MAYIESHA PART 6

919 90 1
                                    

Suka hada hannunsu tare sannan ya kalleta itama ta kalleshi tace muje na shirya.

Sukayi bisimillah tare da tashi sama sai da sukayi nisa sosai suka kalli qasa sukaga sunyi nisa da gurin da suke sosai sannan suka nufi gabas.

Cikin sauri suke tafiya inda suke kallon qasa irin hallitunda ke cikin ta.
Har sunyi nisa kawai sai sukaga wani irin qaton tsuntsu mai mummunar halitta yana tunkarosu

Munawwar yace kishirya fah sbd idan har bamu kasheshibah to shi zai kashemu.

Tsuntsun yana isowa gun da suke sai suka rabu hanya biyu munawwar yayi hagu itakuma tayi dama.
Nan take sukayo cikin tsuntsun da zafin nama.
Suka fidda takobinsu suka kaimasa suka da qarfi.

Yayinda munawwar yaci galabar fille masa kai.

Nan take tsuntsu ya bace batt kamar ba'a taba yinsabah.

Cikin sauri mayiesha taje gunda munawwar yake tace munyi nasarar kashesa.

Munawwar yace wannan qaramine dole sai mun dage dantse sosai sbd duk wadannan aljannune sukeson halakamu.

Tace na fahimta muci gaba da tafiya kawai.
Suna ta tafiya a sana cikin gudu da sauri sunata haduwa da tsuntsaye kala kala masu cutarwa amma Allah yana basu ikon kashesu.

Har dare yayi sannan suka sauko zuwa wani dan qaramin gari wanda yakeda wasu halittu kamar na mutane amma ba mutane bane.munawwar yace zamu kafa wani tsari anan ta yadda bazasu iya cutar damubah.

Tace to shikenan amma fa yunwa nakeji sosai.
Yace kada kidamu tunda muna tare da qarfen tsafi dinmu komai zaizo mana da sauki.

Bayan sun hada daki guda daya mai tattare da qarfin tsafi sannan suka shiga ciki.

Suka hada abunci sukaci sannan tace yanxu inason nashirya yaza'ayi

Yace to nahanakine

Tace to kana nufin a gabanka zan shirya
yayi dariya yace ai saima nashirya miki dakaina.

Ta dauki filo ta jefa masa tace bakada kunya munawwar

Yayi dariya yace to ai saiki koyamun nidai ina waje inajiran kikare.
Tace taya zaka fita waje bayan kasan akwai hatsari sosai

bakajin dabbobi yadda suke wani irin kuka mai ban tsoro.

Yace kada ki damu zan iya kare kaina.

Tace to dan Allah ka kula sosai nima zanyi sauri nashirya sbd mu kwanta da wuri yadda zamu tashi da wuri yace to badamuwa.

Tana cikin shiryawa sai taji hayaniya tayi yawa sosai a waje tace nashiga uku Allah yasa ba hari aka kawo mana bah da sauri ta shirya tafito.

Tana fitowa sai ta saka ihu tace munawwar bayanka yana juyowa yaga wata irin halitta da sandar qarfe zata sara mishi cikin zafin nama yayi sama da sauri
nan take dodon shima yayi fukafukai yayi sama mayiesha na ganin haka tayi sauri tayi sama cikin zafin nama takaiwa dodon suka ta gefensa.

Nan take dodon yasaki wata irin qara ai kuwa saiga dodonni masu yawan gaske sun fito tako ina suka fara tun karo su munawwar.

Cikin tashin hankali munawwar yacewa mayiesha bazamu iya da wadannan dodannin bah kiyi sauri ki shafa tsuntsuwar ki.

Cikin sauri mayiesha ta shafa tsuntsuwar ta dake jikin bahij dinta ai kuwa nan take saiga raunat (tsuntsuwar mayiesha).

Sukayi sauri suka hauta cikin wani irin sauri ta fice daga gurinda dodannin suke aikuwa sai dodannin suka bisu.

Cikin kiftawar ido sai kawai suka nemi dodannin suka rasa sbd tsananin saurin raunat wanda har su saida sukayi mamaki.

Suna ficewa daga wannan diniyar mayiesha tajuyo ta kalli munawwar cikin farin ciki shima yasakar mata murmushi sannan suka shafa raunat.

tayi wata irin Qara sannan taci gaba da tafiya cikin wani irin sauri.
Sai mayiesha tace wlhy munawwar bacci nakeji ga yunwa sannan nagaji sosai.

Yace kenan baki shirya tafiyarbah shine kikace mufarata ai dole sai munyi hakuri yanxu bari musamu guri mai kyau sannan musauka kafin safiya ta ida wayewa.

Tace to shikenan.

Sunata tafiya har saida safiya tafara wayewa dukansu sun gaji amma kwata kwata ba alamar gajiya tattare da raunat sai tafiya take tayi.

Munawwar yana saukar da kansa qasa sai yaga har sun shigo wata duniyar wadda daga ita sai tamu duniyar sannan yace da raunat ta sauka anan su huta.

Ai kuwa nan take tafarayi qasa qasa har saida suka sauka qasa sannan suka sauka daga raunat.

mayiesha ta kalli munawwar ta dafa kafadarsa
Tace munawwar ruwa ruwa kawai saita fadi qasa.

Yayi saurin tallabarta ya taba inwak dinshi nan take sai daki ya bayyana a gabansu.

yayi sauri ya tallabeta yakaita dakin sannan ya kwantar da ita.

Yayi sauri yaje waje gun raunat yace kihuta sosai sbd inason idan muka tashi tafiya sai kin kaimu har gida tayi qara kadan ma'anar ta fahimci abunda yace sannan yakoma daki.

Yana zuwa ya kalli mayiesha sannan ya dauki hannunta dake rike da bahij dinta ya shafa mata a fuskarta nan take ta farfado ya bata ruwa tasha sosai sannan ya zauna yanata bata abunci a baki tanaci.

Bayan sun gama cin abunci sannan yace da ita kidan kwanta kihuta kinji.

Tace nagode munawwar

Yace dame kenan

Tace yadda kake kula dani

Yayi dariya sannan yace ai kamar qanwata kike dole na kula dake.

Sannan ta kwanta nan take bacci ya dauketa.

Ya gyara mata kwanciyarta sannan ya kalli kyakkyawar fuskarta yace kinada kyau.

Shima ya kwanta a qasa saida sukayi baccin kusan awa biyar sannan munawwar ya farka.

Yana tashi yaje yayi alwallah yayi sallah sannan ya tada mayiesha.

Tana tashi yace kiyi sauri kiyi sallah sai kidan huta sbd muci gaba da tafiya.

Tace to yaya munawwar.

Ya kalleta cikin mamaki yace yau kuma nine yayan.

Tace ai ka chanchanci nakiraka da hakanne shiyasa.

Yace to godiya nake sannan yafita zuwa waje.

By maryam ashutrah

Pls your votes and comments are needed and i hope you re really enjoying my short story.
Luv u all.

MAYIESHA Tahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon