Da rana suka gama shirinsu sannan suka wuce zuwa gidansu.
Suna isa aka bude musu gate suka shiga.Misha tana fitowa tace wow daddy i love this house.
Yace to wannan shine gidanmu kuma anan zamu zauna.
Taje gun motar Mayiesha tace daddy wannan motar waye.
Yace motar mummyn kice waccan kuma tawa.
Tace to nikam ina tawa daddy.Yace zan siya miki kema sai a rinka kaiki makaranta a ciki tace yawwa my daddy i love you.
Yace i love you too my misha.
Mayiesha tace nidai idan kun gama shirmen naku kusaman a ciki ta shigewarta.
Munawwar kuwa saida suka gama surutunsu sannan suka shigo.
Misha tace daddy where is my room.
Yace yana sama a gefen na mummyn ki anjima zamuje tare sai nasiyo miki toys da sauran kayan wasa a saka miki a ciki.
Tace muje ka nunamun sukaje dakin tace wow daddy this room is beautiful i really love it.Yace it will even look more beautiful when we decorate it later.
Masu aiki suka fito dukansu sunayi musu sannu da zuwa.
Sannan suka wuce zuwa kitchen hada musu abunci
Sunayin wanka suka sauko qasa cin abunci sai mayiesha tace yawwa dama nayi magana da abba nace dasu zamuje qarshen wannan satin mugansu.
Yace ba damuwa Allah yakaimu.
yawwa dama inason nafada miki zan chanja muna motoci.Tace abban misha amma ai naga wadannan ba abunda sukayi.
Yace ehh amma ai latest dinsu zamu siya.
Tace ba damuwa Allah ya qara budi na alhairi yace ameen.Qarshen satin dukansu harda hajiya suka tafi katsina inda sukaje gidan abba.sun tarbesu da kyau sosai.
Mayiesha tacewa misha wannan grandaddy dinkine.
Wannan kuma Granny dinkice.
Tace umma i like them.Abba ya dauki misha yace yer baturiya mai wayo sosai.
Misha tace daddy na yakoyamun wayo.Munawwar yace Mayiesha zan barku anan sai anjima sai nazo mutafi hajiya takirani akwai abunda zamuyi tace to Allah yakiyaye ya fice.
Misha ta saka kuka itakam a dole saitaje da daddyn ta dakyar suka lallasheta.Hajiya da munawwar sukaje company din alhaji wanda bayan cike ciken takardu da sauransu ya zamanto a karkashin kulawarshi.sanann hajiya ta damka mishi harkokin business dinta dake qasar italy da paris.sannan da sauran companies din.
Yaji dadi sosai sannan yace hajiya kitayani adduah Allah yabani ikon rikewa tace Ameen.Da daddare munawwar da hajiya suka zo gidan abba.inda matar abba ta dafa musu tuwon shinkafa da miyar taushe da man shanu.
Sunaci suna santi.
Munawwar yace gsky aunty kin iya girki sosai.
Tace nagode munawwar amma ai sbd ka dade bakaci abuncin gargajiya bane shiyasa.
Mayiesha tace kikyaleshi aunty kawai fah sbd yace kinfini iya girkine dukansu sukayi dariya.Duk abuncin da sukeci itakam misha saishan cornflakes dinta takeyi acewarta bazataci tuwo bah.
Suna gamawa sai munawwar yace abba dama inason nabiya maka kaida aunty kuje umra wannan watan inshallah.
Abba yayi farin ciki sosai yayi godiya.
Aunty kuma harda yen hawaye acewarta ko abuja bata taba zuwabah gashi yanxu zataje umra.
Tayi godiya sosai.
Hajiya tace ka kyauta sosai munawwar haka akeso mutum yadinga kyautatawa yen uwansa.
Allah yayi muku albarka dukansu
Sukace ameen.
Basu wani dadebah suka fice zuwa gida.
Washe gari kuma suka koma Abuja.Bayan wata biyu
munawwar yaqara zama wani irin babban attajiri ya gina masallatai da gidan marayu sannan yana taimakon mutane iya iyawarsa.Hakama Mayiesha taginawa ummanta masallaci da rijiyoyi a katsina sannan tana taimakawa yen uwansu sosai dama talakawa. bayan haka tana kasuwancin atamfofi da sauran kayan mata tare da hajiya sannan kuma tana da ciki wata daya.to Allah ya sauketa lafiya
Misha kuma an sakata a makaranta inda take kokari sosai gurin karatu.gata kuma da wayo sosai.
Bayan wata takwas ta haifi danta namiji kyakkyawa wanda yaci sunan mahaifin munawwar wato abdulhakeem wanda akekira da mubeen.inda akayi buki na kece raini.
Hajiya tatashi bata danjin dadin jikinta inda suka tilasta akan lallai saitazo ta zauna dasu sbd basason tana zama ita kadai gashi tsufa yafara yau lafiya gobe jinya.
Tana zaune a babbar kujera tana dauke da mubeen.tace ina godewa Allah daya azurtani da 'da irinka munawwar sannan da suruka kuma 'ya mayiesha sai kuna jikokina kyawawa misha da mubeen ba abunda zance saidai nace ALHAMDULILLAH.
(The family of M)ALHAMDULLILAH
GODIYA TA TABBATA GA UBANGIJI ALLAH WANDA YANUNA MUN NAGAMA WANNAN LITTAFIN MAI SUNA MAYIESHA kuma ina mika dunbin godiyata ga masoyina.
Ina tare daku da kowane lokaci ni taku maryam shehu ibraheem(ashutrah)Kujira sabon littafina mai fitowa.luve you all😘😘😘😘😘😘😘😘😘😘😘😘😘😘😘😘😘😘😘😘.

YOU ARE READING
MAYIESHA
Short Storylabarine akan wata mace jaruma wacce kwasam bazato ba tsammani ta tsinci kanta a cikin wata duniya. Shin ta hadu da qaddarar tane kokuma mutuwarta. Kubiyoni domin jin yadda ta kasance