Munawwar yace umma wacece wannan bansantabah.
Wannan aminiya tace tun muna yara muke tare.tazo nan ne bikin qanena ne da akayi satinda ya wuce shine takeso takoma gobe.
Yace umma meyasa kika dawo nan da zama bayan ada kaduna muke.
Tace bawai nadawo katsina da zama bane kawai nazo bikine kuma ina hada wasu takaddun filayen mahaifinkane dake nan katsina idan na qare zamu koma abuja sbd bana son zama a kaduna sbd ganin nake a yanxu kowane lokaci wannan bokanyar zata iya sake kwacemun kai sbd haka zan siyar da gidanmu na kaduna.
Yace da izinin Allah umma bazata iya yimun komaibah a yanxu sbd nafi qarfinta.
Suna cikin magana sai aka kirashi a waya yana dubawa yaga abba me yake kiranshi.
Yana dauka sai yace da fatan kana lafiya munawwar yace lafiya qalau abba .
Yasu umma
Abba yace gata ku gaisa.
Ta karbi wayan umma tace dana munawwar kana lafiya.
Munawwar yace lafiya qalau
Tace to ka kula da kanka kuma kasaki jiki da ummanka sbd zataji dadin hakan sosai.
Yace to umma nagode saida safe sukayi sallama yakashe.
Hajiya tace munawwar banason kana rika irin wannan wayar daga yau sbd haka gobe zan baka kudi kaje kaida umar sai kasiyo irin ta yayi.
Sannan kuma zai dinga koya maka mota sbd inason nasiya maka mota bayan haka kuma sai kuje banki abude maka account yanda kaima zaka dinga amfani da kudinka basaina dinga bakabah.
Yace to umma nagode.
Tace nace maka kadena godemun idan na maka abu.
Yanxu katashi kaje ka kwanta saida safe yace to umma saida safe.
Yana shiga dakinshi yaga yanda aka gyara ko ina ya qara kyau sosai.sai yaje yayi wanka sannan yasaka kayan bacci yayi shafa'i da witr sai ya dauko gana must go dinshi ya bude ya dauko hotonda sukayi tare da mayiesha yana kallo.
Ya daga wayarsa yakirata bugu uku ta dauka.
Suka gaisa sannan suka danyi hira na wani lokaci sannan sukayi sallama ya kwanta..
Washe gari mayiesha ta gama shirinta tsaf xuwa makaranta saita daga wayanta takira wayan munawwar har kusan sau uku sannan ya dauka.
Tace ina kwana yaya
Yace lafiya qalau qanwata
Tace har yanxu bacci kakeyi baka tashibah
Yace ai gashi yanxu kintadani
Tace to katashi kaje kayi wanka sannan ka karya yace to qanwata.
Tace nidai zantafi makaranta saina dawo.
To ayi karatu dayawa sukayi sallama ya kashe.
Yana tashi yaje yayi wanka yana fitowa ya shafa tsadaddun man shafawansa ta taje gashin kansa sannan ya feshe jikinsa da turaruka masu dadi sannan ta bude drawer ya dauko qananan kaya masu kyai yasaka.
Yana saukowa zuwa parlor ya tadda hajiya zinaru zata wuce.
Bayan ya gaidasu sannan yace hajiya har zaki tafi
Tace wlhy yanxu zan tafi munawwar sai kuma idan aurenka ya tashi.
Ya shafa gefen fuskarsa cikin kunya.
Hajiya salamatu tace kidena zolayarshi fah.
Bayam sun rakota har gun mota tashiga sukayi sallama sannan tafice zuwa airport.
Suna shiga parlor yawuce dinning ya dibo abunci soyayyen dankalin turawa da kwai da kuma shayi mai kauri da sausage.
Ya kalli abunci yace Allah sarki jinake kamar naje nakaiwa mayiesha sbd nasan watakila yau koko da kosai tasha tafice makaranta.
YOU ARE READING
MAYIESHA
Short Storylabarine akan wata mace jaruma wacce kwasam bazato ba tsammani ta tsinci kanta a cikin wata duniya. Shin ta hadu da qaddarar tane kokuma mutuwarta. Kubiyoni domin jin yadda ta kasance
