34-35

1.1K 82 2
                                    

*BADARIYA*
*1441H/2019M.*


®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga kinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar rayuwar duniya da lahira.}_

       🎐G•W•A🎐
_*GASKIYA DOKIN ƘARFE•* 🏇🏻_

Story and written
           By
*AUNTY NICE*

*_WANNAN BOOK SADAUKARWA NE ZUWA GAREKI MISS XERKS._*

~Wattpad@GaskiyaWritersAsso.~

{innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, ina miƙa ta'aziya wa iyalen Alhaji Babagana Zaki, na rashin ɗansu, ƙaninsu, Aliyu zaki (Abba)da akayi ranan saturday, matar shi kuma ƙanwata Fauxy ina miki ta'axiyan rashin miji da kikayi, tabbas na tausaya miki Fauxy, domin mutuwan miji sai Allah, Allah ya jiƙan mijinki ya mishi rahma yasa yana cikin Rahma, Allah ya baki haƙurin wannan rashin da akayi, 😭😭😭.

*PAGE* 34----35

*__________*📖Murmushi yayi yana kallo na yace, "Beauty bari nabarki kije ki huta nima kaina yana ɗanmun ciwo ne, gara naje na kwanta da wuri, kuma Baba ma yana son ganina" ya faɗa yana duba na, nima sallama na mishi na juya cikin gidan mu.

Besty bai sake leƙoni ba sai ranan Friday da safe, ina gidansu Besty Feenah ya ƙirani na faɗa mishi ya sameni acan, lokacin kuma angama cire mun jan lalle saura baƙin, haka nabawa Aunty ya gana haƙuri akan bari naje na dawo sai a saka mun.

Can wurin side ɗin Yayah Kamal yayi parking ganin babu mutane ta wurin, ina ƙarisowa na mishi sallama kenan sai ga Yayaah Kamal ya fito daga palon shi, har inda muke ya kariso.

Abin mamaki sai naga ya miƙawa Besty haannu, Besty ma da hanzari ya miƙa mishi fuskar shi ɗauke da fara'a yana faɗin,"barka dai ango, yayah hidima"?

Yayah Kamal abin mamako shima fuskan shi da fara'a yana kallon Besty yace, "ae kaine ango domin gaka ga amaryah baka ko ɗaga mata ƙafa, ga adon lalle duk an maka, domin burgeka" ya ƙarisa dukkansu suna dariya.

Kallon mu yayi yace, "ku shiga cikin palon mana ko,inaga hakan ae zaifi tsayuwa wajen" ya faɗa yana miƙo mun key ɗin palon shi.

Sallama suka yi cikin barkwanci wanda bantaɓa ganin Yayah Kamal yana yi ba, haka muka karisa ƙofan palon na buɗe mana, muka shiga.

Muna zama Besty ya dubeni yace, "Beauty anya bazaki burkita mun tunani ba da irin wannan kyau da kike ƙarawa? dubi wani jan lallai da aka miki kaman na sa harce na lashe shi" yana faɗa kaman zaiyi yayah.

Ina masa wani rausaya wanda bansan yaya akayi nakeyi ba nace, "sai ma anjima idan an karisa mun baƙin na ƙara wargaza maka tunanin" na faɗa ina rufe ido na.

Dukkan mu dariya mukeyi,sannan yace "Gaskiya Beauty idan donni zakiyi wannan kwalliyan toh bana son baƙin lallai, ni jan kawai ya wadatar dani, amma bakin gaskiya bai cika burgeni ba".

Kallon shi nayi nace " insha Allahu Besty har abada bani sake yin baƙin lallai sai ja, tunda don kai zan dinga kwalliyan".

Daga dukkan alamu maganan dana faɗa ya mishi daɗi, don kasa rufe bakinshi yayi sai murmushi yakeyi, dai-dai lokacin wayan shi ta ɗauki ƙara.

"Hlo Hammah yayah kake?" ina ji nasan da Hammah Umar yakeyi, abin mamaki Besty har wani mantawa yayi dani sai labari yake bawa ɗan'uwanshi, kaman daga sama naji yace, "lah Hammah gata nan ma muna tare" sai ya miƙo mun wayan fuskar shi ɗauke da murmushi.

Kara wayan nayi ina mishi sallama shima daga ɗayan side ɗin yake amsama mun, lokaci guda kuma duk sai mukayi shiru, har na ɗauka wayan ta yanke ne, zan miƙawa Besty sai naji muryan shi yana cewa.

BADARIYYA Completed {03/2020}.Where stories live. Discover now