani chanji.
Ya kalleta yace wani chanji zan baki ai naira dari nakawoki.
Tace kamm buu ai wlhy naira hamsin ne ake kawoni daga makarantarmu zuwa gida.
Yace to nidai a dari na kawoki har ya tada adedeta dinsa zai wuce sai ta cire hijabi taci damara.
Ta chakumo kwalar rigarsa tace wlhy kodai kabani hamsin dina kokuma nayi maka uban duka.
Yanajin haka yafito daga adedeta dinshi yace kece zakiyi fada dani to gani ki dakeni muga.
Ai kuwa yana fadan haka kafin ya rufe baki ta kai masa uban naushi a fuska nan take hancinsa yafara jini.
Yace jar ubannan nikika fasawa hanci ai wlhy yau sai dai akwasheki sumammiya anan.
Nan take yara suka taru suna kallonsu.Har ya daga hannu zai mareta sai tayi saurin rike hannunsa ta juyashi da qarfi sai kawai jin kayi qashin hannunsa yace qasss.
Yabuga ihu tace ai wlhy gobe bazaka qara cewa zaka dake wata macen bah ballan tanani.
Tasake kai mishi bugun naushi a ciki tace kabani hamsin dita kokuma yanxunan na karairayaka.
Ai kuwa cikin sauri ya mika mata hamsin yaja adedeta dinsa cikin mamakin qarfi irin na mayiesha ya fice.Ta juyo ta kalli yaranda ke gurin ai kuwa kowa yakama gabansa.
Sannan tashiga gida.
Tana shiga tafice zuwa kitchen ta dibo abunci ta tarar da umma a parlor tace umma ina wuni
Umma tace lafiya qalau yana ganki kinci damara haka.
Tace umma wani dan adedeta ne fa yaso ya renamun wayo shine nakoya masa hankali.
Umma tace wato baki dena wannan halin nakibah na dukan mutane to idan abbanki yadawo saina fada mishi zakiji ajikinki yau.
Nan take tace umma dan Allah kiyi hakuri bazan sakebah.
Tace to da kin kyautawa kanki sbd ba namijinda yakeso ya auri mace masifaffiya.
Tace nifa umma kinsan niba masifaffiya mace sai idan an tabo ni.
Tace amma ai yanada kyau mutum yakasance yanada hakuri.
Nidai yanxu kigama cin abuncinnan kicire uniform sai ki kaimun markade.Tace to umma.
By maryam ashutrah
![](https://img.wattpad.com/cover/175608420-288-k615443.jpg)
YOU ARE READING
MAYIESHA
Short Storylabarine akan wata mace jaruma wacce kwasam bazato ba tsammani ta tsinci kanta a cikin wata duniya. Shin ta hadu da qaddarar tane kokuma mutuwarta. Kubiyoni domin jin yadda ta kasance