*typing*
*BADARIYA*
®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION* ✍🏻
{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar rayuwar duniya da kuma lahira.}🎐G•W'A🎐
*GASKIYA DOKIN ƘARFE* 🏇🏻Story and written
By
*AUNTY NICE* 😘Wattpad@GaskiyaWritersAsso.
*WANNAN LITTAFI SADAUKAR WA NE ZUWA GAREKIMISS XERKS*
*PAGE* 30--31
*___________*📖Babagana yana isa lagos ya shiga gidan da yake, har zuwa lokacin zuciyar shi zafi rake mishi, kasa yin komai yayi ya hau gado ya kwanta.
Idon shi yana kallon saman ɗakin ya dafe goshin shi da ɗayan hannun shi, yana ta ayyana abubuwa a ranshi game da rayuwanshi da Mama, sai yaji ƙaran wayan shi.
Kaman baxai ɗauka ba, wani zuciyar ya saka shi ya ɗauka, ganin sunan Hammah Umar ne ajikin screen ɗin ya saka shi tashi zaune.
"Hello Hamma!" cewar Besty wanda daga jin muryan shi kasan akwai rauni a cikin muryan, Hammah ne yake tambayan shi yanda ya baro gida da kuma isowan shi lafiya, sannan yace mishi.
"Babagana ina so kayi haƙuri ka cire abinda Mama ta maka a zuciyarka, domin ita uwa haƙuri ake dayita akowani lokaci, domin a samu a rabu dasu lafiya".
Lumshe ido Besty yayi yana jin wani irin sanyi a zuciyar shi, domin a rayuwa ya daɗe yana so yaga Hamman shi yana shiga al'amuranshi, gashi yau ɗaya yaji zuciyar shi ya fara sanyi domin jin daɗin da Hammah ya yi na nuna damuwan shi a kanshi.
Lokaci ɗaya yaji bakinshi ya buɗe yana cewa, "Hammah ni da nace ko na haƙura da auren Riyyah ce"?........ "kull naji kana faɗin haka Babagana, ita ae matsayinta na uwa kamata biyayyah a rayuwa ba wai ance idan tana so ka kauce hanya ka biye mata kuyi ɓarna ba, a'a ba haka ake nufi ba, kawai ku zauna lafiya har Allah ya rabaku lafiya, amma shi maganan aure babu wannan tunda bawai an sameta da wani na kasu bane wanda yakai a ƙi aurenta."
Babagana yaji zuciyar shi tayi sanyi, suka cigaba da hiransu kaman dama sun shaƙu, Hammah yana ta ƙwantar mishi da hankali, har zuwa wani lokaci sukayi sallama.
Sai a sannan Besty yaji ƙarfin gwaiwan ya nemeni a waya.
Inajin ƙiran da kaman bazan ɗauka ba, amma sai wani zuciyar ya danne ni na ɗauka, ina ɗauka ko magana banyi ba nati shiru kawai.
Dariya yayi sanan yace, "Beauty nah, nayi laifi ko"? Murguɗa baki nayi kaman yana kallo na nace, "Da akayi me kuma?".
"Beauty don Allah kiyi haƙuri wallahi wani abu ne ya sha mun kai, har zuwa dare ban samu kaina ba, da Asuba kuma aka neme ni a Office duk hankalina a tashe na tafi babu shiri".
Hmmm kawai nace ba tare dana tanka ko kalma ɗaya ba, haka yayita rarrashina ina jinshi, a ƙarshe ya mun sallama, ajiye wayan mukayi amma sai na samu kaina da jin daɗi saboda ko ba komai nasan lafiyan shi qalau.
Ranan sunday muka koma school, bayan mun koma ne Besty ke tambayana yayah mukayi da Besty akan maganan ɗinki?
"kawai Aunty tace na bari akwai wata ƙawarta a kaduna da sukayi zata aika mata wasu, sannan kuma Hammah Haidar yace a aika mishi zai baiwa telan da zata miki".
Haka muka cigaba da hiran mu, kuma na kwantar da hankali na domin muyi karatu a nutse, domin yanzu muna second semester ne, aji 2 zamu tafi.
YOU ARE READING
BADARIYYA Completed {03/2020}.
RandomLabari mai ƙayatarwa,nishaɗantarwa yare da faɗakarwa.