MAYIESHA PART 9

818 45 0
                                        

Sunata tafiya sama cikin gajimare cikin farin ciki dajin dadi.
Haka kuwa suna isowa sannan sai kawai sukaga sun bace battt kafin su ankara sai gasu a filin makarantarsu mayiesha.

Mayiesha ta kalli munawwar cikin farin ciki ta rungumeshi.

Tace mu godewa Allah wanda da taimakon sane muka samu dawowa zuwa wannan duniyar tamu.

Taja hannunsa tace kayi sauri muje gida sbd banason kowa ya ganmu.

Shikam munawwar yayi shuru yakasa cewa komai.

Haka ta rufe fuskarta sbd kada a ganeta har saida suka isa kofar gidan sannan ta kwankwasa.

Umma kuwa na daki zaune tayi tagumi tanata tunane tunane sai taji anata kwankwasa gida.
Ta zata abban mayisha ne yadawo.

Tatashi sannan taje gun kofar tana budewa sai taga mayiesha nan take cikin farin ciki mayiesha ta rungume ummanta har da zubar da hawaye.

Umma cikin mamaki da kewar yer tata ta kalleta cikin hawaye tace mayiesha ina kika shiga  kika dauki tsawon wannan lokacin baki dawo gidabah.

Mayisha tace umma yanxu dai mushiga cikin gida.

Ta kalli munawwar tace shigo.

Suna shiga cikin gida suka wuce  parlor suna zaunawa sai umma ta kalli munawwar tace mayiesha wannan kuma waye.

Mayiesha tayi murmushi tace umma zanyi miki bayanin komai amma dai yanxu kibari mudan huta tukunna.

Sai umma tace to shikenan ki kaishi dakinki ya huta kekuma sai kije dakina nikuma bari na hada muku abunci sannan kuma nakira abbanki.

Tace to ummata.

Munawwar  yabi bayan mayiesha yana ta kallon irin gidanda suke rayuwa.

Suna shiga daki tace yanxu kashiga ga bayi nan bari na kawo maka ruwa sai kayi wanka.

Yayi murmushi sannan yace to mayiesha.

Bayan ta kawo mishi ruwa ya shiga yayi wanka yana fitowa ya shafa inwak dinsa saiga tufafi masu kyau a jikinsa.
Yana gama shiryawa.

Ya zauna akan katifar dakin yana kallon dakin yace Allah mai iko dama a irin wannan rayuwar mayiesha take zaune.

Amma kwata kwata idan mutum ya ganta zai zata daga gidan hutu take kuma yer masu kudi ce.

Tana fitowa wanka ta shafa mai a jikinta sannan ta saka hijab zuwa dakinta.

Tana shiga sai taga munawwar a zaune sai tunane tunane yake tayi.
Tashiga da sallama sannan tace nazo zan dauki kayanane.

Tana daukar tufafinta zata fita dakin saita kalli munawwar tace lafiya dai naganka a haka tunda muka iso baka ce komaibah.

Yace ba haka bane kawai gajiyace tamun yawa

Tace to kadan kwanta ka huta kafin abba ya dawo sai a zauna asan yadda za'ayi kakoma gidanku.

Yatashi yaxo gunda take yace mayiesha banason naje na barki a wannan halin.

Cikin mamaki tace wani hali kenan.

Ya kalleta sannan yayi shuru kadan yace ba komai.

Tace to bari nayi sauri naje na shirya.

Tafice tana zuwa ta shirya sai tafito ta taya ummanta girki.

Suna gamawa saiga abba yadawo daga kasuwa.
Cikin zumudin ganin mayiesha ya daga hannu sama yayiwa Allah godiya  yana shiga parlor ita kuma tana fitowa daga kitchen cikin jin dadi mayiesha ta rungume abbanta.

Cikin farin ciki abba ya kalleta yace mayiesha ke nake gani a idona

Tace abba nice mayiesha ce.

Yace mayiesha ina kika tafi kika barmu nida ummanki cikin kadaici.

Tace yanxu dai abba ka zauna zan baka labarin komai amma kafinnan ina zuwa.

Tatafi dakinta ta kira munawwar suka fito tare.

Munawwar yana isowa parlor ya durkusa qasa ya gaida abba.

Cikin mamaki abba ya amsa.

Sannan munawwar ya zauna.

Abba yace da mayiesha waye kuma wannan

Mayiesha tace abba zan baka labarin komai amma dai yanxu muci abunci.

Umma tana gama hada abuncin ta kawo parlor suka zauna dukansu sunacin abuncin.

Suna gamawa sai mayiesha ta kwashe labarin komai ta fadamusu.

Abba ya kalleta yace wannan labarin naku kamar tatsuniya umma tace a gsky nikam  ko a cikin tatsuniyoyin da nakeji ba kamar wannan sai dukansu sukayi dariya.

Abba ya kalli munawwar yace yanxu inshallah zansan yadda za'ayi kakoma gida idan naje kasuwa gobe zanyiwa aminina magana saiya nemomun inda mahaifanka suka da zama.

Munawwar yace to abba na gode.

Sai abba ya kallesu sannan yace yanxu bari naje na sanar da malam abbas cewa sun dawo.

Sai mayiesha ta kalle abba tace amma abba meye fa'idan yin hakan

Abba yace mayiesha tunda kika bata malam abbas ne yaketa kwantar mana hankali akan zaki dawo sannan kuma yana tayamu da adduah.

Tace to shikenan abba.

Abba yana isa gidan malam sai yake tarar dashi zaije masallaci bayan sun gaisane yake sanar dashi cewa mayisha ta dawo.

Cikin farin ciki malam yace to yanxu kaga masallaci zanje idan mukayi sallah sai muwuce chan gidan naka.

Abba yace to shikenan

Bayan sunyi sallah sai suka wuce.
Suna shiga cikin gidan mayisha na ganinshi sai kawai ta bata fuska sannan ta gaidashi ciki ciki.

Suna zaunawa dukansu sai malam abbas ya kalli munawwar sannan ya kalli mayiesha sai ya lura da abunda ke hannunsu.

Malam abbas ya kalli munawwar yace sannu dan saurayi wannan abun dake hannunwanku  kaida mayiesha menene.

Munawwar ya kalli inwak dinshi sai yace qarfen tsafi ne.

Malam yace karfen tsafi fa kace.
Munawwar yace eh.

Sai malam abbas ya kalli abba sannan yace mudan fita waje akwai maganarda zamuyi.

Bayan sun fito sai malam ya kalli abba yace wannan qarfen tsafin da kake gani dole fa a rabasu dashi sbd idan ba hakabah aljannu bazasu taba barinsubah.
Dole sai an salwantar dashi.

Sai abba yace to amma kasan idan ita mayiesha zatayi saurin yarda ta bada nata munawwar ba lallai ya yardabah sbd ya saba da abunshi.

Malam yace hakane gsky amma yanxu abunda za'ayi shine zan san yadda zan fahimtar dashi.

Bayan sun koma parlor sai malam abbas ya kalli munawwar yace malam munawwar nasan tabbas bakason komawa duniyarda kafito ko ba gaskiyabah.

Munawwar ya kalleshi sai yace eh tabbas hakane.

Sai malam yace to hanya dayace za'abi da zaihana kakoma idan kuma kaki ka amince to tabbas nasan bada dadewabah komawa zakayi.

Munawwar cikin tashin hankali yace wace hanya kenan

Malam yace ta hanyar salwantar da wannan abun dayake hannunku.

Munawwar ya kalli mayiesha itama ta kalleshi.

By maryam ashutrah

MAYIESHA Onde histórias criam vida. Descubra agora