93-94

1.7K 85 20
                                    

*BADARIYYAH*
*1441H/2020M.*

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION*✍🏻
{ _Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar rayuwar duniya da lahira._ }

    🎐G•W•A🎐
*GASKIYA DOKIN ƘARFE*🏇🏻

Story and written
          By
*_AUNTY NICE_*

*_WANNAN BOOK ƊIN SADAUKARWA NE ZUWA GAREKI MISS XERKS._*

~Whatpad@GaskiyaWritersAsso.~

*page* 93--94

*___________*📖Yana shiga side ɗin Mama ya samu tana fitowa daga kitchen zata wuce ɗakinta, nuna ta yayi da yatsan shi yana zare ido yace.

"ki tattare kayanki na baki minti talatin ki bar mun gidana, tunda ban isa da ke ba, kinje kin zubar mun da mutuncina a idon mutane, kin ɓata rayuwar ƴaƴanki a idon duniya, yanzu a tunaninki akwai wanda zai so bawa sauran yaranki ƴa su aura? Babu wanda zai si haɗa zuriya da ke idan yasan ciwon kanki".

Nuna mata hanyar ɗakin yayi yana, "wuce mana kin tsaya kin zuba mun shegun idonki na rashin son zaman lafiya"

"Allah ya shiryeki Zahra tun da ƙuruciyar ki nake fama da ke, amma har yau baki gyara ba kuma baki duba mutuncinki dana iyayenki ballantana mijinki, saboda haka kafin kiyiwa ɗana baki ki fita ki bar mun gida na na sake saki ɗaya, na laifin da kikayi a bainar jama'a, idan kuma kin saka ɗanki ya saki matar shi Fatima, toh kije na ƙarisa sauran biyun ma".

Yana faɗin haka ta saki ihu iya ƙarfinta, wanda har sai da wurin ya amsa,shi kuma ya saka ƙafa ya fita a parlour.

Faɗuwa Mama tayi a wurin tana kuka, da ƙyar ta ɗauko wayanta tayi dialing number Ummanta, amma abin mamaki sai da tayi misscall goma bata ɗauka ba, sannan ta maida kan na Aunty Fannah ita ma taƙi ɗauka, har saida Mama ta gajji ta haƙura, har ƙasa ta sunkuya tana kuka.

Daga baya ta ƙira Hammah shima firr yaƙi ɗauka, tana kuka tana kallon fuskar wayan hankalinta a tashe tana mamakin abinda Umma da Hammah da Aunty Fannah suka mata.

Daga baya ta kira Abdulrahman yana fara ringing kuwa ya ɗauka, daga ɗayan gefen muryan shi a ɗan murtuke ya amsa mata da "hello Mama".

Tana ƙara muryan kukanta tace, "Abdul Babanku ya sake ni yanzu kuma yace ya bani minti talatin na bar mishi gidanshi, Abdoul na ƙira Umma na da Fannah sunƙi ɗaukan wayata, Hammanku ma yaƙi ɗaukan wayata, nashiga uku Abdoul yayaj zanyi yau kam, wallahi Fatima da ƴarta sun cuceni, sun rabani da mijina da uwata da ƴan'uwa na da ɗana".

Ajiyan zuciya Abdoulrahman yayi, duk da baiji daɗin sakinba amma har ga Allah yasan an ƙure Baban shi ne, domin yasan irin haƙurin da yake da Mamansu, sannan kuma yasan tana shiga hakkin ƴaƴanta, duk da rasuwar ɗanta bai saka ta ladabta ba, toh meye zai girgiza zuciyar Mama?.

Shiru yayi yana sauraran kukanta da yake ji har cikin ranshi, da ƙyar ya buɗe baki yace.

"Mama gaskiya ni ɗanki ne amma kuma zan gaya miki gaskiya, abinda kikeyi baki kyautawa ko kaɗan, ko daga rasuwar Hammah Babagana ya kamata ki haƙura da abinda Allah ya hukunta, sannan ae bai kamata ki yi abinda kikayi a cikin mutane ba, ko don darajar mu ƴaƴanki da mahaifiyarki da take wurin, ɗazu Ummah ta ƙirani bakiji irin kukan da takeyi ba, wallahi sai da hankalina yayi mummunan tashi, ga Hammah Umar ko amsa wayar mu yakasa, toh Mama me kike so ne? Kinfi so idan da rabo ki mutu a haifah? Gaskiya Mama shawara zan baki a matsayina na ɗanki kawai ki barwa Allah ya yi ikon shi, don baki isa ki hana abinda ya nufa ba, saidai ki shiga matsalah wanda muma ya iya shafan mu".

BADARIYYA Completed {03/2020}.Where stories live. Discover now