MAYIESHA PART 26

615 28 0
                                    

Qarfe biyu dai dai suka isa garin katsina inda daga nan suka zarce zuwa gidansu mayiesha.

Suka tarar da mutane dayawa anata karban gaisuwa abba yana ganinsu yace sushiga cikin gida.bayan sun zauna sannan hajiya tayi mishi ta'aziya Mayiesha dai sai faman kuka takeyi.
Abba yace kiyi hakuri Mayiesha kowa zai mutu yanxu hakuri kawai za'ayi dakuma yi mata adduah.

Bayan kwana uku angama karban gaisuwa sannan suka sanar da abba akan Mayiesha tana da ciki yayi farin ciki sosai sannan yayi adduar Allah ya sauketa lafiya.

Hajiya tace amma mezai hana mukoma dakai chan abuja idan yaso saika zauna tare damu.
Abba yace a'a kawai kubanni anan sbd nafison zama anan tare da mutanena.

Hajiya tace to amma ai zama a haka kuma cikim kadaici ba dadi.
Yace hakane amma hakurine kawai nawa.

Tace to Allah yaji qanta da rahama.

Mayiesha na zaune a parlor tana cin abunci munawwar yashigo yana ganinta yace waton kinanan kina aikinki nacin abunci.

Tayi dariya tace idan kuma bancibah saika fara cewa banason cin abunci.

No bahaka nake nufibah amma fa naji dadi sosai dana ganki yau kin zake kina cin abunci kuma gashi har dariya kikeyi

Zaka fara zolayar taka kenan koh

Amma ai gsky na fada to amma yakamata muwuce abuja banda gobe sbd kinsan za'a fara exams

Hakane gsky amma kasan meye

Saikin fada
Wlhy banason mubar abba anan shikadai

To kinsan amma idan yayi magana baya chanjawa kuma yace shidai abarshi anan kawai.

To Allah yasa hakan yafi alhairi

To ameen.
Ranar jumuah suka dawo abuja inda suka koma makaranta ranar litinin.

MAYIESHA Where stories live. Discover now