53-54

1.3K 77 10
                                    

*BADARIYA*
*1441H/2019M.*

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga kinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar rayuwar duniya da lahira.}_

       🎐G•W•A🎐
_*GASKIYA DOKIN ƘARFE•* 🏇🏻_

Story and written
           By
*AUNTY NICE*

*_WANNAN BOOK SADAUKARWA NE ZUWA GAREKI MISS XERKS._*

~Wattpad@GaskiyaWritersAsso.~

*page* 53---54

*__________* 📖Ranan ko kitchen ban bi Aunty don tayata ba, daga ita sai masu mata aiki suka haɗa break-fast, ina ganinta gudu-gudu ta shigo ta wuce toilet bata kula ni ba.

Tana fitowa a wanka har lokacin bakina a zunɓure ina ta binta da kallo kaman zanyi kuka.

Juyowa tayi ta kalleni ta taɓe baki tace, "kina da aiki Riyyah idan tsakaninki da mijin ki bazaki iya gaya mishi magana ba sai wani ya shigo? Toh wallahi sirrinki zai zama a waje" ta cigaba da shirinta bata kalleni ba kuma.

Haka na shige toilet ɗin nayi wanka na fito ita kuma tana saka uniform ɗinta don tafiya office, kallonta nayi nace.

"Aunty na ƙira shi a waya idan ya yarda na biki ki ajiye ni"?

"duk wanda ya miki" ta faɗa fuskanta babu walwala ta quce ta bar ɗakin.

Jikina naji yayi sanyi, matar nan tana iya ƙoƙarinta akaina don taga ta sama mun ƴanci amma ni kuma ina neman watsa mata ƙasa a ido, ni bata san na tsokano Hammah bane kuma ina tsoron haɗuwan mu da shi.

Wani dogon riga na lace na ɗauko nasaka, na fita zuwa palon, akan dinning na samu Aunty da Baba suna break kuwa cikin sauri yake, har ƙasa na tsuguna na gaishe da Baba sannan na miƙe na koma ɗakin.

Aunty ce ta buɗe ɗakin ta shigo tana kallona tace, "kin tambaye shin ne"?

"Aunty kiyi haƙuri naga kaman na ɓata miki raine, ban tambaye shi ba, zan jira idan ya shigo sai na tambaye shi".

Murmushi tayi tace "ba komai ƙirashin kawai, duk yadda yace sai ki sameni a parlo ko", ta juya ta fita bayan ta ɗauki handbag ɗinta.

Jiki na a sanyaye na kira number shi, amma har saida ya gama ringing bai ɗauka ba, zuciyana ya fara bugawa kodai yayi fushi ne? Kawai sai naji ya biyoni da ƙiran.

Da sauri na ɗauka ina sallama, shima daga ɗayan side ɗin ya amsa mun, sannan kowan mu yayi shiru, "wani abu kike so ne"? Naji ya tambayeni.

Cikin muryan tsoro tsoro nace dama zanbi Aunty ne ta sauƙe ni a gidan Adda Umaima ta haihu ne".

"Yayi safiya kije gidan mutane, ki bari idan na tashi zuwa 11:00 zan kaiki, Allah ya raya mata abinda ta haifah cikin musulunci", ko jiran mai zance baiyi ba ya kashe wayan.

Kallo na bi wayan da shi cikin ɓacin rai naji haushin abinda ya mun, nace "lallai ma Hammah nan don ba so na yakeyi ba ko? Yanzu da Besty nane da gudu-gudu zai yadda baya son abinda zai ɓata mun rai, amma ji wannan mutumin hmmm zan rama kuwa" na faɗa ina komawa na kwanta.

Aunty na shigowa cikin sauri tace, "ke nake jira fa" ina turo bakina nace, "bayan yaƙi, wai sai ya tashi wurin 11 zai kaini" dariya tayi tace "hakan ma yana da kyau, sai ki kula da kanki ki fita kuma kiyi break, sai na dawo" ta faɗa tana fita.

Komawa nayi na kwanta na ɗauki wayana, whatsapp na buɗe najira zuwa wani lokaci message suka gama buɗewa.

Da sauri na duba status ɗin Besty Feenah saiga photon babyn kuwa yadda nayi zato, "Masha Allah" na faɗa don kyaun baby da girman shi, tura mata nayi sannan na sauƙa ina bin chtt ɗin mutane ina karantawa ina reply.

BADARIYYA Completed {03/2020}.Where stories live. Discover now