*BADARIYA*
*1441H/2019M.*®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga kinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar rayuwar duniya da lahira.}_🎐G•W•A🎐
_*GASKIYA DOKIN ƘARFE•* 🏇🏻_Story and written
By
*AUNTY NICE**_WANNAN BOOK SADAUKARWA NE ZUWA GAREKI MISS XERKS._*
~Wattpad@GaskiyaWritersAsso.~
*page* 57---58
*____________*📖Ina shiga parlor naga babu kowa sosai naji hankali na ya kwanta, share hawayen fuskana nayi da sauri na wuce ɗayan ɗakin Auntyn.
Toilet na shige na wanke fuska nah, sannan na dawo ɗakin na shafah powder da ɗan kajal, na wuce ɗakin Aunty.
Aunty na kwance saman gadonta tana ta rubutu a wani takarda, gefenta kuma Mujaheed ne yake ta danna mata kafanta, kallona tayi ta maida kanta kan ɗan littafin tana cewa, "har kundawo ne? yayah mai jego da angon namu"?
Dariya nayi kaɗan na zauna akan stool ɗin dressing mirrow ina amsa mata da, "ango mijin ƴan mata yace agaisheki da kyau, har yabani goro yace na kaiwa Mummy" na faɗa ina jifan muja da gyale na.
"Babu wani Mummyn nan, dani yake auren bari kiga gobe naje zamu dai-dai ta kanmu"ta faɗa tana dariya, dai-dai lokacin kuma ta mike zaune tana duban abinda ya hana Mujaa yi mata matsan ƙafan.
Kallonshi tayi taga yana hararah nah kaman zaiyi kuka, kama haɓanta tayi tana cewa, "waya ta ɓa autan Baba da Aunty"?
Jijjiga kai yayi ya ɗauki gyalen dana jefe shi yace, "kuma na ƙwace gyalen ki" ya faɗa kaman zaiyi kuka, ni kan dariya nayi ina cewa, "ayyah Mujaheed am naga duk kayan ka sun koma gwanjo shiyasa na baka gyale nah ɗan kanti" tashi yayi yana kuka ya jeho mun gyalen yana "bana son kayan ki nima" yana kuka ya fita a ɗakin.
Aunty tana dariya tace, "gaskiya Riyyah kin ta kura auta na, shifah ya tsani maganan gwanjon nan, gani yake da gaske duk kayanshi gwanjon ne" ta faɗa dukkan mu muna dariyan.
Hira mukayi da Aunty har zuwa 10:00 da yake yau ba girkinta bane, saida mukayi hiran tukun na wuce ɗayan ɗakin, bayan nayi wanka na saka nighty nah sai tunanin Hammah na ya faɗo mun, ina tambayan kaina toh ni me na mishi yayi fushi yau? Haka dai nayita saƙa da warwara a raina har bacci ya ɗauke ni.
Da safe wajen karfe 9:30 wayan Besty Feenah ya tashe ni, a razane na ɗaukin wayan nakai kunne na, ihuu ta saka mun tana dariya tace mun "albishir besty" miƙewa nayi na zauna ina cewa "goro".
"Adda Hafsat ma ta haihu yanzu nan, an samu baby boy ita ma" bansan lokacin dana dirƙa daga kan bed ɗinba nace, "Alhamdulillahi Allah ya raya mana su da imani, ashe zamu zo kano ƙawata".
"wani irin ƙawa kuma? Na bar matsayin Bestyn kece yanzu"? Ta faɗa tana ɓata rai.
Dariya nayi mata sannan nace, "kinsan duk ranan da nace miki besty sai na tuna Besty Babagana araina, shiyasa ma na yankewa wa raina gara nace miki ƙawata, don ranan da kika kirani sai da naji faɗuwar gaba, shiyasa na maida sunanki akan phone ɗina da Kawata, ina fatan kin fahimce ni"?
Jiki a sanyaye tace, "na fahimce ƙawata, kuma na gode da tunatar dani da kikayi, don wallahi ranan saida Adda hummy ta faɗa, tace kullum taji nace basty saita tuna da Bestyn mu, Allah dai ya mishi rahma".
A hankali murya ƙasa-ƙasa na amsa mata da "Ameen", itama jin yanayin dana koma sai tayi saurin yimun sallama ta katse wayan, ta gumi nayi a zuciyata ina cewa "da yanzu besty ne miji na, da kowani irin rayuwa zamuyi"? Sai naji hawaye na biyo fuskana, ban ankara ba naji wani kuka yazo mun mai azaban ƙona zuciya, besty yana sona baya mun fushi, amma wannan kam baya sona shiyasa yake mun fushi.
YOU ARE READING
BADARIYYA Completed {03/2020}.
RandomLabari mai ƙayatarwa,nishaɗantarwa yare da faɗakarwa.