Da safe abba da munawwar na zaune suna kallon news itakuma tana kitchen tana hada breakfast.
Tana cikin soyar dankali sai taji an rufe mata ido tace to yanxu ma bazaka barni nayi aikinbah.
Yace naga ai aikinne yayi miki yawa a gaskiya dole yau nakira yen aikinki su dawo.
Tace da dai yafikam.Suka gama hada breakfast din tare suka kai parlor.
Bayan sun gama munawwar da abba suka fita.munawar ya zazzagaya dashi ko ina a cikin garin sannan sukaje cash n carry suka danyi shopping sannan suka dawo gida.Mayiesha na daki kwance tana hutawa sai taji cikin ta yafara ciwo.nan take abun ya fara tsanani da sauri ta dauki wayanta takira munawwar cikin sauri ya iso daki ya tallabeta sai mota.
Abba na gaban mota munawwar yayi driving suka wuce asibiti.Suna isa aka shiga da ita labour room.
Munawwar yakira hajiya ya sanar da ita halin da ake ciki.Ba bata lokaci saigata a asibitin.
Mayiesha tasha wahala sosai sai bayan awa uku sannan ta samu ta haihu.inda ta suntulo yer ta kyakkyawa fara tass.
Likitan na fitowa tace ina mijinta
Yace gani
Tace ina tayaka murna matarka ta haihu ta haifi diya mace.Dukansu sukayi hamdalah sannan sai likitar tace yanxu dai tana dan hutawa zuwa anjima saiku shiga kuganta.
Munawwar kam farin cikiba daga nan bah.
Haka abba da hajiya.Bayan awa daya suka shiga ciki hajiya ta dauki jaririyar ta kalleta tace amma wannan yarinyar mashallah akwai kyau gashi tana kama da mamanta.
Da sauri munawwar ya dauketa ya kalleta sosai sannan yayi mata kiss a gishi yace barka da shigowa duniya my daughter Allah ya rayamun ke.
Dukansu sukace ameen.
Bada jimawabah Mayiesha ta farka sannan ta karbi babyn ta takallah tace wannan yarinyar kin wahalar dani sosai amma dai Allah ya albarkaci rayuwarki .dukansu sukace ameen.
Da daddare aka sallamesu suka wuce zuwa gidan hajiya.
Sbd tace bazata zauna a gidan tabah sai tayi arba'in
Sannan tace jibi zamuje katsina sbd achan nakeso ayi bikin tunda
Duk yen uwana suna chan.
Dukansu sukace to Allah yakaimu.
Mayiesha tanashan kula sosai ga hajiya da kuma baby wacce dakeda yawan kukan banza.Ranar biki yarinys taci sunan mahaifiyar mayiesha inda ake kiranta da MISHA.
Anyi taro sosai sbd har yen uwan alhaji abdulhakeem dake zama a kaduna saida suka halacci bukin sannan da qawayen hajiya wadanda ke zama a qasar waje dakuma na sassan nahiya daban daban.
Misha kuma tasha kaya kala kala.Bayan sunyi kwana arba'in a katsina sannan suka fara shirye shiryen dawowa.
Munawwar yaje gun abba yace abba ya maganar mu
Abba yace wace magana kenan
Ta aurenka mana
Ohh munawwar kenan mun sasanta da wata bazawara dake hayin layinmu kuma ta amince saidai kawai yanxu ni ake jira.
Amma tana da 'ya yer qarama.Ai abba wannan ba matsala bane kuma kaga zakuci gaba da kula da ita tare amma ninakeso na dauke nauyin bikinan gabaki daya kawai idan an saka rana sai kafadamun.
Abba yace munawwar kenan waton kama fini son wannan auren
Wlhy abba kawai banason kana zama kaikadaine kaga akwai kadaici
Hakane maganarka munawwar Allah dai yashige muna gaba
Yace ameen.Da suka koma abuja hajiya ba qaramin shirya Mayiesha tayibah sannan ta koma gidan mijinta.
Bayan munawwar ya sanar da Mayiesha da hajiya akan auren abba ba qaramin dadi sukajibah sannan suka saka albarka.
Hajiya tace amma fah yakamata yakasance kafin kuwuce london sbd kunga admission dinku yafito kawai abunda yarage shine kufara shiri.
Dukansu sunji dadi sosai sannan bayan munawwar ya sanar da abba shima yayi farin ciki sannan yace sunje sun samu iyayen matar kuma sunce ko nan da sati biyi ma yayi.Munawwar yace to Allah kaimu.
Bayan ya sanar da hajiya dukansu suka fara shirye shirye daga lefe har izuwa hadimar biki duka hajiya ta dauka.
Bayan sati biyu akayi bikin alkasim wato abban mayiesha da habiba.
Bikin anyishi dai dai baiwuce tsaribah saidai hajiya sunyi hidima sosai gun walima.
Ana kawo amarya ya gabatar da ita gunsu hajiya.
Yace wannan itace 'yata tilo wato mayiesha ameenatu
Saikuma munawwar mijinta sannan mahaifiyarsa wato hajiya salamatu.
Mutanen kirkine wadanda ba kamar su sannan bamuda kamarsu a duniya sbd haka kema inason ki kyautata musu sosai Allah yabamu zaman lafiya.
Tace inshallah zan kyautata musu sbd ai baza kaki mai sonkabah.
Hajiya tace to Allah yabaku zaman lafiya da kuma aure mai dorewa
Dukansu sukace ameen
Bayan wani dan lokaci suka tashi zuwa gida.
Inda akabar ango da amaryarsa😜😎
Mayiesha na cikin bacci misha ta tashi sai faman kuka takeyi amma Mayiesha da nauyin bacci duk batajibah munawwar yatashi ya dauketa sannan ya dinga bubbuga Mayiesha dakyar tatashi ta karbeta.tace wlhy Misha tacika tsiwa.
Munawwar yace nidai kada kiyiwa 'yata fada.
Da kyar aka saku takoma bacci sannan suma suka koma bacci.Washe gari da safe sukaje sukayiwa su abba ban kwana sannan suka kamo hanya zuwa abuja.
Suna dawowa suka fara shirye shiryen tafiya London.
Bayan sun gama komai ranar jumuah suka shiga jirgi zuwa london.Suna isa suka wuce masaukinsu wani babban gida me mai matukar kyau wanda anan hajiya ko alhaji suke sauka idan sukazo london.
BAYAN SHEKARA UKU🌼🌼🌼
suna sunata shirye shiryen dawowa musha tace ammi kenan zamu koma nigeria bazamu dawobah.
Mayiesha tace misha kenan zamu dawo wani lokacin amma dai bayanxu kusabah.
Munawwar yace ki kyaleta zan dinga kawoki idan kinaso kinji.
Tace yawwa daddy na.
Munawwar yace kinga gobe zamu wuce umra zamuyi kwana goma sannan daga chan kawai muwuce zuwa Nigeria.
Tace hakan ma yayi sosai.Suna gama umra sannan suka kamo hanya zuwa Nigeria.
Suna isowa Nigeria aka aiko driver ya daukesu suka sauka a gidan hajiya.
Da sauri misha taje gunta tace granny nayi missing dindi kikace zaki zo amma baki zobah.
Hajiya tace kiyi hakuri banida lafiya ne shiyasa.
Mayiesha tace hajiya ya jikin naki.
Wlhy da sauki sosai Mayiesha
To Allah yaqara sauki.
Misha taje gun munawwar tace abba wannan shine gidanmu.
Yace no wannan gidan hajiyane gobe zamuje namu gidan.Tace i hope yafi gidanmu na london kyau
Mayiesha tace misha kiyi shuru da bakinki kincika surutu.
Hajiya tace ku kyaleta tayi maganarta
Yanxu dai kuje ku huta sannan kuzo kuci abunci.
Suka tasho zuwa daki mayiesha tace misha zonan.
Misja tace no nikam ina nan gun Granny dina ita zata kula dani.
Hajiya tayi dariya tace sosaima kuwa baby na.Bayan sun huta sannan suka sauko zuwa cin abunci suna gamawa suka fice daki domin su kwanta.
Misha kuma ta lakewa hajiya lallai saidai su kwana tare.Mayiesha takira abba take sanar dashi dawowarsu .yayi farin ciki sosai sannan tace qarshen sati zasuzo nan katsina.
Yace Allah yakaimu.By Maryam ashutrah

STAI LEGGENDO
MAYIESHA
Storie brevilabarine akan wata mace jaruma wacce kwasam bazato ba tsammani ta tsinci kanta a cikin wata duniya. Shin ta hadu da qaddarar tane kokuma mutuwarta. Kubiyoni domin jin yadda ta kasance