*BADARIYA*
*1441H/2019M.*®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION* ✍🏻
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar rayuwar duniya da kuma lahira.}_'''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE🏇🏻_*Story and written
By
*AUNTY NICE* ✍🏻*WANNAN BOOK SADAUKARWA NE ZUWA GAREKI MISS XERKS.*
~Wattpad@GaskiyaWritersAsso.~
*PAGE* 32---33
*_________📖* Dariya nayi ina kaɗa kaina don jin abinda Besty ta faɗa, ina kallonta ina dariya nace, "kinsan dai yanzu yazama surukina saboda haka ki daina haɗani da shi, bakima lura da wani abu ba Besty".
na faɗa ina ƙara sautin dariya na.
Kallona ta tsaya yi, ina kan dariya na cigaba da ce mata, "ai idan kin lura da haɗuwar Hammah Umar sai kace Omer na film ɗin tarkon ƙauna, inaga baki taɓa lura da kamanin su ba ko?".
Tsalle ta daka ta faɗo kaina tana dariya, wanda har saida ta bani tsoro tace,
"Besty wallahi hakane, kullum saina yita tunanin da wa yake kama ashe ke kan kinsan kayanki, Besty har yanayin tsayin su, da ɗaure fuskansu iri ɗaya, sai yau na ƙara yadda, kai amma munyi missing wallahi".ta faɗa tana zunɓuro bakinta gaba.
Hararanta nayi nace, "mekike nufi da munyi missing? Besty na ma har ya fishi kyau, kawai tsayi zai nunawa Besty don wallahi kama sukeyi, Besty mai fara'a da son mutane ma".
na faɗa ina ture ta daga jikina.
Har ƙasa ta faɗo tana dariya tace, "gara ma na daina damuwa da kyaun su don babu wanda yafi Hamma Haidar ɗina".
ta faɗa tana juya ikebenta.
Haka muka yita muhawara kowa tana cewa nata yafi haɗuwa, har muka gama abinda zamuyi.
Tunda Besty ya koma kullum sai ya ƙira Mama amma bata ɗaukan wayan shi, haka babu yadda ya iya saidai ya tura mata text.
sukuma sauran gidajen kowa shirye-shirye ya keyi, amma gidan Mama babu abinda take shiryawa, saidai Baba ya sanar da Aunty Fanna akan ta tsaya akan komai.
Ranan da muka gama exams muka dawo gida, inda zamuyi hutun kusan wata uku, a lokacin kuma auren mu saura 3weeks.
Tunda muka dawo aka hanamu yawo, kusan kullum Aunty sai tazo gidanmu, ana tamana shiri kaman daga kanmu amare sun ƙare.
Mummy takanas ta ɗauko mana wata mata daga maiduguri wacce ake cemata Aunty Yagana tana ta mana gyaran amare.
Ga wani dilke da ake mana dama mun tare gidan Mummy ne aka ware mana ɗaki guda,nidai sai dare nake zuwa gidan mu na kwana wurin Ummi na.
Idan kunga jikina sai ka rantse da Allah irin matan baƙaƙen larabawan nan ne, domin wani colour nane ya ƙara fitowa yayi kyau, dama ga jikina duk gashi ne akwance, wanda suka ƙara maida jikina yayi kyau.
Kullum Besty ta kalleni sai tace, "kai Besty kina da wani irin fitinannen kyau, gaskiya Besty ya more, kinga yadda kika canja kuwa?".
nidai dariya kawai nake mata, don nasan babu ƙarya nayi kyau saida godiya wa Allah subahanahu wata'ala.
Ana saura sati ɗaya Adda Hummy da Adda Hafsat suka zo, wanda ko kaɗan bazaka ga Adda Hafsat kace cikinta ya shiga watan haihuwa ba, domin ya baje a jikinta ne, sai uban ɗuwaiwaya da tayi, amma kuma duk inda ta zauna da ƙyar take tashi.
YOU ARE READING
BADARIYYA Completed {03/2020}.
RandomLabari mai ƙayatarwa,nishaɗantarwa yare da faɗakarwa.