MAYIESHA PART 21

625 32 0
                                    

Tana shiga daki taji an rufe kofa tana juyowa sai taji anyi saurin rungumeta tace swt hrt ai saika tsoratani haka

Yace haba dai ai bansan matata da tsorobah sbd ita jarumace ya tallabeta zuwa gado yace ina bukatarki matata.

Bayan sun gama jin dadinsu sannan suka shiga toilet sukayi wanka sannan ta shiryashi yace  kinga lokaci ya kure bari nayi sauri naje nasan yanxu haka abokina yana jirana.

Allah yakiyaye mun kai mijina saika dawo

Yana saukowa qasa saiga nabila ta fito yana ganinta yayi kamar bai gantabah yafice warsa.

Tace kaidai akeji ta haura sama zuwa part dinshi tana shiga parlon tayi arba da mayiesha tafito sannan tace nabila harkin tashi dazu naje dubaki da muka dawo amma kina bacci

Tace ehh ban dade da tashibah.
Dama abu nakeso kibani
Tace to muzauna koh

Suna zaunawa sai tace dama kudinane sunyi qasa shine nakeso kibani kamar dubu hamsin zanyi wani abu.

Mayiesha tace nabila dubu hamsin fa kikace

Eh duhu hamsin kodai sunyi kadanne

Mayiesha tace a gaskiya banida dubu hamsin a hannuna amma kibari idan mai gidan ya dawo sai natambayeshi

Nabila tace haba taya kina zama a wannan gidan kice wai bakida dubu hamsin

Kinga nabila bazan yimiki qaryabah inada dubu ashirin idan zasu isheki saina baki idan kuma bazasu ishekibah saikibari haryadawo

Tace kidaukomun kawai zanyi maneji.

Mayiesha tatashk zuwa daki tana mamakin kome nabila zatayi da kudi haka.

Tana shiga daki sai nabila ta hango ipad din nabila a kan table tana charge taje kusa ta dauka tace tabdi ipad kuma ta apple amma fa ta burgeni.tana
Jin motsin mayiesha satayi sauri ta zauna

Gashi sai kiyi maneji

Nabila ta karba sannan tace waccan ipad din takice

Mayiesha tace ehh tawace

Nabila tace amma fah kinajin dadinki sosai wlhy amma idan ranki bazai bacibah inason ki aramun.

Mayiesha tace ba damuwa kidauka idan kin qare saiki mayarmun

Nabila ta dauki ipad din tana murmushi tace thanks sis tafice.

Wacece nabila?!

Nabila abdullahi yer uwace  ga mahaifin munawwar wato alhaji abdulhakeem wacce a gidansu aka sake mata da yawa sbd itace auta a dakinsu sannan kuma ummarta ta sake mata sosai hakan yasa takeyin abunda taga dama idan tace zataje makaranta saita biyewa qawayenta suje suyi tayin shaye shayensu hakan yana matukar batawa mahaifinta rai amma ita bata damubah kuma gashi ummanta ta daure mata akan komai bayan sunyi hutun makarantane tace zatazo abuja tayi hutu gun hajiya sbd tasamu damar yin abunda ranta keso wannan kenan.

Cigaban labari:

Da daddare kusan qarfe takwas da rabi nabila tatashi tayi shiga cikin wasu irin matsasun kaya masu bayyana rabin jikinta taci kwalliya sannan ta dauki makullin motanta takira aisha tace muhadu kawai a club.
Tafito parlour bakowa har zata fita sai mayiesha tafito kitchen ta ganta tace nabila ina zakije yanxu da daddare.

Nabila tace gidan qawata zanje

Amma ahaka zaki fita ko mayafi babu kuma ki kalli irin shigarda kikayifah

Kinga dan Allah kada ki matsamun kawai kiyi harkar gabanki saina dawo tafice.
Ana bude mata mota ta taka motar da gudu tafice.

Mayiesha tace ikon Allah wannan kuma wace irin macece haka Allah ya sawwaka ta zauna a parlor tana danne danne a wayanta.

Bayam minti ashirin sai taji horn din motar munawwar tayi saurim fitowa ta tarbeshi yace da fatan na tarar da matata lafiya qalau.

Tace ina cikin koshin lafia mijina suka fice zuwa parlor yace yunwa nakeji sosai muje naci abunci sbd kinsan bazan iya cin abuncin kowa sai naki.

Suna tsakar cin abunci yace ina nabila ko motsinta banaji

Mayiesha tace tafita

Tafita kuma cikin wannan daren ina taje

Wai taje gidan qawarta bazata dadebah zata dawo

Yace amma da daddrennan Allah yasa lafiya

To ameen.

Tana zaune da qawayenta sai masha'arsu sukeyi sunata rawa har kusan qarde goma da rabi aisha tace wannan wayar kuma a ina kika samu

Tace ta matar dan uwanane na karba.

Aisha tace amma fah tabirgeni sosai

Allah koh nima haka shiyasa ma nakeson idan nakoma nace mata kawai ta barmun ita.bari naje toilet nadawo.
Cikin tangadi da maye tashiga toilet ai kuwa tana shiha aisha tasaka hannu ta dauke ipad din ta boye a jakarta sannan tatashi taci gaba da rawa.

Munawwar da mayiesha suna kwance suna labari sai yace wai lafiya har yanxi nabila bata dawobah

Mayiesha tace haba aiba qaramar yarinya bace da zata bata nasan duk inda take yanxu tana hanyar dawowa gida
Kodai zaka kira wayar tane

Noo banda numba dinta fah
Yawwa ki daukomun ipad dinki zan tura hotonta sbd inason akawomun irinta.

Tace ayyan aikuwa na arawa nabila ita dazu sbd tace wai zatayi amfani da ita

Taya zaki dauki abunki kibata kinsan me zatayi da ita

Haba dai ai bazatayi wani abu da bashida kyaubah yanxu dai kayi hakuri idan ta dawo saina karba bazan sake batabah

Yawwa baby na dadina dake idan nayi miki magana baki musamun.

Har kusan sha biyu  na dare sannan aisha tace yakamata fah nabila kije gida kinga nikam sai qarfe uku zankoma nida bashir.

Nabila tace to saida safe ta dauki jakarta cikin maye tashiga mota tana tafiya a hankali dakyar ta iso gida.

Ana bude mata ta shigo a lokacin su munawwar sukaji qarar shigowarta nan yayi saurin lekawa yaga itace sannan cikin fushi yafito zuwa qasa mayiesha ta biyo bayanshi.

Tana shigowa parlo tana tangadi tasamu guri ta zauna a lokacin ya sauko qasa.
Yace nabila daga ina kike

Ta kalleshi sannan tayi shuru batace komaibah

Yace tambayarki nakeyifah

Tace daga gidan qawata nan yayi saurin rufe hanci yace meye wannan kikasha mai wari haka.

Ba komai kawai lemu ne nasha

Yace nabila dama kina shan giya subhanallah

Mayiesha tace giya kuma haba dai taya zakace haka

Gashinan kinajin warinta amma wannan yarinyar kin cika  cikakkiyar yer iska to wlhy daga yau kin dena fita daga gidannan bani makullin motarki.

Meyasa zan baka makulli

Kibani kafin na kwasheki da mari ya dauki jakarta ua bude ya dauki makullin sannan yace ina ipad din mayiesha

Nabila tace tana ciki manah

Bata ciki kibani nace

Tana ciki mana ya wurga mata jakar yace gatanan ki daukomun.

Nan mayiesha tace dan Allah kabita a hankali mana zanyi mata magana gobe kaga yanxu ba'a hayyacinta takebah

Ta rike nabila takaita har daki ta kwantar da ita sannan tafito.

By maryam ashutrah.

MAYIESHA Where stories live. Discover now