Bari nayi miki adduah inshallah zai dena.
Tace wayyo nikam mutuwa zanyi.
Ya kalleta yace idan da mutuwa zakiyi da baki fadabah.yatashi zuwa parlor ya dauko ruwa cikin fridge da cup sannan ya dawo daki.
Ya zuba ruwam cikin cup yayi wasu adduoi sannan yabata yace kisha.
Tace bazan iya shabah.ai kuwa kokikarbi ruwannan kisha kokuma yanxunnan nakaiki asibiti ayi miki allura.
Dajin hakan tayi saurin karba sannan ta shinye duka ta bashi kofin.
Ya ajiye sannan yazo kusa da ita yace sannu matata yanxu zai dena ciwo kinji kidan kwanta ki huta.
Ta kwanta ya rufe ta da bargo sannan yayi mata adduah sannan yaje ya kwanta.
Washe gari da safe.yatashi yayi wanka ya shirya cikin getzner mai masifar kyau yafito kamar wani balarabe sai kamshi yakeyi.
Sannan yaje gun mayiesha yace tashi kije kiyi wanka muje mu gaida hajiya.Tace to.
Idan kin qare ina parlor ina jiranki.Yafice Itakuma tashiga wanka.
Tana fitowa ta shafa mayukanta masu dadin kanshi ta feshe jikinta da turaruka sannan ta fiddo wata abaya mai matukar kyau ta saka.Ta saki gashinta wanda ya kwanta har gadon bayanta sannan ta dauki mayafinta tafito.
Tana isowa gunda yake ta gurkusa har qasa tace ina kwana mijina.
lafiya qalau matata ya jikin naki.
da sauki sosai.
kinyi kyau sosai kamar wata yer larabawa.
kaima haka yanxu dai tashi muje.
Ya tashi yana a gaba tana binsa a baya har suka iso parlor.
Nan suka tadda hajiya tare da wani mutum suna magana.
Suna qarasa maganar mutumin yaficewarsa.
Sannan suka isa gunda take suka durkusa har qasa suka gaidata.Hajiya tace Allah yayi muku albarka yarana.
Yanxunnan nake cewa nakiraku ku karya sai gaku kun fito.Yanxu muje dinning muci abunci.
Dukansu suka tafi dinning inda munawwar ya sakawa mayiesha naman kaza da soyayyar doya da kwai da kuma sausage a plate.da kuma shayi.
Shikuma tea kawai yasha.
Suna qarewa hajiya tace gobe nakeso mukoma abuja.
Munawwar yace tunda wuri haka.
Tace ehh sbd achan ne gidan mayiesha yake nasiya muku gida wanda zaku koma chan da zama.Munawwar yace hajiya wai kina nufin wannan gidan wanda kika nunamun satinda yawuce.
Hajiya tace eh.
Munawwar yayi murmushi yace hajiya Allah ya biyaki da gidan aljannah
Dukansu sukace ameen.
Hajiya tace bayan haka kuma nasiyawa iyayenki gida anan yanxu haka sun koma achan da zama yau dinnan sannan nasamarwa mahaifinki aiki a wani company na dake garinnan.da kuma mota wacce zai dinga zuwa aiki.
Mayiesha nan take hawaye suka fara zubo mata tace ina matukar godiya a gareki hajiya bansan dame zan saka mikibah a duniyar nan.
Hajiya tace haba dai ai ke ba suruka ta bace kinkasance 'ya a gareni kuma kun chanchanci fiye da haka daga gareni sbd asana diyyar kune farin cikina yadawo gareni bayan shekaru dayawa.
Sannan kuma nan da wata daya inason naturaku london domin kuci gaba da karatunku achan sbd inason nayi saurin damka maka dukiyar mahaifinka kafin mahassada suyo chaa akanta.
Munawwar yace to shikenan hajiya Allah ya kaimu.
Tace ameen.
Yawwa mayiesha kitaso muje daki akwai abunda nakeso nabaki.
Munawwar yace haba hajiya kuma shine sai kunje daki.
Hajiya tace to ina ruwanka tsakanina da 'yata.
Yace to nayo shuru nidai idan kingama ina parlor ina jiranki.
Tace to.
Bayan sun shiga daki hajiya ta bude drawer dinta ta dauko wani yer qaramar jaka ta baiwa mayiesha tace gashi kyautace daga gareni.
Mayiesha ta durkusa har qasa tace nagode sosai hajiya.
Bakomai yanxu kitashi kije sai kibude a gaban mijinki sbd akwai inda nakeso naje.Mayiesha tace to Allah ya tsare hanya.
Ameen mayiesha.
Tana shiga parlor dinta da sallama munawwar yace yawwa gwara kizo kigwadamun a bunda hajiya ta baki.
Mayiesha tace to ina ruwanka da kayana.
Ya tashi yaje gun inda take ya matso sosai jikinta yace mekika ce.
Tace bakomai
Yace ai nazata zaki maimaitane sai kiga abunda zanyi.
Tace nidai yanxu kaga ban san meye ma acikin jakarnan bah muje saimu gani.yace yawwa gwara da baki budebah.Bayan sun zauna sai mayiesha ta bude jakar ta dauko wani dan qaramin kwali ta budeshi.
Tace wow meye wannan abun.
Munawwar ya saki dariya yace wannan wayace.Mayiesha tace wannan wace irin wayace haka mai kyau sosai kamar madubi.
Munawwar yace iPhone 8 kenan.
Tace amma zaka koyamun yadda ake amfani da ita sbd nikam ban iyabah.
Yace ai dole na koya miki sbd kada ki dauki wannan qauyancin zuwa abuja.
Tace nadaiji.ta dauko dayan kwalin babba ta bude sai taga laptop ce mai matukar kyau.
Tace kaga wannan laptop ce
Yace to ya akayo kikasan wannan
Tace ai ina ganin irinta a office din principal dinmu.Munawwar yace kinga koni nan banida laptop amma kinga hajiya ta siya miki.
Mayiesha tace sbd tafi sona akanka shiyasa.
Yace oho dai ai bazanji haushibah yanxu dai bude wannan kwalim muga meye.
Ta dauko kwalin shima ta bude tace woww kaga wannan qatuwar wayace.
Munawwar yace wannan ita ake kira ipad amma fa tayi kyau sosai nima zan chanja tawa na siya irin taki.
Tace nikam wadanan abubuwan duka yaushe zankoya.
Yace a hankali duka zaki koya mana kuma kinga idan mukaje london duka zaki bukacesu sbd karatu.
Tace hakane
Munawwar yace gaskiya hajiya tanasonki sosai amma nima zanyi miki kyauta wadda tafi wadannan duka.
Tace ba wata kyauta wacce takai wadannan amma zamu gani ai.
Yace hakane kam suma cikin magana wayarsa tayi ruri yana dubawa yaga faisal ne.
Yana dauka faisal yace ango kenan ya amaryar taka.Munawwar yace gatanan lafiya qalau gobema zamu wuce abuja.
Faisal yacd haba dai kenan yakamata muzo yaj muci abuncin amarya kafin ta wuce.Munawwar yace ba wanda zai wahalarmum da amarya sbd haka idam ma zuwa zakayi kazo da abuncinka.
Faisal yace to shikenan zanxo sbd yakamata musan juna.
Munawwar yace nifa inada kishi ko ganinta banason kuyi amma tunda ka tilasta to wlhy kazo kaikadai.
Faisal yace angama sai kum ganni.sukayi sallama.Munawwar yace wai faisal zaixo ya ganki yanason musan juna kafin mutafi.
Tace ayyah ba damuwa sai yazo.
Yanxudai kitashi ki kwashe kayannan kikai daki.
By maryam ashutrah.
![](https://img.wattpad.com/cover/175608420-288-k615443.jpg)
YOU ARE READING
MAYIESHA
Short Storylabarine akan wata mace jaruma wacce kwasam bazato ba tsammani ta tsinci kanta a cikin wata duniya. Shin ta hadu da qaddarar tane kokuma mutuwarta. Kubiyoni domin jin yadda ta kasance