[10/10, 14:59] Anty Nice: *BADARIYAH*
*PAGE* 1⃣
Ni Badariyah Ibrahim haifaffiyar garin bauchi ce cikin karamar hukumar ganjuwa cikin kafin madaki, mahafina Abba Ibrahim a kafin madaki aka haifeshi, su uku iyayensu suka haifah, mahaifina shine da na farko a wurin malam mustapha Abba bafulatanine na asalin garin kafin madaki, bayan an haifeshi ne, da shekara biyar aka haifi gaggo Ai, bayan shekara uku kuma aka haifi goggo Fatima.
Abba nah yakasance farine kyakyawan bafulatani amma Allah yayishi mai yawan shiru, iyakacin Abba nah primary, SBD rashin kudi na mahaifin su bai samu yacigaba da Karatuba, akwai abokinshi Abdullahi dan makotansu ne shiyasamu ya cigaba da karatunshi na sakandare, kakana malam mustapha mota yake ja, kuma mahaifina wani lokacin yafi zama a shagon wani tela yana mishi yaron shago.
Mahaifina bayida wani buri irin yaga yayi karatu amma Allah bai yaddah ba, lokacin da abokinshi Abdullahi yagama sch sai bappan shi ya daukeshi suka koma bch yasaka shi a makaranta, yana diploman shi a bacas, a lokacin Abba na yadage da koyan dinkinshi inda ya saka goggo Aisha da goggo Fatima a makaranta, xuwa lokacin goggo Aisha tana aji daya a secondary ita kuma goggo Fatima tana aji hudu a primary.
Mahaifiyar su Abba nah mai suna zainabu amma suna kiranta ummah itama bafulatana ce kyakyawar gaske amma ita ba fara bace bakace saidai amma bakinta mai kyau ne gata bata cika tsawo dayawa ba, duk da rayuwar kauye ce amma kana ganinta xaka ga asalin kyau da diri irin na 'ya mace, gata da gashi mai duhu ga tsawo ga cika, kuma dukkan sajenta gashi ne gashi har goshinta, idan ka kalli bayan wuyanta shima duk suma ne, gashi akwaita da hakuri da rashin magana Wanda a wurinta mahaifina ya dauki shirunta da HAKURI.
Duk cikin yaran gidansu babu wacce tayi kyaun umma da kalanta duk farin mahaifinsu suka dauko da tsayinshi.
Lokacin da abokin Abba nah yagama karatun shi, sai bappanshi yasama mishi aiki a PRIMARY EDUCATION BOARD, inda bappanshi yake aiki a natsayin chairman na wurin ba bata lokaci Abdullahi ya tattara yanashi yanashi ya koma bauchi gaba daya, xuwa wannan lokacin goggo Aisha tana aji hudu a secondary, lokacin kuma Abba Abdullahi ya bijiro da maganan yana son autenta, amma malam mustapha Wanda suke kiranshi da bappah yace yayi hakuri ta kammalah karatunta, amma Abban bauchi yaki amincewa yanemi alfarmar amusu baiko hankalinshi zaifi kwanciya, haka bappah yayi badon yasoba, don shima burin shi kenan yaga sunyi karatu mai zurfi amma idan iya secondary ne ma tasamu ta kammalah.
Bayan shekara biyu lokacin anyi bikin Abban bauchi da goggo sun tattara sun koma bauchi inda suka zauna a fadaman mada kusa da gidan bappan Abban bch, bayan wani lokaci Abban bch yanemawa Abba nah shago a kasuwar winti wurin nuhu tela dayake shine telan matan bappanshi, ba a dauki lokaciba Abba na ya kware da dinki kaman yayi shekaru a wurin tunin ya tara customers, amma bai yadda ya zauna a gidan abban bch ba sai Yakama haya a cikin unguwar gwallaga sbd yafi mishi kusa da winti.
Bayan shekara daya goggon bch ta haihu inda tasamo danta namiji mai tsananin kama da abban bch saidai yayi farin goggon bch, bayan suna yaro yaci suna Aliyu, sunan mahaifin Abban bch amma ana kiran shi haidar, akwana a tashi yau har goggo Fatima tagama sch inda ta taho bch don tasamu admission a school of nursing bauchi ba bata lokaci ta tattaro tadawo, amma a cikin sch taxauna cewar bappah dayace hankalin shi zaifi kwanciya akan ace ta tare gaba daya gidan addanta saidai karshen sati ta dinga zuwa musu.
Abba na alokacin ya fito damagana auren shi da 'yar kawunshi yayan umman shi mai suna Halimah Wanda muke kiranta ummi, ba a dau lokaciba akayi bikin amma yabarta a can kafin madaki bayan sati yake zuwa mata kafin yasamu gida, don baya son gidan haya mai mutane dayawa,.
Alokacin kuma goggo Aisha tasake haihuwar danta na biyu Wanda yaci sunan Abba nah, Wanda ranan sunan aka saka mishi Ibrahim Khalil, bayan sunan Khalil da sati biyu Abba nah yasamu gida a cikin gwallaga, gidane mai dakuna biyu a Jere sai kitchen da toilet kawai sai filin tsakar gida mai Dan fili kadan, dayake ummin mu mai tsafta ce sai yaxama gidan ko kai waye kashiga saikayi shaawar shi.
YOU ARE READING
BADARIYYA Completed {03/2020}.
RandomLabari mai ƙayatarwa,nishaɗantarwa yare da faɗakarwa.