MAYIESHA PART 28

597 25 0
                                    

Bayan Mayiesha ta farfado ta huta sannan aka sallamesu suka koma gida.
Sosai hajiya take kula da ita.

Munawwar kuma banda damuwa ba abunda yakeyi haka dai yashirya yaje gidan abokinsa ahmad.
Ahmad yace lafiya munawwar ma ganka a haka ba nutsuwa
Wlhy wata mastsalace narasa yadda zanyi dakaina.
Yace fadamun ina saurarenka.
Ya fada masa komai abunda yafaru.
Ahmad yace lallai kuwa dole ka rikice amma yanxu kada ka damu nasan koda kaje hajiya bazata saurarekabah amma ni zanje nayi mata magana.
Yace yawwa friend Allah yasa ta fahimceka.
Ameen
Sukayi sallama yafice gida.
Da daddare Ahmad yashirya yaje gidan hajiya yana shiga suka gaisa sannan yace hajiya dama inaso nayi magana dakune akan munawwar.
Hajiya tace kaga ahmad nasan duk bakinku daya dashi basai kayimun wannan maganarbah nasan shine ya turoka to kaje kace mishi yakiyayeni.
Ahmad yacd hajiya da dai kun saurari abunda zan fada.
Tace ba abunda zaka fada na yarda dakai kawai katashi katafi.
Yace to nabarku lafiya yatashi ya fice daganan kawai ya fice zuwa gidan munawwar.
Bayan ya sanar dashi yadda sukayi da hajiya sanan munawwar yace to yanxu meye mafita.
Ahmad yace nimadai bansanibah amma  inada wata yer shawara.
To kafada mana
Mezai hana kadena zuwa gunsu sannan tunda kaga yau kagana exam dinka kawai ka shirya ya koma katsina idan kuma ka kashe wayarka.
Idan komai ya lafa sannan suka dena ji daga gareka nawasu kwanaki dole su zasu fara nemanka.
Yace good wannan shawarace mai kyau kuma haka za'ayi.

Washe gari ya kashe wayarsa sannan yafadawa ma aikatan gidanshi yabasu hutu sai idan ya nemesu.
Daga nan yabasu wasu yen kudade sannan ya fice zuwa Katsina.

Yana isa Katsina ya fice zuwa gidansu mayiesha.
Abba yayi farin cikin ganinsa sosai sai kuma munawwar yabashi labarin duk abunda yake faruwa.
Abba yace tabbas nasan mayiesha da kishi sosai amma kada ka damu idan ta sauko ita da kanta zata nemeka.

Bayan kwana biyu Mayiesha na kwance akan gadonta sai tunane tunane takeyi sai hajiya tashigo.
Tace Pls Mayiesha kidena wannan damuwar kada ya taba lafiyarki.
Mayiesha tace kinga fah hajiya ko gidannan yadena zuwa yaganni.
Sbd fatima ta fiye masa ni.
Hajiya tace kiyi hakuri bari nakira wayarsa.
Takira wayar har sau biyu amma a kashe.
Tace kinga wayarsa a kashene

Mayiesha ta fashe da kuka tace watakila yanxu haka suna tare shiyasa yakashe wayarsa.
Hajiya tacd barshi kawai zanyi magana dashi.
Da kyar hajiya tasamu Mayiesha taci abunci sannan ta kwanta.

Har kusan sati daya idan hajiya takira wayarsa sai taji a kashe.

Mayiesha tace nifa hajiya hankalina yafara tashi anya kuwa lafiya munawwar baya daukar wayansa kodai zamuje mudubane.

Hajiya tace gaskiya kam sbd yau kusan sati daya kenan wayarsa a kashe amma bari na saka jamil yaje gidansa yadubo.

Takira jamil tace pls kaje gidan Munawwar ka dunomunshi sbd yau kusan sati daya ina kiransa amma wayansa a kashe.
Yace to hajiya.
Ba'a dadebah yadawo yace ban tarar da kowa a gidanbah saimau gadi wanda yasanar dani cewa yanxu kusan kwana goma kenan munawwar baya gidansa.

Hankalinsu duka yatashi sosai.
Mayiesha tace duk lafinane nashiga uku ina munawwar yashiga.
Da sauri hajiya takira wayar ahmad amma yanuna shi rabonsa da munawwar an dade.
Hankalinsu duka ya qara tashi

Da sauri hajiya tace maza jamil yaje police station yakai rahoto a fara nemansa.

Mayiesha kam sai faman kuka take gashi taki taci komai.

Abba da munawwar na zaune a parlor suna hira sai munawwar yace amma abba yakamata fah kasake wani auren.

Abba yace ai kuma yanxu na tsufa auren me zanyi.
Eh dukda haka zaka samu wadda zata dinga yimaka girki.
Hmm munawwar kenan to shikenan idan ma zanyi auren wazan aura.

Ai bazawara zaka samu ka aura kokuma cikin yem uwa kanema.
Yace to zanyi shawara amma bana tunanin za'a samu wacce zata maye gurbin matata yanxu

Inshallah za'a samu.
To Allah yakawo ta
Ameen.

Mayiesha na kwance a palon hajiya sai kallon hoton munawwar takeyi tana hawaye.
Dan Allah munawwar kadawo gareni kodan sbd danka dake cikina wlhy na hakura.
Tatashi taje gun hajiya tace har yanxu ba'a samu inda yakebah

Wlhy mayies ba'a samubah nima na damu sosai kuma tun farko mukayi kuskure da bamu saurare shibah.

Hakane hajiya.

Da sassafe bayan abba da munawwar sun gama karyawa saiga kiran ahmad yashigo wayan abbah.

Ya baiwa munawwar yace ga ahmad ne yake kira.

Yana dauka yace yane dan gari.
Ahmad yace kai najifah an fara sanarwa a tv ana nemanka Wlhy kadawo kafin karasa matarka.
Yace aikuwa gobe gobennan zan taso zuws abuja.
Yace dadai yafikam.
Yana kashe wayar yace amma yakamata fah gobe na shirya zuwa abuja.sbd wai har anfara nemana a talabijin.
Eh toh hakane yakamata sbd daga dukkan alamu sun fara nadamar qim saurarenka yanxu kaga idan kaje dole  da kansu zasusi suji abunda yafaru.
Hakane abba.

Abba yace amma nima dani za'aje kam sbd naga inda kuke zama.
To badamuwa Abba Allah yakaimu.

Washe gari hajiya da mayiesha na zaune a palo suna hira sai Mayiesha tace wlhy hajiya sai yanxu nasan inason munawwar kuma bazan iya rabuwa dashibah.

Hajiya tayi dariya sannan tace waton ko kunyata bakyaji koh.

Yanxu dai kitashi muje supermarket mu gama siyayyar kayan jaririnki.
Mayiesha tacd wlhy yau nauyin jikina nakeji sosai
Ai daurewa zakiyi.

Suna shiryawa suka je wuse market suka gama siyayyan kayan jariri.
Suna dawowa suka saka sauran kayan cikin akwati.
Mayiesha tace wlhy hajiya wannan jaririn yasha kaya yanxu fah akwati goma kenan mukayi.
Hajiya tace gsky kam amma ai dole na gyara mijina dakyau.

Sai sukaji ance kokuma matata bah idan macece.

Suna juyowa sukaga abba tare da munawwar a bayanshi
Da sauri dukansu suka tashi Mayiesha batasan lokacinda ta rungume munawwar bah sai kuka.
Abba yace yaran yanxu bakuda kunya a gaban nawa.
Da sauri ta sakeshi tana rufe fuska.
Suka samu guri suka zauna Mayiesha tace shine kaje ka barni nikadai.
Munawwar yace kekadai kuma ai ga hajiya kuma keda kanki kikadawo gurinta da zama.

Abba yace ina wuni hajiya
Lafiya qalau wlhy ashedai kana tare da dan naka.
Abba yace ai muna tare dashi a katsina.
Munawwar yace inawuni hajiya tace lafiya qalau munawwar

Abba yayi kyaran murya sannan yace naji duk abunda yafaru kuma a gaskiya baku tsaya kuma fahimceshi bane inda kukayi kuskure kenan amma bari kuji daga bakinsa.

Munawwar yafada musu komai daga yadda sukayi da fatima yadda tasamu nombar sa dakuma plan dinda suka hada da ahmad.

Mayiesha ta fashe da kuka tace kayi hakuri munawwar na zargeka da abunda ba hakabane
Yace bakomai ai tun farko sakaci nane.
Abba yace to ai haka akeso a fahimci juma kuma alhamdulillah kuma kinga daga yau idan kuka samu matsala saiku tsaya ku fahimci juna.
Hajiya tace hakane Nima kayi hakuri da naki na saurareka
Yace ba damuwa hajiya komau ya wuce.
Abba yace kunga tunda komai yazama dai dai gobe zan koma katsina.

Hajiya tace baza'ayi hakaban kabari kadanyi kwana biyu anan sai azaga dakai kaha yadda abuja take.
Munawwar yace hakane kam gsky abba kuma kaga sai muje gidanmu tare.
Abba yace taya zan kwana gidan ya ta ai ba'a haka a al'adarmu.
Mayiesha tace haba abba kada kace haka mana.
To shikenan naji.
Bayan sunci abunci dukansu suka huta sannan Mayiesha ta shirya suka koma gida.

By maryam ashutrah

MAYIESHA Where stories live. Discover now