Harta juya zata tafi sakuma nabila ta hango ipad din mayiesha a cikin qaramar jakarta
Tayi saurin taci gabanta tace aisha inaso naga wannan wayar dake a jakarki
Aisha tace sbd me
Sbd naga tayi kamada ta mayiesha ne
to ba ita bace wannan ta wani abokinane
To kinunamun mana
No basai kingani bah
Aikuwa nan nabila tayi sauri ta saka hannunta a cikin jakar aisha ta fiddo ipad din tace jar ubannan kai wato aisha dama kece kika dauki wannan ipad din shine kuka wani fuske.
Aisha tace dalla malama kibani wayana ta kwace iPad din daga hannun nabila.
Nabila tace waton aisha bayan iskanci da lalata abokanai dakuma shaye shaye harda sata kikeyi kuma kirasa wacce zakiyiwa sata saini.
Anyi miki sata din kokinada qarfine ki kwata banza kawai marar hankali kinga kifice daganan kafin na sako miki karnuka wlhy.
Nabila najin anyi maganar kare tace kinyi hasara wlhy shegiya wulakantatta.
Tace ai kece babbar wulakantatta wacce take son halakar da yen uwanta banza marar wayo kawai.
Nabila tafice tana maijin haushin aisha dakuma tunda duk irin abubuwanda tayi mata abaya.
Bayan wata daya:
Suna fitowa daga lectures fatima tace wai wlhy nagaji sosai gashi yau wannan lecturer din ya wahalar damu
Mayiesha tace kedai kawai kibari gashi da kallon mata.
Nidai yanxu zan wuce gida sbd nima a gajiye nake sosai gashi inajin bacci.
Amina tace waike mayiesha anya lafiya kike kuwa naga ko a class muke saiki fara tangadin bacci idan kuma muka fito saikice bacci kikeji sosai kiyi saurin wucewa gida.
BINABASA MO ANG
MAYIESHA
Short Storylabarine akan wata mace jaruma wacce kwasam bazato ba tsammani ta tsinci kanta a cikin wata duniya. Shin ta hadu da qaddarar tane kokuma mutuwarta. Kubiyoni domin jin yadda ta kasance
