*BADARIYA*
☄®
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION*✍🏻
{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin riban duniya da kuma lahira.}🎐G•W•A🎐
*GASKIYA DOKIN ƘARFE*🏇Story and written
By
*AUNTY NICE*😘*WANNAN LITTAFI GABA ƊAYAN SHI SADAUKARWA NE GAREKI, MISS XERKS*
{WANNAN SHAFIN KYAUTACE GAREKU IYAYEN GIDA NA, ƳAR ƘAUYE, DA UMMU NABIL, ALLAH YA BIYAKU DA ƘOƘARIN DA KUKEYI A KAINA, NAGODE MUKU SOSAI.}
*PAGE* 16
Mun daɗe a haka kaman bazai sake magana ba, chan kuma sai naji yace "Beauty! Gobe in Allah ya kaimu zanje Lagos, akwai wani interview da zanyi, don Allah kimawa mijinki Addu'a".Ido na yana kanshi nace ,"insha Allahu zanyi, amma yaushe zaka dawo"?
Uhmmm kawai kimun addu'a, inaga zanyi sati ɗaya,.
Zuwa wani lokaci na raka shi har jikin motan shi, bayan yayi sallama wa Abba nah da Ummi nah, a jikin motan yake nuna mun motan da Baban shi ya canja mishi, bayan ya dawo, murna na mishi sannan mukayi sallama.
Tunda Besty na ya mun waya ya isa lafiya, bamu saake waya ba sai bayan sallan ishaa, inda yake sanar mun da gobe ƙarfe tara zasuyi.
Addu'a na mishi alƙawarin daren yau zan tashi nayi, yana wata irin dariyan daban gane kanta ba, yace "Beauty kinsan dariyan me nakeyi kuwa yanzu"?
Girgiza kaina nayi kaman yana ganina, sannan nace"sai ka faɗa my besty!"
Ɗan dariya yayi mai sauti sannan yace "ɗazu a airpot muka haɗu da Yusuf aminin Hammah Umar, shida matar shi, kinsan me yace"?
batare dana ce komai ba ya cigaba da dariyan shi yana mun bayani "tambayan farko ke yafara tambaya na, nace mishi ae an bani ke".
shine fah ya riƙe bakinshi yana mamaki, wai amma ya mun murna don samun first class mata irin ki sai antona, ga hipps ga komai, amma shi ya kwaso wata kamar walƙiya, bayan saida Hammah yagaya mishi qualities ɗin macan gaske, amma yayi taurin kai.
Kinsan abin dariyan? Nima dariyan nakeyi tun banji mai zaice ba, yana dariya yace "Beauty duk maganan da mukeyi fah matar tana gefen mu kaɗan, sai wani rausay takeyi kamar wata catoon".
Gaba ɗaya dariya muka kama yi da Besty, sannan nace "Besty baka tsoron nima rana ɗaya kawai na rame, na dawo kaman ita? na faɗa ina mishi dariyan ihun da yayi da ƙarfi".
Yana dariya yace "amma zan baki horo saboda tunanin da kikayi, wato fata ki keyi na shiga gararin damuwa ko? To ƙwalelenki, nan gani na bari, hakanan zakiga Beauty na ƴar duma-duma, ya faɗa yana mun dariya".
Besty yana son tsokana a rayuwar shi, ga baya fushi, sai dariya yake ta saka ni, har saida naji na sake da shi, sannan yace Beauty Hammah mabtausayin shi nakeyi, saboda idan kinga sirangalin Zainab kaman na catoon, gashi yana bala'in son mace ƴar duma-duma.
***************
Ranan da Besty zai dawo, yasaka ni dole naje gidan su wirin Auntƴ, wai dole sai ni zan mishi abincin taryan shi, babu ƴadda na iya tun safe nayiwa Ummi sallama, akan zanje gidan Aunty kuma sai gobe na dawo.
Ina zuwa mukayi karo da ɗan mujaheed ɗina zasu tafi sch, don sammako nayi zuwa gidan, dav sauri yakama hannu na, yana tambayana " Adda Riyyah anan zaki kwana?".
Amsa mishi nayi da ehh, sannan ya fita yana ta murna, shi kuma, Khalifah murmushi kawai yakeyi yana kallona, har yaje bakin ƙofa tukun yace "Adda ayiwa Hamma Babagana delicious, idan mun dawo zamu lasa, ya fita yana ɗan murmushi.
YOU ARE READING
BADARIYYA Completed {03/2020}.
RandomLabari mai ƙayatarwa,nishaɗantarwa yare da faɗakarwa.