This page is dedicated to my beautiful family lov u all😘
Cigaban labari🌼🌼🌼🌼🌼
Yana fitowa sai yaga raunat bata waje yasan ta tafi kiyo.
Yace amma yakamata nadan zagaya naga yadda wannan gurin yake.Yana cikin tafiyane sai ya hango wata tsohuwar mai siffar mutane amma kunnayenta kamar na alade tana zaune agurin wata magudanar ruwa tacika tulu amma takasa dauka.
Yadan firgita kadan da ganin irin wannan halittar amma sai yanuna rashin tsoro yabi ta gurinta zai wuce sai tace dashi yakai wannan dan saurayin katemakamun na aza wannan tulun akaina.
Ya kalleta cikin rashin yarda amma sai yaga yakamata ya taimaketa sai yace idata to.
Har ya dauki tulun zai aza mata akai saikuma tace kaga inada karancin karfi a tattare dani ka taimakamun ka isar mun dashi har izuwa masaukina.
Yace to shikenan muje
Tana tafe a gaba yana biye ta ita a baya.
Suna cikin tafiya kawai sai matar tasaki wata irin gigitacciyar dariya nan take saita kidime tazama wani irin qaton dodo mai matukar girma.Nan take munawwar ya saki tulun ganin wannan halittar.
Sai tace kai aganinka ka tausayamun kenan koh shiyasa zaka taimakamun
To nikuma wannan qarfen tsafi dake hannunka nakeso kabani.Yace bazan bakibah saidai kikarba da karfi.
Nan kuwa tasake wata irin dariya sai kawai ta ziro dogon harsheta da niyyar zata kamashi.
Ai kuwa nan take yayi tsalle yayi sama.Ta kalleshi sannan itama ta zira hannunta mai tsayin gaske zuwa kamashi amma yayi nasarar sarar mata hannu.
Ai kuwa sai tarabu kashi biyu wata dodonniya tafito daga jikinta sai suka zama su biyu kenan.Munawwar bai tsorata bah sai kawai yace mata nayi niyyar yimiki alkahairi amma zaki sakamun da sharri.
Ta kalleshi tace kaine kasan wani abu alhairi nikuma bansanshibah nan take suka kaimasa hari.
Idan yasamu nasarar datsar wani ban gare na daga jikinsu sai su qara yawa.
Nan kuwa suka rikide cikin wani irin gumurzun yaki amma basu samu nasara akansabah.Suna cikin fadar bai ankarabah sai wani dodon ya sareshi a gefen wuyanshi nan take yasaki wata irin qara ya juya sai yamaida takubbansa guda biyu.
Yafara fada dasu cikin zafin nama.Wani dodon ya ziro harshensa kenan zai kama qafar munawwar sai kawai ji akayi fasss jini yana zuba.
Munawwar yana juyowa yaga mayiesha ce.
Ta kalleshi tace bazaka iya kaikadai bah dole saida taimakona
Cikin fushi mayiesha tayi tsalle ta sare kan daya daga cikin dodannin sai kawai ganin akayi kansa a qasa yafadi matacce.Munawwar yace kenan takobinkice kawai zata iya kashesu.
Tace hakane sbd haka kabarni kawai dasu.
Ai kuwa haka akayi saidai kawai a dinga ganin rabin jikin dodanni da kawunansu suna faduwa a qasa.
Suna cikin gumurzun yakinne taga munawwar yana kokarin faduwa a kasalance sbd sarar da dodo yamasa a wuya jini take fitarwa sosai.Nan kuwa hankalinta yayi matukar tashi sosai sai ta shafa qarfen tsafi dinta nan take sai ga raunat tazo gurinda suke.
Suka samu dakyar suka hau saman raunat ta tashi da sauri.
Tana tashi tayo qasa cikin sauri sai kawai ganin kake dodanni na mutuwa saida raunat ta kashesu gabaki daya sannan tayi sama sai faman gudu takeyi.
Mayiesha ta kalli munawwar dake kokarin sumewa tace dan Allah munawwar kakara hakuri yanxunnan idan muka isa duniyar mu zamu samu guri mu tsaya.Ya kalleta yace muna sauka kihada qarfin inwak dina da bahij dinki saiki shafamun a fuskata.
Cikin kuka da tausayin halinda yake ciki tace to zanyi hakan.Har kusan awanni biyar suna ta fanan gudu saman iska tun munawwar yana daukrewa harya sume.
Suna shiga duniyarmu nan take tafara ganin ruwa ta ko ina da ciyawu kala kala nasu kyan gaske.sai taga wani irin duhu kuma yana tunkarosu tana ganin hakan tasan aljannune suke son hakasu shiga.Duhun yana tunkarosu sai mayiesha ta kalli raunat ta shafa gashin jikinsa tace Bismillah allahu akbar.
Aikuwa nan take raunat ta qara gudu sukayi cikin dubu dinnan da gudu.
Kafin kiftawar ido sai duhun ya watse.
Sai suka ga wani dan gari qarami ba komai a cikinsa daga dabbobi sai bishiyoyi.
Ta shafa raunat tace da ita musauka anan saboda nayiwa munawwar magani.
Ai kuwa nan take raunat tafarayi qasa qasa har saida suka sauko.
Suna saukowa nan take duka dabbobin dake gurin suka dinga guduwa sbd ganin tsabar girman raunat.Itakuma mayiesha tana saukowa daga bayan raunat tayi saurin rufe idanuwanta tare da shafa bahij dinta nan take sai daki ya bayyana a gabanta.
Da sauri tadinga jan munawwar a hankali sbd bazata iya daukan shibah har daki.
Tana kwantar dashi ta kalli kyakkyawar fuskarsa tace yayanna bazaka banni bah ka mutu inshallah yanzunnan zaka farfado.
Ta hada bahin dinta da inwak dinshi nan take suka bada wanj irin farin haske sai ta shafa a fuskarsa.
Nana take sai jinin dake zuba a fuskarsa ya tsotse tayi sauri ta yaga mayafinta ta daure masa wuyansa inda yaji rauni.
Sannan ta samar da ruwa ta dinga goge masa duk inda jinin ya bushe a fuskarsa.
Ta dauki hannunsa ta dinga gogawa tana dan Allah yaya munawwar ka farka.
Amma saidai yana numfashi amma ba alamun farkawa.Nana take ta fashe da kuka tana fadin dan Allah yayana ka farka kada ka barni bayan na cika maka burinka na dawo dakai duniyarka zakaga mahaifanka.
Amma shuru baya motsi saita kwantar da kanta kan kirjinsa tana jin bugun zuciyarsa tana kuka har bacci yayi gaba da ita cikin tsabar gajiya.
Shikuma nan take sai munawwar yaji zuciyar shi tana bugawa da qarfi sai ya dinga bude idanunsa a hankali.
Ya saukar dasu akan mayiesha dake kwance akan kirjinsa.By maryam ashutrah

ŞİMDİ OKUDUĞUN
MAYIESHA
Kısa Hikayelabarine akan wata mace jaruma wacce kwasam bazato ba tsammani ta tsinci kanta a cikin wata duniya. Shin ta hadu da qaddarar tane kokuma mutuwarta. Kubiyoni domin jin yadda ta kasance