Umma tace aure kuma
Ai ba soyayya a tsakaninsu.Hajiya salamatu tace ai nikam bama aure nakeso yayi yanxu bah sbd inason yayi karatu.
Abna yace ehj hajiya hakane karatun yana da matukar muhimmanci amma kuma namiji idan yakai irin wadannan shekarun anason ayi mishi aure sbd samun nutsuwar zuciya.
Tace hakane kan amma zanyi shawara.
Yace to badamuwa yanxu bari nakira miki shi.
Tana shiga dakin ta yaddata a kan gado tana kuka yace haba mayiesha bafa mutuwa zanyibah meyasa zaki tada hankalinki.
Tace yayana nasaba dakai bacci kawai yake shiga tsakaninmu banason kayi nisa dani dan Allah kada kaje ka barni.Yacs kinga mayiesha yakamata naje sbd yanxu dole na zauna tare da ummata sbd mufara shakuwa sannan mu fahimci juna amma nayi miki alkawarin zan dinga xuwa ina ganinki.
Suna cikin hakane sai abba yashigo da sallama munawwar ya kalleshi yace yawwa abba dan Allah ka fahimtar da mayiesha.
Abba yace mayiesha kiyi hakuri ai bawai bazan dinga zuws yana ganinki bane kinji.
Tacw to ka dauki alkawari.Munawwar yace nayi miki alkawari.
Tace to muje na shirya maka kayanka.Abba yace idan kun qare kufito da wuri.suna shiga dakin ya kwashe dukkan kyansa tasaka mishi a gana must go.
Ta dauka shikuma yana biye da ita a baya.
Suna fitowa hajiya dukansu suka tashi tace to mukam zamu tafik kuma inshallah Allah zamu dinga kawo muku ziyara akai akai.ta bude jakarta ta dauko dubu dari biyu ta mikawa abba.
Tace gashi ayi cefane.
Abba yace ai abunda mukayiwa munawwar sbd musamu lada mukayi bawai sbd musamu sakayya daga gunkubah hajiya.Tace tabbas hakane kuma nima bawai sbd hakan na baku kudinnan bah dan Allah ku karba.kuma ba kyau baida hannun kyauta baya.
Abba ya karba sannan dukansu sukayi godiya.
Suka rakasu har bakin mota suna shiga sai munawwar ya kalli umma yace nagode miki sosai da irin kula dani da kikayi Allah yabiyaki da gidan Aljanna kaima abba haka.
Yace ba komai munawwar kuma dan Allah kamar yadda nasanka da amana da kuma tarbiyya dan Allah kaje da wadannan kyawawan halayen naka a ko ina.tabbas mutane zasu sokaYace nagode abba.
Ya kalli mayiesha yace nagode miki yer qanwata da kulawarki.
Yashiga mota yana hawaye.
Suna daukar hanya sai hajiya tace munawwar wadannan kayan naka idan muka isa gida zan baiwa mai gadi su yaci gaba da sakawa yanxu zamu biya dakai boutique ka siyo kaya iya wadanda kakeso sannan kuma muje supermarket kasiyo duk abunda kake bukata.
Yace to ummata nagode.
Tace haba godiyarme kakemun kada ka sake godemun sbd na maka wani abu.
Bayan sunje boutique da supermarket sun siyo duk abunda zai bukata sannan suka fice zuwa gida.
Nana aka bude musu gate suka shiga wani irin katafaren gida na gani na fada.wanda kallo daya zaka masa kasan lallai mutanen cikinsa attajirai ne
Suna parking din mota suka fito sannan yace akwai abunda nakeso naduba cikin kayana idan na dauka saina kawo wa mai gadi.
Umma tace to badamuwa my son.Suna shiga cikin parlor munawwar yadinga bin ko ina da kallo sbd babban parlor ne sosai gashi anzuba mishi dukiya ta ko ina sai sheki da kamshi mai dadi ke tashi.
Yana zaunawa sai hajiya salamatu tace wannan shine gidan mahaifinka dake wannan garin na katsina.
Yanxu muje na nuna maka part dinka.
Sannan kuma dan Allah kasaki jikinka kayi duk abunda kakeso sbd wannan gidankane.Yace to umma ta.
Tana tafe yana binta a baya suka isa wani bangare na gidan.
Tana bude kofar suka shiga wani parlor hadadde wanda idan akace za'a fadi irin kyansa zai dauki lokaci.Tace wannan shine parlour dinka sannan kuma ga dakinka a chan.zansaka a kawo maka kayanka kuma masu aiki zasuxo su gyara maka komai sannan idan akwai wani abu wanda baiyi makabah ka sanar dani sai a chanja maka.
Yace to ummata tace ta huta sosai taficewarta.
Munawwar ya dinga bin ko ina da kallo sannan ya shiga dakinsa mai matukar kyau gashi babba sannan ga wani irin hadadden gadi a ciki ga sanyi ta ko ina.
Ya shiga toilet yayi alwala yayi sallah sannan dinga godewa Allah daya sadashi da mahaifiyarsa.Yana cikin hakan wayarsa tayi qara yana dubawa sai yaga mayiesha ce.
Ya dauka tace dafatan kun isa gida lafia yace lafiya qalau mayiesha da fatan kinci abunci.Tace eh yanxu muka gama cin dambu nida umma.
Yace to yayi kyau nima yanxu zanje naci abunci saina kiraki.
Tace to shikenan kakula da kanka.yace kema haka sukayi sallama yakashe.
Yana fitowa parlor ya tadda masu aiki suka gaidashi sannan sukace sunason sushiga dakinshi domin su jera mishi kayansa yayi musu izini sannan suka shiga.
Yana fitowa babban parlor ya tadda hajiya zinaru.
Ya durkusa har qasa ya gaidata sannan yake tambayarta ina umma.
Tace tana dakinta ta nuna mishi dakin.Ya shiga dakin tarw da sallama ta taddata tana sallah.
Yasamu guri yazauna tana gamawa ya gaidata ta amsa cikin jin dadi.Sannan tace munawwar dama inason idan kadan kwana biyu anan na maidaka makaranta kaci gaba da karatu.idan kuma qasar waje kakeso to duk wannan ba maj wahala bane.
Sannan bayan haka inason idan kagama karatu na damka maka duk dukiyar mahaifinka kaci gaba da juyawa sbd nikam kaga shekaruna karawa suke tayi.kuna qarfina yana ragewa.
Yacd hakane umma nima inason naci gaba da karatu amma banason nayi nisa da mayiesha.
Tace yawwa dama akan ita mayiesha din na yanke shawarar zaka aure ta sbd shakuwar dake tsakaninku kuma naga yarintace mai hankali kuma kaima kaga kakai munzalin yin aure.
Yace umma taya zan auri mayiesha bayan ba soyayya a tsakaninmu kuma nikam a matsayin qauna ta na dauketa.
Tace ai idanma kunyi aure zaka iya zama da ita a matsayin qanwarka kuma matarka.Yace to shikenan umma banason nakiyi miki biyayya akan koma idan har mayiesha ta amince nima na amince.tace
Yawwa Allah yayi maka albarka.Yace ameen.
Tace nasan kanajin yunwa muje muci abunci.
Suka tashi zuwa dinning table.
Suna gama cin abunci sai hajiya zinari tace amma hajiya yakamata nakoma abuja gobe sbd yarana zasu dawo daga dubai jibi.
Hajiya salamatu tace hakane kam gaskiya Allah ya kaimu.
Tace bari naje na fara shirye shirye.
Tace to idan nagama da munawwar zanxo nasameki.
Tace to shikenan ta tashi zuwa dakinta.
By maryam ashutrah
KAMU SEDANG MEMBACA
MAYIESHA
Cerita Pendeklabarine akan wata mace jaruma wacce kwasam bazato ba tsammani ta tsinci kanta a cikin wata duniya. Shin ta hadu da qaddarar tane kokuma mutuwarta. Kubiyoni domin jin yadda ta kasance