*BADARIYA*
*1441H/2019M.*®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga kinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar rayuwar duniya da lahira.}_🎐G•W•A🎐
_*GASKIYA DOKIN ƘARFE•* 🏇🏻_Story and written
By
*AUNTY NICE**_WANNAN BOOK SADAUKARWA NE ZUWA GAREKI MISS XERKS._*
~Wattpad@GaskiyaWritersAsso.~
{*_Aisha Usaman (mama Abdallah) na Miss Xeks Novella@, wannan shafi kyautace gareki, don ƙaunarki da books ɗinmu, Allah ya barmu tare._
*page* 38___39
*_________* 📖 Bani na farfaɗo ba har saida aka dawo daga kai Besty nerh! .
Tunda na buɗe ɗaki naga mata ƴan office ɗin su Aunty da ƴan uwan Baba daga jama'are cike a ɗakin Aunty nah wasu suna palo, sai na tabbatar wa raina lallai na rasa Besty har abada.
Babu wanda ya lura da kukan da nakeyi sai Adda Humairah a hankali ta dafah baya na itama tana kukan, Mummy ce ta matso kusa damu tana ta bamu haƙuri.
A can karshen gadon na hangi Aunty nah ta kudundune cikin hijabin ta tana ta kuka.
Gefe ɗaya kuma Umma ce zaune akan kujeran ɗakin, Goggo na gefenta kowansu zaune cikin alhinin wanna rashi da mukayi.
Tunda akayi rasuwan nan ban samu na leƙa koda palon Aunty ba, ballantana ya danganani da waje, don ko Baba har ɗakin Aunty ya shigo muka gaisa, yayita bani baki, har yana gaya mana rikecewan da Hammah Umar yayi, amma inda yake sun hana shi zuwa, saidai sun nemi alfarman tura matar shi ko hankalinshi zai kwanta.
Nidai babu abinda yake damu na kowani lokaci sai tunanin irin rayuwar da mukayi da Besty nerh!.
Hmmm ajiyan zuciya na sauƙe lokacin da muke cin abinci da su Adda hummy, duk da tunda muka faraci bai fi spoon uku na ciba, saidai inata juya spoon ɗin a cikin plet ɗin.
Kallona Adda Hummy ta tsayayi cike da tausayawa, domin tunda na saka abincin a baki na, nake ta sauke ajiyan zuciya.
"Riyyah don Allah kiyi haƙuri kici abincin nan mana, Babagana fa addu'an ki yake buƙata bawai kiyi ta kuka kina saka damuwa a ranki ba Riyyah ta!" Adda Hummy ta faɗa tana kallo na fuskanta ɗauke da tausayi nah.
Share hawaye nayi nace mata, "naji Adda insha Allahu zan daina kukan," na faɗa ina kan share hawayen.
Tunda akaje aka dawo daga kai Besty Baba yace ana sallan azahar a ɗaura auren su Besty da Fauzy, don bai yadda ace antara mutane kuma a haƙura da auren ba, mutuwa dai anriga da anyi shi, sai dai addu'an Allah ya jiƙanshi.
Haka akayi ana ɗaura auren aka saka kowani ango ya ɗauki amaryar shi, ba tare da anyi wani rakiyan amare ba.
Washe gari kuma saiga kowacce amaryah angonta ya kawo ta, ranan Besty tayi kuka kaman ranta zai bar ruhinta, nidai saidai binsu kawai nake da ido.
Bayan anyi sadakan uku kowa ya koma inda yake.
Washe garin bakwai ɗakin daga ni sai Aunty ina tayata muna gyaran ɗakin, sai jifa-jifah mata suna shigowa ƴan gaisuwa, har lokacin nakasa daina zubar da hawayen rashin Besty nerh!.
Aunty ko rana ɗaya bata taɓa ce mun uffan ba, koda zan zauna ina kukan, saidai itama ta nemi wuri ta zauna tayita kukan.
Muna cikin haka saiga Baba ya shigo har ɗakin Auntyn bayan shi kuma Gidaɗo ne, "haba Fatima mau zangani haka? Kinsa yarinya agaba kuna ta kuka, abinda ya kamata ke kibata hakuri amma saiki biyeta kuna kuka?Babagana ya riga ya barmu a yanzu tsakanin mu da shi fah addu'a yafi buƙata.
YOU ARE READING
BADARIYYA Completed {03/2020}.
RandomLabari mai ƙayatarwa,nishaɗantarwa yare da faɗakarwa.