61-62

1.4K 76 1
                                    

*BADARIYA*
*1441H/2020M.*


®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga kinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar rayuwar duniya da lahira.}_

       🎐G•W•A🎐
_*GASKIYA DOKIN ƘARFE•* 🏇🏻_

Story and written
           By
*AUNTY NICE*

*_WANNAN BOOK SADAUKARWA NE ZUWA GAREKI MISS XERKS._*

~Wattpad@GaskiyaWritersAsso.~

*page* 61---62

*____________*📖 Har nayi niyyan murɗa key ɗin kuma sai wata zuciyar ta haneni, komawa da baya nayi ina kallon ƙofan nace, "Hammah kayi haƙuri tsoro nakeji, kuma yanzu Aunty zata dawo fah", na faɗa ina wucewa kan gadon.

Ƙwafah yayi yace, "zamu haɗu ne yarinya sai kin eaina kanki, zaki san da soja kike wasan", sannan ya faɗa da karfi don naji, "ki tabbatar kin haɗa mun dinner".

Saida naji ƙaran motan Aunty tukun na buɗe ƙofan da sauri nayi hanyar kitchen, ina ji ta shigo ni kuma da sauri na fito daga kitchen ɗin na iso wurinta ina mata sannu da dawowa.

"Mekike girkawa banji ƙamshin komai ba"?  Ta faɗa tana bina da kallo.  Turo baki gaba nayi ina cewa, "Aunty nifa nakasa sanin abinda zanyi ne, shiyasa najira ki dawo".

"amma Riyyah tunaninki kaɗan ne, ta yayah ma zaki zauna zaman jiran saina dawo? Idan kuma nayi dare fah? Don Allah tashi ki wuce kisan me zaki dafa, ae nagaya miki abin da yafu so".

Dama abinda nake nema tamun kenan, don bana so ta gane a shiriritana na ɓata lokacin, kitchen na wuce na fitar da kifi guda uku manya, wanke su nayi na gƴara, don ina son nayi irin gashin *(Maman hazeek*) don ya mun daɗi babu karya.

Gwaten dankali nayi wanda yasha vegetables sosai, sannan na gasa kifin, na haɗa mishi ginger kuma wanda yasha pineapple a ciki.

Ina gama aka ƙiea sallan isha, da sauri na fitar mishi zuwa parlon Baba don nasan Baba yau yana side ɗin Mama ne, sannan na wuce ɗaki donyin sallah.

Da ƙyar na nutsu na shiryah lokacin da Khalifah yazo yace mun Hammah ya shigo, wai naje nayi saving ɗinshi inji Aunty, haka na fito badon raina yaso ba.

A hankali na karasa wurin dinning ɗin inda shima lokacin ya kariso ya zauna, dai-dai zai zauna ya saka ƙafan shi ya taka nawa sannan ya murtsuka don mugunta.

Da sauri na matsa ina faɗin "washhhh Allah Hammah me na maka kuma"?

Ko kallona baiyi ba ya ja sit ya zauna, turo baki nayi inata ƙananun mita na, tukun na zuba mishi dankalin kaɗan a cikin wani pilet mai kyau, sannan na ɗauka kifin da yaje naɗe a cikin poil paper na ɗaura akan ɗatan pilet ɗin, sannan na ɗaura fork akai, gefe naja kujera na zauna ina hararan gefe ina ƙunƙunin takani da yayi

Ko ɗaga kai baiyi ba ya kalle ni, abincin shi kawai yake ci babu wani damuwa a tattare da shi ko kaɗan.

Yana gamawa yaja kujeran ya miƙe ba tare da ya kalli inda nake ba ya bar wurin, da ido na bishi cikin mamaki ina buɗe baki.

Har gefen kujeran da Aunty take yajw gefe yaɗan zauna, yan mata magana wanda ni tsabar ɓacin rai ban ko ji me yake cewa ba, daga baya ya tashi bayan ya mata sallama ya fita a parlon, ko juyowa baiyi ba ballantana ya kalle inda nake.

Yana fita su Gidaɗo da Aunty suka zo kan dinning ɗin Aunty tana cewa, "gara muma muyi dinner ɗin don duk ƙamshi yagama cika mun ciki tun Hammanku yana ci".

Kowan mu zama yayi mukayi dinner a tare, gefe ɗaya zuciyata sai ta fasa ta keyi da abinda Hammah ya mun, wato gani ƴar iska na mishi girki shi kuma yaci ya tafi gurin wanda yasan darajanta sama da ni ko"? Na faɗa kaman zan fasa kuka a zaune a wurin, kawai daurewa nakeyi don kar su gane halin da nake ciki, har muka gama.

BADARIYYA Completed {03/2020}.Where stories live. Discover now